GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIÊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINSUNNAH-BLOGSPOT.BLOGSPOT.COM


WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA LACCOCI DAGA MALAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI; {mumbarinsunnah@gmail.com]

Sunday, 16 September 2012

HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’A {4}


CANJA KALMOMI DAGA MA’ANONINSU NA ASALI
       Malamai sufaye suna baiwa kansu wadansu martabobi wanda asalinsu suna dangana sune da Imam Aliyu Ibnu Abi Dalib, Allah ya yarda da shi, cewa kowane Annabi yana da mutane bakwai zababbu amma shi Annabinku mai tsira da amincin Allah, an ba shi mutane goma sha hudu ne zababbu. Sune, Abubakar, Umar, Ibn Mas’udu da Ammar yardar Allah ta tabbata a gare su. (Ibn Maja da Tirmiziyyu). Amma shi Tirmizi yace ance da Aliyu cewa su wanene, sai Imam Aliyu yace, “Ni da ‘ya’yana, kuma da ta’afar da Hamza da Abubakar da Umar da Mus’ab bin Umairu da Bilal da Salman da Ammar da Ibn Mas’ud. Amma ruwaya ta Ibn Abdul-Barri bai ambaci Mus’ab Ibn Umairu ba. Sai Tirmiyi ya cika na goma sha hudu da Khuzaifatu da Abah Zarrin da Mikdadu.
       Tilmisani ya ambaci Abu Na’imrawin hadishin cewa daga Aliyu ya ji, shi Imam Aliyu yace, “ya ji daga Annabin Rahama mai tsira da amincin Allah. Amma ga yadda lafazin hadishin ya zo, “Ba wani Annabi daga cikin Annabawa said a aka ba shi wasu zababbun mutane guda bakwai wadanda za su zama masu wazirai to, ni kuma Annabi, an bani zababbu mutane kamar haka, Hamzat da Ja’afar da Aliyu da Hassan da Husaini da Abubakar da Umar da Abdullahi dan Mas’ud da Abu-Zarrin da MIkdaru da Khuzaifata da Ammaru da Sulman da Bibil.
       Kuma wani malami mai suna Zununni Al-misri Allah ya masa rahama yace “Nakibai mutum (300) ne, amma najibai guda (70) ne, kuma Al abudahu su (40) ne, Walakhyaru kuwa su (7) ne, umdodi kuma su (4) ne, shi kuma gausi guda daya ne a duniya.
       Wadannan wasu darajoji ne na sufaye
       Kuma an sami Hadisi daga Abubakar Madu’I ya bada labari daga wanda ya ga khadiru bawan Allah kuma salihi ya yi Magana da shi, yace masa, “ka sani, lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya rasu, kasa tayi kuka kuma tace “ya shugabana, yanzu ka barbni kenan yanzu ba wani Annabi da zai rika tafiya a cikina har tashin kiyama? Sai Allah ya yi wa kasa wahayi cewa, “zan sa miki a bayanki daga cikin al’umma wadanda zukatansu kamar zukatan Annabawa ne, bazan rabaki da suba har zuwa tashin Kiyama. Sai aka ce masa “Nawa ne mutanen da zasu zo bayan Annabi? Sai aka ce “Akwai waliyai guda (300) sai Nujaba’u guda (70) akwai kuma Autadu guda (40),k da kuma Nukaba’u guda (10), da kuma Urafa’u guda (7), Mukhtaruna guda (3), sai kuma Gausi guda daya (1).
       A cikin wadannan guda ukun, in gausi ya rasu, sai a zabo guda daya daga uku shi zai gaje shi, kuma daga cikin guda bakwai sai a dauko daya, shi zai cika gurin na ukun, kuma daga gomanne za’a dauko ya cike gurbin guda bakwai, daga cikin arba’in kuma a dauko guda ya cike guda goma, daga cikin (70), sannan a dauko daya daga bayin Allah a cike gurbin na (300) da aka dauka to haka za’a rika yi har zuwa tashn Kiyama.
Kuma ba za’a tashi kiyama ba har sai an rasa mai cewa “La haula walla kuwata” a bayan kasa. Allah ya sa mu cikin musulmi, kuma ya tayar damu cikinsu ranar tashin kiyama.
       Wannan Magana an ciro tane daga wani littafi mai suna. “Sharhin Ashafah” (na wani Malami mai suna Aliyul Khadi). A kashin na farko babi na uku, fasali na daya. Za ‘a gani.
       Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yace “wadannan maganganu da aka yi, ba wani mutum da zai iya gaya maka cewa su wanene mutum (300) cewa sun e wane da wane, da kuma mutane (70) dinnah da kuma (40) da kuma (10) da kuma mutane (7) da kuma mutane (3) da kuma cewa ai wanene gausu da aka yi maganarsa a cikin littafin. Kuma su ma da kansu ba wani mutum da zai iya cewa shi ne daya daga cikin mutanen nan da akace khadiri ya fada da zai ce shine kaza. Balla kuma har yaba da wani labari, don kuwa wannan al’amari ne da yake danfare da ilimi na gaibu, kuma Allah yace “Ba zai aiko wani Manzo ko Annabi ba, kuma ga shi Annabtaka da manzantaka ya yanke.
       Saboda fadar Allah cewa “Shine masanin abin da ke boye, kuma ba zai sanar da wani ba sai wanda ya yarda da shi daga cikin manzanni, zai sanya musu kariya a gabansu da kuma kariya a bayansu, don tabbatar da wannan manzo ya isar da sakwansa, kuma Allah saninsa kewaye yake da su, kuma ya kidaya komai daki – daki”. (Jinni 26-27). (kuma a halin yanzu Annabtaka ta yanke daga kan Annabi Muhammadu mai tsira da anincin Allah,ba wani Annabi bayansa,kuma ba wani wahayi da zai bayyana mana cewa wane ne gausi da ake nufi, balle kuma a sanar da sauran kasha-kashe da aka yi bayaninsu a baya. Saboda fadar Allah mai girma da daukaka na cewa “wadanda suka kirkiri karya suka jingina wa Allah ko, wadannan basu da rabo, kuma ba za su rabauta ba, sannan ‘yar rayuwa kadan za su yi a duniya sannan su dawo gare ni a lahira, kuma zan dandana musu a zaba mai tsanani, don abinda suka kasance suna aikatawa na kafirci. (Yunusa 69).
       Sheikh Abubakar Gumi yace “Allah ya tsare mud a nuna wa Allah tsaurin ido saboda falalrsa da baiwarsa amin. Kumad aga karshe, ni bance komai ba akan wanda ayce yaga Khadir, sai bayani ne akan abubuwan da aka fada na cewa ba wani wanda zai kara samun wahayi, sai dai ina karawa da cewa” godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.
       Kuma yana daga cikin bidi’ah bin wani Shehi a cikin barna da nuna son wannan mutumin koda yana cikin barna da kuma son rai, bai ka mata a cigaba da karanta addu’ar nan da ake kiranta “Jauharatul Kamali” ba saboda dalilai sun bayyana cewa karantata kuskurene a nassi da kuma hankali, kuma ya saba wa shari’a, ita wannan jauharatul kamali ga yadda lafazinta yake shine “Allahumma salli wa sallim ala sayyaidina Muhammadu ainirrahmati ar-rabbaniyyati, waya kutatu, al-mutahakkikatu, Al-ha’idati bi markazi fuhumee, Wal’ma’anee, wanurul akwani mutakawwinati nu Yuhaladaneer, sahibul hakki rabbanaee, al-barkil asada’I bima zanil, ayahilal mali’ati, likulli muta’arridi minal  buhuri wal awanee, wa nurukallami’I allazee mala’ata bihi kaunukal ha’idi, bi amkinattil maka’in Allahumma salli wa sallim ala’ainil hakki, allatee minha urushil haka’iki ainil ma’arifil, akwami, siradikal tamul, askamu, Allahumma salli wa sallim ala dal’atil hakki bihakkil, kanzul, a’azamu, ifadatika, ilalka, ihadatulnuri, almudal sama, sallallahu alaihi wa’ala a’ilhi ta’arifuna biha, iyahu”
       Sheikh Gumi yace “wannan addu’a tana da wahala cikin fadarta da kuma ma’anarta, kumabata yi kama da maganar Annabawa ba, kumaina ganin an kirkireta ne a cikin kalmar “askamu” kuma wannan kalma tana nuna tafi kowane ciwo zafi a cikin ciwunna, don ba yadda zai yiwu akan abin da suke cewa wai kalmar an ciro tane daga cikin mikakkiyar hanya to, amma a ilimi sanin sarhu, malamai basu da wata kalma kamar haka, don kuwa “ba’a cire sunan da yafi kowane daraja sai a cikin ismu sulasi, mai cancan jawa da karbar fifitawa, kuma malaman sarfu basu taba kawo wannan wazani daga alala wanda yake daidai da askama wanda ba wani kaucewa a ciki. Kuma duk wanda aka rasa cikar wannan sharadin to, ana neman wata kalma ce da zata cika ta in kuwa basu samu ba, to suna neman wata kalma ce wacce zata cika tasu kalmar a mizani, misali in ance mutum tsayayye ne to, ba dama a ce “Askama” sai dai a ce “huwa ashaddu istikamatan” to da haka su ka ce, da ma’anar ta bayyana. Amma in aka ce “Askami a wazanin sarfu, to yana nuna cewa ciwonda ya fi kowane ciwo zafi kenan. Don haka, kuskurene a siffanta Annabi da cewa “Siradikal tamul-askami” da yabo suke so, to da sai su yi amfani da wata kalma ba kalmar “Askamu ba” koda yake wani malami mai suna Asheikh Umarul Futi ya yi bayani a cikin littafinsa mai suna Rimahun huzbil Raheemi ala nuhuri hizbil rajeemi.
       Yace “kalmar nan ta “Askamu” itace hanya mikakkiya ba tare da wata karkata ba. Kasani, kalmar Askamu, tana daga cikin fil’ilin kalmar istikama na fi’ili sudasee, wanda asalinsa kama ne, sai aka karamasa harafi uku, sai ya zama “istafa’ala lolaicn da aka yi nufin gina kalma akan wazanin af’ala, na fifita wani abu mai daraja, sai aka goge alifinsa da ta’un dinsa da alifun dinsa, wanda yake da asalinsa “wa’un ne sai aka bar “seenun” din don ta nuna cewa wannan aikin an cisgoshi ne daga fi’ili mai “istikama” daga sudasi mai kalmomi shida, ba wai an cisgoshi daga “kama” bane.
       Kuma daga cikin irin wadannan akwai wata kalma mai suna “Aswaku” wacce take cikin siffa ta “af’alul-tafdir” wacce aka ciro ta daga “af’alul-tafdir” wanda aka cisgota daga “istikama” na khuma see. Wanda asalinsa “Shaka ne kuma asalinsa mazidi da harafi biyu, sai ya zama af’ala. Idan aka masa kari sai a goge ta’un da aka masa kari na asali, sai ya kom “Aswaku” idan aka ce maka “Saboda me aka goge kalma “inistikama” amma ba’a goge “Ishtikaki ba? Sai a ce ai zamanta a “Khumasi” ba zai cutar ba, sabanin kalmar (Istikama sudasi) domin in akabar kalmar “Istikama” a lokacin nan sai ta zama “Akwama” to ma’anar ba zai bayyana ba wajen nuna kwarewa a sarfu. Idan aka fassara kalmar nan ta farko za ta bada ma’anar tsayuwa mai kyau wadda ba bu karkafa a ciki. In kuma aka fassara shi a kan hanya ta biyu wato aka ce “Akwamu” to amfanuwa da waccan ya tabbata akan asalin kalmar dominya tsawu ne akan kalmar “Ikama”
       Idan aka maka tambayar cewa “wanene ya yi wannan fassara daga cikin maluman lugga na sarfu? Sai ka bad a amsa cewa ya zo a cikin “Kamus” littafin nan daya ke fasara luggar Larabci, cewa ma’anar “Kamus” ana nufin jama’a ne maza da mata. Amma idan rijahine to ana nufin maza ne kawai. Kuma ya ci gaba da cewa “kaga asalin “kama” to anan ne aka samu kalmomin “kama” kauman” wa kumantun” wa ikayaman wa “kamat” “kawamatuhu kawannan kunatu ma’ahu” wa kawamatul mar’atu wahidati, wama bainal ra’aka taini kaumawatun, walmaka’nun maudu’ul kadamaini, wa kamatul-mar’atu tanuhu, dafikat, wal’amru’I tadala kasti kama.
       “Wa’ammash ti kakuhu fakad kila feeru” Dukkan wadannan kalmomin ana sanunsu ne kuma don a nuna asalin kalmomin a Larabci, kuma haka su ka zo a cikin munjidi wato (Kamus). Kuma kalmar “Ishtikakuhi” asalinta daga shauku ne (wato son rai zuwa wani abu, inda har ya kai “Shakata ni hubbi har” (son wance ya shiga zuciya ta). Kamar “Haja nee” (wato ina begen sa) har zuwa “Ishtikakahu” (wato baegensa da sulasi da ake yi musu kari za’a ga lokacin da aka zo gina af’alu tafdeel. Su “Ziya dar” aka cire. Don kuwa da aka cike ziyadar sai aka yi wazanin cikakkiyar ka’idar wadda bata da wani matsala amma ta saba da kalmar nan ta “askamu” domin da suka ce “Askamu” sai suka cire asalin maimakon ziyada da aka yi wanda da an ce Akwami da sun yi daidai masu “Alifun” sai ay zama “Akwamu” wato ya zama wamu af’alu don haka aka gine” wazani ismu tafdii “Amma wani malami yace “yana zzaton wajen cirowa ne aka yi kuskure, wato maimakon akucemu sai aka ce “Askamu” koko “mudallasasun” (wato wanda yake son ya lallata gaskiya saiya canza “
akwami” da Askamu” kuma Shaikh ya yi bayanin cewa ko da anyi kuskure wajen fada ko wajen cirowa to, duk da hakama ba’za a bi wannan fassara ba don kuwa dukkansa kuskure.
       Kuma Shaikh Abdullahi Gwandu Dan Fodiyo, a cikin wata kasidarsa mai suna “Hisnil Rasini” akan ilimin Sarfu, ba’a bin malami cikin bata, gaskiya kuma ko daga wajen jahili ta taho to, a yi aiki da ita. Sannan malamin yaci gaba da cewa don ba wani dalili da za’a karbi wadannan uzurori.
       Don kuma bai kamata a dore wa Larabawa wata kalma dan a cimma wata sabuwar buri da bukata ba. Don kuwa bai halatta a canza wa malaman nahawu ka’idarsu da cimma wata manufa ba. Saboda su maluman bidi’a suna kuka ne da abubuwa kyawawa na lafazi, ba wai tana, zuwa ne da wata manufa ba sai dai in ta zo a cikin wani lafazi sai su sanya ta a afke don cimma burinsu. Don haka bayanin da su kace “askamu” daga”akawamu” ne, ba daga Ak-wamu” bane, asalinta daga “sakama” ne, wace take dauke da ma’anar rashin lafiya ko siffa mai dauke da ciwo. Kuma siffanta Annabi mai tsira da amincin da wannan siffa bai dace ba, bai halatta kafiri ya siffata wannan da Annabi ba, balle musulmi ya siffata shi da ita, don an hana mutum ya siffatan Annabi da siffa biyu wato yabo da suka.
       Saboda fadar Allah Madaukakin Sarki cewa, “kar ku cewa Annabi “Ra’ina” (wato ka saurara mana ya manzon Allah), don kuwa kalmar “Ra’ina” tana daukar ma’ana biyu, wato ka saurar da kuma ya kai rubabbe. Saboda haka aka canza wannan kalma ga sahabbai su ce “nzurna”. Ya ci gaba da cewa yak u Musulmi ku ji abin da Allah yake gaya muku kuma su kafirai suna da sakamakon azaba ranar gobe Lahira. (Bakara 104). Kuma a wata aya Allah yace, “idan kafirai suka zo suna gaishe ka da wata kalma da abinda Allah bai gaishe ka da ita ba, in suna hira a tsakaninsu sai su rika cewa ‘yaya Allah ba zai mana azaba ba saboda wannan kalma da muke gaya masa in ya kasance Annabin Allah ne? sai Allah yace, “wutar jahannama tai she su kuma za su shigeta, kuma makomarsu ta munana.” (Mujadala 8).
       Sheikh Gumi ce “Ba wani bukatar dauko maganar Shiek UmarHuti anan na dauko shi ne dai saboda jin tsoron kar wani malami ya yi amfani da shi, ya rufe gaskiya, don kuwa har yanzu akwai wasu maluma masu kokarin daga karya akan gaskiya tun da can, har zuwa wannan lokacin da muke ciki; masu kokarin sa guba a cikin addini don su fitar da masu addinin da gaskiya daga cikinsa, kumadon su yaudari masu imani. Allah ya tsare mu daga makircinsu, kuma ya shiryar damu hanya madaidaiciya da baiwarsa.
       Har yanzu dai daga cikin abubuwan da malamn bidi’ah su ke cusawa mutane wadanda suka sabawa shari’a kamar hana sufaye da ‘yan dariku zuwa ziyara wajen malaman sunnah suna gindaya musu wasu sharadodi da basu da wani dalili, da kuma sa su akan cewa kada su yarda su nemi ilimin Fiqhu da na shari’a, alhali wadannan abubuwa sun e hanyoyin tabbatar da shari’a da kuma dora su akan wasu wurudai da lazimomi wanda wani ma mai yi baya fahintar abin da yake fada.
       To, duka wadannan abubuwa suna daga cikin bidi’o’I munana da aka hana. Kuma yana ma cikin abubuwan da Allah ya hana, “ku kuwa mutane suna da wasu ne masu tsara musu dokoki wadanda Allah baice a yi ba? Ba don Allah ya yi alkawari cewa sai ranar rabewa za’a yi musu hukunci ba, to, da tun a nan duniya Allah zai hukunta tsakaninsu. Lallai ne azzalumai suna da azaba mai radadi (Shura 21). Kuma Annabi mai tsira da aminci yace, “shin me ya sa mutane suke shardanta abin da Allah bai shardanta ba wani sharadi da baya cikin littafin Allah, ko da shardin sun kai guda dari (100) ba za’a yi aiki da suba.” (Imam Bukhari ya ruwaito).
       Kuma Shaikh ya ci gaba da cewakaranta sunaye da ba’a san ma’anonin sub a, ba za su amfanar ba. Kamar yadda Allah mai girma yake cewa. “wadanda basu san abin da suke fada ba yayin dawafi a dakin Allah mai girma to, wannan addu’o’in sub a ta zama komai ba a dakin Allah, sai dai tafi, da sowa, kuma a ranar tashin kiyama za’a ce su dandani azaba saboda abinda suka kasance suna butulcewa a duniya. (Al-Anfal 35).
       Wadansu malamai suna cewa “Zaaka ga mutum yana cewa “La’ilahaillahu” amma bai san abin da yake cewa ba, har ya kai yana cewa “Haa haa, sai yenta kawai yanake yi. Kuma zai yiwu a sami wani mutum ya rika karanta wadansu sunaye da abi sun manufofinsu ba, alhali ma wasu masu cutar da shi neb a masu amfanar da shi ba, kamar yadda Allah yake cewa a littafin sa, “shi mutum yana ta rokawa kansa sharri yana nufin alkairi ne yake roko, saboda shi dan Adam mai gaggawa ne.” (Isra’I 11). Hakakuma yayi tayin addu’ar da sunayen da bai san suba, sai ayce masa, “me ya sanar da kai wadannan, kila ma kalmomi ne na kafirci ba ka sani ba”,. Shehu Usman da Fodiyo ne ya fada a cikin littafinsa mai suna Bayanil-bidi.
       Kuma yana daga cikin ka’idojin su nayin amfani da wasu kalmomi da maganganu ba’a wurin da shari’a tayi umarni ba kamar kalmar nan Madadu (wato samun wata fa’ida a wajensu. Wanda kuma ma’anarta a cikin littafin Allah shine. Karin azaba. Saboda fadar Allah madaukakin sarki “Za mukara musu azaba ka ri mai yawa” (suratul maryam aya ta 79). Amma in suna nufin kari a cikin alheri ne to, ya zo a ruba’I neb a sulasi ba. Inda Allah yake cewa, “Yumdi ukumbi amwalin wa banina” (wato Allah zai kara muku alheri a cikin dukiyoyinku da ‘ya’yanku). Allah yana cewa, “Wanda ya kangare ya sabawa Manzon Allah, bayan gaskiya ta bayyana masa a sarari, amma ya bi hanya bata muminai ba to, za’a jibinta masa abinda ya jibinta, kuma a kona shi da wutar jahannama kuma makoma tayi muni.” (Nasar 115). Kuma a wata aya Allah yana cewa, “kuna so na sanar da ku wadanda ayyukan su suka lalace a duniya, alhali suna zaton ayyukansu suna kan hanya, sune wadanda suka kafirce wa ayoyin Allah, sune wadanda suka kafircewa saduwa da Ubangiji, to sukan ba za’a dora aikin su a ma’auni ba. Sannan kuma, sakamakonsu jahannama ce. Sannan kuma, suka yi a duniya, kuma suka riki ayoyina da manzanni na abin izgili.” (Khafi 103-106)
       Sheikh Gumi yace abin da ake nufi da mumini a wadannan ayoyi, Allah ne mafi sani , kuwa sune sahabban Annabi da tabi’ai da tabi’ittabi’ina da wadanda suka bi hanyoyinsu da kyautatawa har zuwa ranar tashin al-kiyama. Kuam yace “Allah ya sanya mu a cikin masu jin Magana, kuma su bi mafi kyanta.

TUNTUBE DA KURA-KURAN WASU MALAMAI TAFSIRI
       Yana daga cikin wadansu abubuwa day a kamata a tunatar cewa wasu malaman tafsiri duk da kokarin da suka yi cikin fassara ma’anonin ayoyin Al’Kur’ani, sun kware wajen kawo kissoshi na dalilan saukarwa. Amma duk da wannan kokari na su, wasu basa auna kissoshin da suke kawowa, don kuwa daga cikin kissoshi sai ka ga kissoshi ne na karya, wadanda makiyan addini suka kirkiro su don su sa guba a cikin addini. Kuma wasu kissoshi, an dauko sune daga littatafai. Yahudu da Nasara da suke canza addininsu kuma suka jirkita shi. Wani lokaci kuma, ana samun kuskure ta fuskar rashin tsayawa a fahimci tartibin ayar, koma a aura tsakaninta da tsakanin ginshikai ingantattu da ake gina Musulunci a kai. Ga kadan d azan ambata akan wadansu kissoshi na karya.
       Daya daga cikin shi ne kisser Haruta da Maruta wanda na yi Magana a baya na yadda za’a fahimci lafazin cewa ayar tana korewa neb a wai tabbatarwa take yin a maganar Annabi Sulaiman ba, tun daga tushe. Almar yadda suka bada kisser shi ne wai “mala’iku amincin Allah ya tabbata a gare su, lokacin da suka ga yawan zunibin dan Adam da yake hawa sama, sai suka aibanta dan Adam, cewa bai cancanta ya zama Khalifan Allah a bayan kasa ba, suka ga sune suka fi cancanta a sa su a bayan kasa, wanda Allah Madaukakin Sarki yace, “su zabo mala’iku guda biyu daga cikinsu wadannan da za’a sasu Khalifofi a bayan kasa, sai suka zabo Haruta da Maruta. Sai Allah ya sa musu sha’awa irin tad an Adam. Daga sa musu sai ya sanya musu su rika hukunci ga dan Adam a bayan kasa, kuma da yamma su rika dawowa sama.
       Kuma daga cikin abin da ake hana su a bayan kasa sune : ka da su yi shirka, kuma kada su kasha rai bada hakkin shari’a ba, kuma kada su sha giya, kuma kada su yi zina, su kasance suna hukunci a tsakanin mutane da rana, in dare ya yi kuma, sai su karanta sunayen Allah mai girma, sai su haye sama. Sai wata mace kyakkyawa mai suna Zahara’u ta kawo kara wajen mala’ikunnan sai ta fitine su har suka aikata duk abin nan da Allah ya hane su har ma suka sanar da ita addu’ar da suke yi suna hawa sama, da ta karanta, sai taga ta yi sama, amma daga bisani sai Allah ya shafe ta ya mayar da ita tauraruwa, su kuma lokacin da hawa samansu ya yi, sai suka karanta addu’ar sai fukafukansu suka ki motsawa ta yadda za su tashi, daga nan sai suka gane cewa sun saba wa Allah. Wai wannan abin ya faru ne a lokacin Annabi Idris, daga nan sai suka tafi kamun kafa wajen Annabi Idrissu. Sai Annabi Idris, ya roki Allah. Sai Allah y ace ya yarda, amma da sharadinsu zabi inda suka faso a yi musu azaba, a duniya ne ko Lahira? Sai suka zabi cewa a yi musu a zaba a nan duniya, saboda ita azabarta mai yankewa ne. to wai yanzu suna nan ana musu azaba a Babila har zuwa tashin AL-Kiyama. Shi ne sukace wai wadannan mala’iku sun e suka koya wa mutanan babila sihiri.
       Imam Jamal ya ce “wannan ta Yahudawa ce kawaisuka kirkiro ta, ba kissace ta gaskiya ba, don kuwa ta saba wa nassi da kuma hankali”.
       Sheikh Gumi yace ita wannan kissa ta kore kariyar nan da aka dora wa mala’iku da su bas a saba wa Allah abin daya umarce su. Kuma yace ta saba wa tarihi, don kuwa Annabi Idirs ya yi zamani net un kafin a yi rowan Dufana, a zamani mai tsawo. Kuma ya ci gaba da cewa irin wadannan kissoshi suna lalata kyakkyawar akida ta Musulunci, kamar yadda, suka ce mala’iku ne su ke koyar da sihiri a lokacin Annabi Sulaiman wanda wannan ba gaskiya bane. Kuma bin da yafi da cewa da wannan shine a dangana shi da manufofi na Yahudanci ga malaman Yahudu da yake sun san gaskiya amma suka canza ta daga bigirenta. Kuma duk wanda ya san gaskiya, kuma ya ki aiki da ita to, ya zama shaidan, domin sune suka kirkiri ilimin sihiri don su ribace kwakwalwar mutane, amma sai suka dangana shi da Annabi Sulaiman cewa ya mallaki duniya ne ta hanyar sihiri, wannan kuwa an kirkira wa Annabi Allah karya, kuma sun karkatar da hankulan wawayen mutane wadanda suka bar littafin Allah suka koma ga neman ilimin sihiri donsu mallaki duniya. Sai Allah ya karyata su don kuwa Annabi Sulaiman baiyi sihiri ba, kuma mala’iku ma ba su karantar da sihiri ba, na cewa Haruta da Maruta ba’a saukar da su a Babila ba, kuma su basu koyar da kowa sihiri ba, sai dais u shaidanun malamai sune suka karantar da sihiri kuma su ne suka kafurta. To wannan kisser tana nuna mana cewa kissace ta karya ba gaskiya bace.
       Yana daga cikin kissoshi da ake karantar da mutane ta Annabi Yusuf wacce take tattara da abubuwa masu kima da daraja da suke koyarwa don a yi koyi da su, sai wasu malaman tafsiri suka karkatar da ita, suka kebeta ga Annabi Yusuf da yan’uwansa, alhali ita kissa ce ta karantar da duniya gaba daya.
       To, duba ka ga yadda suka kawo ayar nan mai cewa “Hakika ta yi kokari sai ya sadu da ita wato (Zulaikha), shi kuma ya yi kokarin gudu don ka daya sadu da ita.” Su ga yadda suka fassara cewa “ita dai tayi kokarin saduwa da shi, sai shi ma ya yi kokarin saduwa da ita, ba don ya ga hujjojin Ubangijnsa ba, day a sadu da ita wato sai ya ga mahaifinsa Annabi Yakuba, sai ya dauki kirijin Yusuf, sai sha’awar ta fita ta ‘yan yatsun sa. Wai ba don zuwan Annabi Yukuba bad a ya sadu da ita. Wato irin wannan kaddarawa da aka yi, ya fitar da ayar daga ainihin ma’anarta, saboda yana ganin lokacin da Zulaikha ta nemi saduwa da shi hart a rufe kofa, sai ayce “Allah ya tsare da wannan aiki, don shi ya kyautata makomata, don azzalumi ba shi da rabo a wajen Ubangiji”. To, wadannan sune hujjojin da Annabi Yusuf ya tuno na cewa duk wanda ya aikata wannan aiki ba shi da rabo. Kuma sune hujjojin da suka hana shi fadawa cikin wannan alfasha. Wannan tsoron Allah za ta iya hana kowane mutum in ya tuno da girman Allah wajen aikata alfasha kamar yadda Annabi Yusuf ya aikata.
       Kuma da suka ce “hamma” (wato niyar aikata laifi) to, wannan ba laifi bane, sabdoa ya zo cikin hadisi cewa Annabi mai tsira da aminci yace, “wanda ya yi naiyar aikata wani mummunan aiki, sai Allah ya tsare shi bai aikata ba to yana da lada guda cikakke. Allah shi ne mafi sani.
       Kamar yadda suka ce wai mahaifinsa ay zo ya bugi kirjinsa, sai sha’awar ta fita, wannan yana nuna karya ne a zahiri don kuwa shi mahaifin na sa, wato Annabi yakubu, yana ta nemansa fiye da shekara talatin (30) da suka wuce.
       Kuma yana daga cikin wannan kissa ta Isra’ila, fadin Allah madaukakin Sarki day ace, “Ya Manzon Allah, Allah ya ishe ka kuma muminai ma sun isar maka daga makiya da mahassada da kuma kafirai makiya Allah”. To wannan fassara in aka yi mata haka to, an yi kuskure, don kuwa kuskure ne a ce Allah da muminai ne za su kare Annabi mai tsira da amcinin Allah, abin day a kamata tafsirin ya zama shine, Allah ya isar wa Annabi, cewa zai kare shi kuma shine zai kare muminai ko da bayan rasuwar Annabi ne mai tsira da amincin Allah don wannan fassara, itace da fi dacewa da shari’a da hankali. Allah shine mafi sani.
       Daga cikin tafsirin da aka sa Isra’iliyat, fadin Allah Madaukakin Sarki “bamu aiko wani mazno ba ko Annabi sia idanyayi burin isar da sakon Allah, sai shaidan ya sanya masa kokwanto a cikin wannan buri nasa, sai Allah ya goge wannan kokwanton da shaidan ya sa a cikin zuciyar wannan manzo ko Annabin, sai Allah ya daidai ta a yoyinsa sai isar da sakon daidai yadda Allah yake nufi. Allah masanine kuma gwani. Abin da shaidan ya sanya kokwanto a cikin zuciyar manzo ko Annabi sia abin ya zamo fitina a cikin zukatan wadanda suke da ciwo a cikin zukatansu da kuma wa danda zukatansu suka bushe, lallai azzalumai suna cikin kokwanto mai nisa”. (Hajji 52-53)
       Mai Jalaini ya fassara wadannan ayoyi guda biyu a cikin tafsirnsa. Yace bamu aiko wani manzo ba kafin kai ya Annabi Muhammadu wanda muka umarce shi da wani aiki da sakon da aka ba shi, sai idan yayi niyar karanta wannan sakon, sai shaidan ya jefa masa abin dab a wanna sakon bane na Allah. Saboda Annabi ya karanta Suratul Najami a cikin majallisar kuraishawa cewa shin ba kuga Lata da Uzza bad a manata na ukunsa? Sai shaidan ya jefa wa Annabi a harshensa na wata Magana wace ba kur’ani ba wato, “Tilka garanikul’ulha inna shaf’atu Hannah laturtaja.” (Ma’ana wadannan mutane ne manya manya ai ana kaunar cetonsu, ai cetonsu ana kauna). Da kuraishawa suka ji ya yabi gumkan su da cewa ana kaunar cetonsu, sai kurishawa suka yi farin ciki. Daga nan sai Mala’ika Jibrilu yace masa “ai ya fadi abin da yake ba’a cikin kur’ani ayke ba, shaidan ya jeta masa a harshensa. Sai Annabi yayi bakin ciki, sai Allah ya goge wannan abin da shaidan ya jefa masa, dan Annabi ya nutsu don Allah masani ne akan abin da shaidan ya jefa wa Annabi, kuma gwani ne na gyara abin da shaidan ya jefa na kuskure. Allah gwani ne akan komai da yake aikatawa. To, wannan abin da shaidan ya jefa a bakin Annabi, sai ya zama jarrabawa ga wadanda suke da ciwo a cikin zukatansu na shakka da munafunci, da kuma wanda suke mushirkai ne ga barin karbar gaskiya.
       Hakika kafirai sun a cikin sabani mai tsawo da Annabi mai tsira da amincin Allah da kuma muminai, ta yadda ya ambaci allolinsu da abin da suke so, su ka ji dadi, daga karshe sai Allah ya lalata wannan abin day a sa su farin ciki sabani, ami tsawo da Annabi mai tsira da amincin Allah da kuma muminai, daga karshe sai Allah ya lallata wannan abin daya sa su farin cikin.
       Sheikh Gumi yace, “idan an dubi wanna tafsir za’a ga akwai karkata mai yawa akan shari’a don an tabbatar da abin da Allah yakore shi tuntuni ba shi ma. Don kuskuren ma shine da aka ce Annabi ma yakaranta sai daga baya mala’ika Jibrilu ya sanar da shi, wannan bai kamata ma ace ya fito daga bakin Annabi mai tsira da amincin Allah ba, saboda tun farko Allah y ace “yak are shi daga fadar wani kuskure da har za’a jingina shi gareshi, saboda Allah yace, “Idan muka aiko manzo to, akwai kariya a gareshi gabansa da baynsa don a tabbatar da cewa wannan manzo ya isar da sakon ubangijinsa. Kuma ilimin Allah a kewaye yake da su, kuma ya kididdige komai, ya kuma kidaya komai kidayawa.” Kamar yadda Allah ya ambace shi a karshen Suratul Jinni. Kuma wannan Magana ma mummuna ce wace bai kamata a fada tab a, cewa a ce manzo ya fadi wata Magana ta kuskure, don Allah ya tsarkake shi da cewa “ina rantsuwa da tauraro idan ya buya, kuma dan uwanku bai bace ba kuma bai ketare haddi ba kuma baya Magana akan son rai, in yayi Magana to, wani wahayi ne aka sanar da shi, kuma wanda ay sanar da shi mai tsananin karfi ne, kuma ma’abocin karfi daidaitacce da kwarjini sa’annan kuma yana sama madaukakiya, kuma sia ya zo dab da dab ya sanar da shi har ya kasance gwargwardon ziri’ai biyu ko ma yafi haka kusanci, sannan ya gaya masa sakon Allah abin da aka masa wahayi, kuma zuciyar Annabi mai tsira da aminci Allah bata karyata abinda ta gani bata kuma kokwanto a kan abinda ya gani, ai ya ganshi a wata sauka ma daya sauko, a inda magaryar tukewa take, anan ne kuma yayin da mai lullube magaryar ya lullube kuma bai karkata ba kuma bai kau da gani ba, lallai ya ga ayoyin ubangijinsa masu girma.
       Kuma ba ni labari mana akan Lata da Uzza, shin kuma gani Lata da Uzza suna da wani amfani ne? a dangana irin wadannan kurakurai ga Annabi, abain da bai halatta bane ga shari’a da hankali cewa tabbatar da haka. Shaidan ba zai sami dama ba balle ma ya jefa wa Annabi wata kalma da bata dace ba, kuma saba nissa da kuma kudurce sabanin zancen Allah, wannan kafirci ne.
       Kuma Shaikh Gumi ya ci gaba da cewa, makasudin wannan aya Allah ne mafi sani cewa Annabawan farko kamar Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah cewa suna samun kurakurai da kuma dimuwa, to, wannan dimuwa sai su zaci cewa abin daidai ne, sai suyi kokarin tabbatar da wannan dimuwa alhali kuskure ne, daga nan sai Allah ya canza musu wannan kuskuren da suka yi niyar aikatawa, sai su dawo ga isar da sakonsa ba tare da wani kuskure ba.
       To, dan wannan dimuwa da ta sami wannan Annabin sai ya zam dalili na kafirtar wadanda suke da shakka a zukatansu da kuma munafurci. Amma masu imani, sai hakan ya kara musu imani, akan imaninsu na da irin wanna ya faru da Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah, tare da manyan shugabanin Makka. Lokacin da Annabi yake tare da manyan makka sai Abdullahi Ibn Ummu, Maktum wanda shi makaho ne, bai sancewa Annabi yana tare da manayn mutanen Makka ba, sai ya shiga kawai yana cewa, “ya manzon Allah, ka sanar da ni abin da Allah ya snar da kai. Sai Annabi ya tashi ya shiga cikin gida yana mai fushi saboda yana kwadyin wadannan manyan shugabanni na Makka su musulunta, sai zauwansa ya yanke Magana da su. Sai Allah ya jawo hankalin Annabi a Suratul Abasa, inda yace masa yin haka laifi ne, saboda fushin da ya yi. Yace, “Ya gintse ganinsa kuma ya bad a baya, don wai makaho ya zo wajensa.” (Abbas). Tun daga nan a duk lokacin da Annabi ya ga Abdullahi Ibnu Ummi-Maktum sai ya girmama shi, ya masa murmushi, yace masa barka da zuwa wanda Allah ya zarge ni a kansa. Sai Annabi ya shimfida masa mayafinsa yace, zauna akai. Irin wannan tuntiben ma ya sami Annabi Yunusa amincin Allah ya tabbata a gareshi, inda yayi wa jama’arsa wa’azi suka ki karba sai yayi fushi da su. Da ya shiga jirgi zai kaura, sai jirgin ya fara tambal-tambal zai kife da su, sai masu jirgi suka ce “idan aka rage mutum daya to jirgin zai tafi daidai. Sai aka yi kuri’a kuma kuri’a ta fado kan Annabi Yunusa sai nan take ya fada cikin ruwa sai kifi ya hadiye shi, daga nan sai yarika cewa ba wani “abin bautawa da gaskiya sai kai Allah, t sarki ya tabbata a gareka, hakika ni na kasance cikin azzalumai”. Allah yace sai muka amsa masa, kuma muke tserar da shi daga cikin bakin ciki, haka nan muke tserar da muminai, (Anbiya’u 88).
       Kuskuren da Annabi Yunusa ya yi shine na yin fushi da mutanensa da suka kafirce wa Allah, sai Allah yace ya koma garesu, kuma ya koma, aka aika da shi cikin mutane sama da dubu dari kuma suka yi imani da shi.
       Haka kuma, irin wannan ma ya sami Annabi Nuhu mai tsira da aminci, inda aak halakar dad an sa mai suna Khan’ana. Inda Annabi Nuhu yace, “Ya Ubangiji lallai dana yana daga cikin iyalaina kuma alkawarin ka gaskiya ne, don kuwa kai ne fiyayyen masu hukunci. Sai Allah mai girma yace wa Annabi Nuhu, “Ya kai Nuhu, shi baya cikin iyalanka, ba ka ga aikin da yayi mummuna neb a, kada ka tambaye ni abin da baka da ilimi a cikinsa.” (Hudu 45-48).
       Irin wannan kuma ya sami Annabi Yusuf mai tsira da amincin Allah, a lokacini daya gayawa wani da aka daure su tare a gidan kurkuku, inda yace ka ambace ni a wajen maigidanka sai shaidan ya mantar da shi wannan sako na Annabi Yusuf har ya zauna a cikin kurkuku kusan shekara goma. To irin wadannan kurakurai sune ya kamata a raba su a cikin tafsirin wanna aya, “Bamu aiko wani manzo ba ko wani Annabi, sai idan yayi burin isar da wani sako na Allah, sai shaidan ya sa masa wani dimuwa, kafin ya isar da wannan dimuwar da shaidan ya jefa, sai Allah ya daidaita wannan sakon da yake so ya isar, sai manzon ya isar da sakon daidai ba dadi ba ragi, don Allah masani ne da wannan, kuma gwani ne akan tsare shi. Don haka burin nan bai halatta a sanya shi wai karantawa bane. To idan muka fassara shi da buri to, mun fita daga cikin laifi, kuma mun dace da abinda aka fassara ayar. Saboda Annabi yace, “Biyayya itace kyakkyawar dabi’a, laifi kuma shine abin da yake maka kaikayi a zuciyarka, kuma yake maka kokwanto a zuciyarka. Don haka ne duk wanda yayi maka fatawa to, ya baka hujjar day a dogara a kanta. Allah ya datar damu a bisa yardarsa saboda baiwarsa da karmacinsa. Shima irin kisser Annabi Dauda ne Allah ya yarda da shi. Malaman tafsiri sun kuskure wajen fassara wannan aya “Shin labarin masu husuma ya zomaka kuwa? Lokacin da suka dirko ta Katanga, sai suka shiga wajen Annabi Dauda, sai ya tsorata da su, sukace, kada ko tsorata dam u, ka mana hukunci na gaskiya, ka yi adalci ka shryar damu a bisa hanya mikakkiya.
       Wannan abokina ne, yana da tumaki (99) ni kuma ina da guda daya tal, sai yace in ba shi ita ai tasa ce, kuma ya buwaye ni cikin Magana. Sai Annabi Dauda yace “ai ya zalunce ka, a yayin day ace ka ba shi tinkiyar guda dayan nan. Sai ya ci gaba da cewa, dama haka wasu abokan hulda sashinsu sai su rika zaluntar sa shi, sai dai wadanda suka yi imani, kuwa irinsu kadan ne. sai Annabi Dauda ya tuno cewa ai wannan hukunci da yayi kuskure ne, sai ya roki Allah gafara, sannan ya fadi yana sujada ya koma ga Allah.” (Swad 21-25).
       Kuma ga mai tafsirin zalalul muhalli, ya yadda da fassara wannan ayar. Yace “Kila ance, jama’a biyu ne don ya dace da dalilin abin da yazo na jam’I a cikin lamirin don ya dace da kalmar jam’I daga cikin lamirin. Kuma a wata ruwaya yace “mutum biyu ne don ya dace da lamirin amma kalmar “mutum biyu ne don ya dace da lamirin amma kalmar “khasmu” ana nufin abokin husma ne guda daya. Kuma a wata riwaya ance su wadannan mala’iku ne suka zo a cikin siffar mutane a matsayin masu husuma a tsakaninsu don su nuna wa Annabi Dauda cewa yayi kuskure, saboda kuskuren daya yi, don an ce shi Annabi Dauda yana da mata (99) ne, kuma akwai wani sahabinsa yana da mata guda daya, kuma Annabi Dauda yana son wannan matar, sai ya tura mutumin wajen yaki kuma ya saka shi jagora wanda a can sai aka kashe shi, sai Annabi Dauda ya auri matar, wai itace ma ta Haifa masa Annabi Sulaiman dansa. Kuma sunan mutumin da Annabi Dauda ya auri matarsa shine Oriya Ibnu Hannani.
       Sai Shaikh Gumi yace “wannan kissa kamar yadda aka kawo ta to, bata dace bad a hankali balle ma a shari’a, da aka aiko Annabi Muhammadu mai tsira da aminci da shi. Kuma mafi yawan mutane da magabata, sun karbe ta, sun kuma gina hukunce-hukunce a kanta. Yadda kisser take a tafsirin ayoyin, an kiftar da ita daga ma’anarta, kuma an canza kalmomin, an kuma rikirkita zubin tsarin Al-Kur’ani, an kuma bata kyakkyawar karantarwa mai kima da kuma darasi mai girma wanda shi ne tsayuwar addini duniya da lahira. Sai yace ma wata kissace don a yi hira da ita, kuma a yi dariya. Sai Shaikh Gumi yace gaba da cewa, “Abin da yake wajibi a ambata shi ne a bar asalinsa yadda Al-Kur’ani ya zo da shi, don an saukar da shi ne da harshen Larabci, kuma an sukar wa Annabi Muhamamdu mai tsira da amincin Allah da harshen san a Larabci don ya yiwa mutane bayani da abin da aka saukar masa kuma ya yi wa’azi da shi, kuma shi Annabi an saukar masa da harshensa na Larabawa kuma ummiyi ne shi don ya bayyana wa mutane abin da aka saukar musu kuma su yi aiki da shi da bin umarni.
       Don haka duk wanda ya kula da wannan sura dukkan ta, da rssa ne da ake koyar da mutane don su tsayu sosai akan tsarkakewa. Kuma aka bayyana mu su cewa, wannan tsari shine mai kyau, kuma duk wani tsari daya saba da tsarin Allah, kamar tsarin Adawa da Samudawa da Fir’auna, wanda karshensa rugujewa ne da kuma rushewa. Amma shi tsari na Allah, shine tabbatacce kuma mai cigaba, wanda in aka yi aiki da shito, zai kafa kakkarfar mulki ga gwamnati. In kuma aka yi kuskure to, Allah mai girma da daukaka zai gyara kura kuran ya kuma gafarta, idan aka yi nadama kuma aka tuba. Domin yadda lamarin yake, bamai laifi bane ga wanda yayi kofarin zartar da hukunci na adalci kuma sai ya sami kuskure, daya gane kuskurensa sannan ya tuba kuma ya koma ga ubangijinsa, to, wannan ba mai laifi bane, don kuwa, hakika Annabi Dauda yana cikin bayin Allah na gari wadanda Allah ya zabe su don a yi koyi da shi nishadi don yin ibada a kowane loakcin daga cikin lokuta, kuma ya karfafa masa mulkinsa ya ba shi hikima da iya hukunci da iya huduba, kuma ga shi alkaline wajen yin shari’a da adalci, yana kuma yin rangwame ga wanda ya yi masa wauta, kuma yana tausayin wadanda suka yi imani suka yi aiki na gari. Yana kuma bakin ciki akan kasha su.
       To, saboda kasancewarsa mutum, yana iya yin wani abin kuma ya kaunaci abin kuma yayi burin wani abin, kamar yadda Allah yace “Bamu aiko wani manzo ba kafin kai ko Annabi sai idan ya yi buri, sai shaidan ya jefa wani abu a cikin burin nasa. Daga bisani sia Allah ya shafe masa abin da shaidan ya jefa masa, sai Allah ya daidaita burin nasa ya tafi daidai da yadda Allah yakeso, kuma gwani akan aikinsa (Hajj, 52). Don haka, abin daya sami Annabi Dauda a wadannan ayoyi. Cikin irin wannan ne Annabi Dauda yana cikin masallacinsa sai wasu mutane biyu suka bullo bata inda mutane suka saba shigo masa ba, sai ya tsorata da ganinsu. Amma daga karshe su ka bashi hakuri, kuma ya hakura, sai mai kara ya bayyana kararsa, inda shi mai rauni ne yana neman taimakonsa akan abokin fadansa, wanda shi mawadaci ne, kuma mai’ikarfi, amma duk da haka yana so ya kwace masa tunkyarsa daya, alhali shi yana da guda casa’in da tara (99).
       Da Annabi Dauda ya ji wannan bayani sai tausayinsa ya kama shi, kuma ya yi fushi har ya fusata da halin wannan mawadaci don yana ganin zai keta haddin Allah akan abin daya yi saboda haka, baima saurari wanda aka kawo karar ba, sai ya zartar da hukunci. To, wannan zartar da hukunci da Annabi Dauda ya yi, wannan shine kuskuran daya fada aciki, wanda da so samu ne, da Annabi Dauda ya tambayi wanda aka kawo kararsa kafin ya yi hukunci akan zaluntarsa da aka yi. Sabdoa wanda ake kara mai karfine kuma mawadaci, bayan ya zame shine mai casa’in da tara (99) shine mafi cancanta ya mallaki guda dayar da ake rigima a kanta. Don haka gaggawar hukuncin da Annabi Dauda ya yi kafin a gama bincike, shine kusken da yayi, kuma ba wani kwamanda daya tura wajen daga, wannan ba gaskiya bane. A lokacin na abinb da bai gama bincike a kansa ba. Don haka ya fadi yana mai sudaja da neman gafarar Allah ya yafe masa kuma ya gafarta masa.
       Daga nan Shaikh Gumi yace, “Ba dama a ce malam zalalu al muhalli mai tafsirin da ya ce shi abokin husumar day a yi kara ba inda abokin karar ya yi maganar cewa ya tabbatar aka cewa haka ne, don a cikin ayar ba’a bayyana cewa ya yi Magana ba, tunda kuwa bai yi Magana ba to, ba dama mukaddara cewa yayi Magana, don haka dole ne mubar zahiri mu koma ga abin daya ke zahiri ba. Saboda haka, kuskuren Annabi Dauda yardar Allah ta tabbta a gareshi, na yanke hukunci kafin sauraron wanda ake kara ya yi bayani sai aka yanke hukunci to yin haka kuskure ne, saboda haka ya tuba. Haka kuma fushi da Annabi Dauda ya yi yana nuna hali ne na zuciya saboda jin abin da aka yi, ya yanke hukunci, kamar yadda Annabi Yunusa yayi akan mutanensa lokacin da ay yi fushi da su don kin sauraronsa da su ka yi in da shi Annabi Yunusa ya tafi yana mai fushi daga barin mutanensa sai ya yi zaton bam u da iko akansa.
       Har ya kai ga kifi ya hadiye shi ya yin da aka jefa shi acikin ruwa inda ya yi ta addu’ar, “La’ilaha illa anata subhanaka in nee kuntu mina-zzalimeen” wato, “Baa bin abutawa da gaskiya sai kai Allah, ni nakasance cikin mutane azzalumai”. Har Allah ya kubutar da shi daga cikin kifin.
       Sheikh ya ci gaba da cewa (na’aja) da ake Magana anan hakikani saniya ce ba mace, mutum ba, kamar yadda aka yi bayani a baya na cewa Annabi Dauda ya yi amfani da mulkinsa don yana son matar kwamandansa, ba. Kuskuren da aka samu shine na tabbatar da hukunci da ya yi kafin a gama bincike. Shi yasa ma Allah mai girma yace ya ba Annabi Dauda kafin wanna kisser da bayan gama kisser. Kuma dalilin da yasa aka kawo kisser Annabi Dauda a Al’Kur’ani wa Annabi Muhammadu din mai tsira da amincin Allah, don ya koyi hakurin da Annabi Dauda ya yi ne na irin musgunawar da mutanensa suka yi masa. Sai Allah y ace “ka yi hakuri akan abin da mutanenka su ka fada, ka tuna kuma da labarin Annabi Dauda ma’abucin karfi mai komawa nega ubangijinsa. Har zuwa inda Allah ya cewa Annabi Dauda, “sai muka gafarta masa wancan laifin daya yi, don shi a wajenmu mai mutunci ne kuma mai kyakkyawar makoma.” Allah ya ci gaba da cewa “ya Annabi Dauda mun sanya ka khalifa a bayan kasa, don haka ka yi hukunci tsakanin mutanenka da gaskiya, kar ka sa son zuciyarka, sai ya batar da kai ga barin bin hanyar Allah, wanda da suka bace daga barin bin hanyar Allah, sina da azaba mai tsanani, saboda mance sakayya ranar saka mako”.
       Saboda haka anan inji sheikh “Ba bu sabani na tabbatar da cewa Annabi Dauda yana da mutunci a wajan ubangiji, don kuwa ayce shi halifansa shi mai hukunci ne ga mutanensa a bayan kasa. Mai wannan al’amari yana da bukatar nutsuwa da tunani da hankali na gaskiya, bai kamata ya bi son zuciya ban a fushi da kuma yarda da abin da bai dace a yarda da shi ba. Saboda mai yin fushi ba zai iya yin adalci ba, wanda kuma ya kuma karkatar da shi ga bin hanyar Allah, wanda kuma ya karkata to, yana da azaba mai tsanani ranar kiyama. Allah kuwa ya tsare Annabawa da haka. Kuma da kuskuren Annabi Dauda ya kasance na cewa ya so wata matace na neman mijinta ya saki matarsa, sai mutumin yaki yarda ya sake ta ko da yake yin haka a shari’arsa ya halatta ya yi haka, amma duk da haka bai yi hakan ba, don kar ya keta mutumci mutumin. Kuma kisser ta ci gaban da cewa “wai da mutumin yaki, ya saki matarsa, sai ya nada shi kwamnada kuma ya tura shi wajen yaki, daga nan sai Annabi Dauda ya auri matarsa.
       To wannan Shaikh Gumi ya ce “wannan al’amari yana kore amanar Annabawansa, kuma wajibine kowane Annabi Allah ya zama mai ha’inci, don ma’anar amana shi ne barin abin da Allah ya hana da kuma rashin aikata mummunan abu da gangan, ha’inci kuwa shine akasin haka. Saboda yaudara ta koru ga komawa ga Allah, don Allah yace Annabi Dauda mutum ne mai mutunci a gurimmu, kuma mai yawan komawa ga Allah. Saboda haka, ba yadda za’a ce mai irin wannan siffa yakoma ga ha’inci. Don Allah yana cewa “Allah baya shiryar da makircin masu ha’inci”. (Yusuf 52). Allah ne mafi sani. Kuma shine muke roko ya datar damu bisa daidai.
 DAGA LITTAFIN; AL-AKIDATUSSAHIHATA BI MUWAFAKATUS, NA MARIGAYI SHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI {R}

HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’A {3}


GURARE UKU DA YA HALATTA A ‘DAGA SAUTI WAJEN AMBATON ALLAH MAI GIRMA
       Ya zo a cikin Mukhtasarul Khalil, babin jihadi cewa daga sauti wato Allahu Akbar, Allahu Akbar:
1.   A wajen yaki. Ya halatta a daga sauti ga mayaki a lokacin day a dau kayan yaki, a lokacin da yake fagen yaki wannan shine alamominsu dare da rana wato fadar a lokacin fuskantar abokan gaba, kuma ana so su yawaita kabarbari.
2.   kuma a waje na biyu da za’a daukaka kabbara shi ne lokacin da za’a fita sallolin idi karama da babba tun daga gida har zuwa isa filin Idi da kuma dawowa gida.
3.   Waje na uku kuma shi ne, wajen aiki Hajji, tun daga mikati har zuwa karshen aiki, da kuma fadar Labbaika har zuwa karshe.
To, in banda wadannan wurare guda uku, ambatar Allah a boye shi ya fi, saboda fadar Annabi mai tsira da amincin Allah lokacin day a ga wadansu jama’a suna daga muryar su da zikiri sai yace, “wanda kuke kiran nan yana kusa da ku.” Daga Sahihul Muslim, daga Abi Musa, “cewa muna tare da Annabi mai tsira da amincin Allah, sai wasu mutane suna daga sauti a sarari suna cewa Allah! Allah! Da karfi, sai yace musu, “yak u mutane, ku hutar da kawu nan ku, wanda kuke kira ba kurma bane ba bebe bane kuma ba wanda baya nan ban e, don wanda kuke kira mai ji ne kuma yana tare da ku.
Bai halatta bag a kowane mutum ya ke tare haddodin da shari’a ta a jiye cikin maganarsa da aikin sa. An sami hadisi daga Sahihul Muslim a Kitabul Ilmi daga Ahnaf dan Kais daga Abdullahi, yace Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace “masu shis-shigi sun halaka. Annabi ya fadi haka har sau uku, cewa masu shis-shigi sune masu kutsawa su wuce iyakar da shari’a ta ajiye, kuma sune masu guluyi masu wuce iyaka a magangannun su da aikace-aikacensu.

GURAREN AMBTAON ALLAH DA YA KAMATA MUTUM YA RIKA ZAMA IN BA’A BIDI’A A WAJEN
       Cewa Abu Hurairah ya rawaito hadisi daga Annabi mia tsira da aminci, cewa “Allah mai girma da daukaka yana da mala’ikunsa matafiya wuri-wuri da ake ayyuka na alheri kamar karatun Al’Kur’ani. Idan suka ga wani waje ana karatun AL’Kur’ani sai su kewaye wajen sashensu da sashensu har ya kai sararin sama, idan an gama karatu an waste, sai su koma wajen ubangiji, sai ya tambaye su alhali ya fi sani daga ina suke, sai yace musu daga ina kuke? Sai su ce “Mun taho ne daga wurin bayinka a bayan kasa suna maka tasbihi suna ambatonka, suna gode maka, kuma suna ambatonka, kuma suna rokoka, sai Allah yace “Me suka roke ni?sai su ce sun roke ka aljanna, sai yace, sun gantane? Sai su ce a’a’ basu ganta ba. To, yaya da sun ga aljannar tawa fa? Sai mala’iku suce, “da sun ganta dab a abinda za su roka sai ita. Suna kuma rokon ka neman tsarinka. Sai yace, “me suke namen tsari daga gare ni? Sai su ce suna neman tsari ne daga wutarka. Sai Allah yace “shin sun ga wutar tawa? Sia su ce? A’a, basu ganta ba. Sai Allah yace “shin da sun ganta fa? Sai mala’iku su ce, “da sun ganta ba wani abu da za su roka sai gafararka. Sai Allah yace, “To, na gafarta musu, kuma na tsare su da abin da suka nemi tsari.” Akwai wani, bawa mai laifi ya zo wucewa, sai ya zauna a cikin su, shi ma gafarar hard a shi? Sai Allah yace, “i, shi ma na gafarta masa, saboda su mutanen alkhairi ne, mai zama da su baya wulakanta.” (Muslim ne ya ruwaito).
       Ya zo a cikin Ihya’ussunna wa Ihmadil Bidi’a na Shaikh Usmanu dan Fodiyo, abin day a zo daga sahabban Annabi mai tsira da aminci ko tabi’ina ko tabi’ittabi’ina, to ya wajaba ayi riko da shi ayi aiki saboda kaiwan su kololuwa bisa bin Sunnah da nisantar bidi’a.
       Shaikha Abubakar Gumi yace, “In an tambaye ka abinda yake da dalili a shari’a, amma ba’a sami wani yayi aiki da shi ba daga cikin magabanta, shin wannan sunnah ne ko bidi’a? sai Ahmad Zaruk yace “wannan yazo a cikin wani littafi mai suna Umda’itul Muridul Sadiqu, Imam Malik ya fada cewa wannan abin bidi’a ne. don su magabata basu bar aiki da shi ba, sai don wani dalili da su kedashi a wajensu, don su sun fi kowa kwadayin alkhairi, kuma sun fi kowa sanin sunnar Annabi mai tsira da amicin Allah. To, wannan ya yi daidai da fadin dan Mas’udu ya yin da yaga wadansu mutane sun taru suna zikiri, sai yace “wallahi, hakika kunzo da bidi’a, abisa zalunci, yanzu ku kunfi sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah ilimi ne? ibnul Hajji ya ambaci wannan cikin littafinsa (Madakhal). Don Karin bayani, a duba littafi mai suna Madakhal.
       Haka kuma, Imam Shafi’I yace, “Dukan abin da aka same shi yana da sanadi to, ba bidi’ah bane, ko da magabata basu yi aiki da wannan ba, sabo da kila suna da wani uzuri day a hana su aiki da shi a wannan lokaci. Ko kuma suna da wani dogaro da yafi wancan lokaci a wajensu, ko kuwa sub a su sami wannan hadishin ba, don kuwa da sun samu, da sunyi aiki da shi, shi kuma hukunce – hukunce ana samunsa ne daga shari’a kuma ga shi shari’a ta tabbatar da shi.
       To akan wannane suka saba cikin fahintarsu wajen kamar a taru don a sauke Al’Kur’ani, ko kuma irin zikirin nan da ake haduwa ana rangaji da daga murya, ko umarni wajen yin addu’a na cewa a karanta Fatiha da Kulhuwa sau uku – uku da sauransu.
       Saboda an sami hadisai da suke nuni da yin addu’o’I to amma ba’a sami cewa a yi a cikin umarni na jam’iba, kamar inda Annabi yace ku roka wa dan’uwanku gafara yayin daya mutu aka je bisonsa amma bai jagorance sub a a yin addu’ar, sai ya bar kowa ya yi addu’a gwargwadon inda zai iya a makabartar.
       Kuma Imam Shafi’I ya yi bayani cewa “In dai an sami hadisi cewa Annabi yace a yi to, ko yaya aka yi abin a wajensa an yi daidai.
       Shi kuma Imam Malik cewa yayi, “duk wani hadisi da aka bada umarni in har ba’a yi masa kaifiya ba sai wasu suka ba shi kaifiya to, sun yi bidi’ah. Don kuwa akwai shubuha a ciki.
       Kuma an samu daga Annabi mai tsira da amincin Allah yace, “kada wani ya yi sallar La’asar sai a Bani Kuraiza, sai La’asar ta yi musu a kan hanya basu isa Kuraiza ba, saboda haka sai wasu daga cikin sahabbai suka yi sallah don fahintarsu da cewa Annabi yana nufin da su yi gaggawa ne, to sai gashi basu yi gaggawa ba har lokaci ya yi, sai suka yi sallah, to, amma wasu basu yi ba, said a suka isa Bani-Kuraiza sannan suka yi sallarsu, don su a fahintarsu Annabi yayi musu umarni ne cewa kada su yi sallah sai a can.
       Don haka, da suka dawo sai suka baiwa Annabi labari cewa wasu sunyi sallah kafin su isa saboda ganin lokaci ya kure amma wasu ba suyi ba saboda bin umarni cewa sai sun kai kamar yadda kace. Sai Annabi yace “Shi kenan kowa sallarsa ta yi daidai. Wannan ya na nuna wa kenan cew ain an sami sabanin fahinta akan abu to, ba’a zarginsa indai an sami asalinsa daga sunnah kamar yadda hadisin ya nuna.
       Sai Shaikh Abubakar Gumi yace “yana daga cikin bidi’ah mummuna a yi aiki da nassi ko da an sami nassinsa daga sunna in dai an karkatar da shi bisa son zuciya, kamar yadda wadnsu suka dauka cewa a buga dundufa (ganga) don sanar da aure, sai suka ce ya halatta a yi kade-kade a lokaci shagalin aure, kamar masu buga mandiri a loakcin da suke wani biki saboda fadar cewa za’a buga tambari ko dundufa don sanar da shagalin aure. Malam ya ci gaba da cewa masu wannan fahinta sun yi kuskure, don buga tambari ko dundufa ana yinsa ne a lokacin sanar da aure, saboda haka karkatar da mandiri a kan irin wannan akwai wargi a ciki don ba shi ne wasan da aka bada umarni ba. Kuma mulamai basu yi wani sabani a kai ba. Saboda haka ba addini bane. Saboda haka buga tambari ko dundufa yana da asali, amma mandiri ba shi da wani asali a shari’a don haka ya zama wasa, wato wargi kenan a cikin addini, abin daya zamo wargi, Usman Dan Fodio yace “ai kuwa wargi a cikin addini bidi’ahne.
       Kuma Shehu Usman dan Fodiyo ya fada a cikin littafinsa mai suna Ihya’ussunnah wa Ikhmadul Bid’ah “wace kade kade da raye – raye bidi’ah ce harantacciya. A lokacin da yake ambataon bidi’o’I haramtattu yace” yana daga cikin bidi’o’I haramtattu, akan irin abin da mutane suka haddasa akan babul-ihsan (wato raye-raye da) wake-wake da kade-kade da shirya kasidodi, wai kyuaktatawa ne a wajen sufaye. Sai shehu Usman Dan Fodiyo yace “a wajen janhuran malami wannan bidi’ah ce harambatacciya a shari’ah.
       Wani Malami mai sun Izzudin acikin littafin sa, Kawaidul Ahkami, y ace malaman sufaye suna da matsayi wajen sauraron:
(1)        Akwai wandan da ilimi yak an zo musu da natsuwa da halaye masu kyau a lokacin da suke sauraron Al-Kur’ani to wadannan sune mafifitan masu sauraro.
(2)        Masu martaba ta biyu, sune wadanda suke samun abubuwa na nutsuwa ta hanyar sauraron wa’azi da tunatarwa sai suji sun nutsu kuma su ji da di.
(3)        Martaba ta uku kuma akwai malaman sufaye da suke samun nutsuwa ta hanayr zikiri da wake-wake da karanta kasidodi wai akwai jin dadi da hutawa ta haka.
(4)        Masu martaba hudu kuwa cewa suke yi wai “dadi na zuwa musu ta hanyar sauraron kade-kade da wake-wake ta hanyar buga ganga kamar mandiri da sauransu. Sai dai malam yace duk wanda ya tabbatar haranmunne, amma dai yafi samun nutsuwa in yana sauraron haka, to wannan ya zama mai kuskure. Wanda kuma yace ta halatta saboda koyi da malaman da suka ce wannan sauraro haka ne to ya bar tsantseni ga sauraronsa amma mai kyautatawa ne ga iliminsa da halaye na wannan abu.
(5)        Wasu kuma sunce wadanda nutsuwa take zuwa musu da jin dadi yayin sauraron irin wadannan kade-kade da raye-raye kamar sauraron jita da algaita ko kakaki da sauraron abubuwan kade-kade na zamani da ake yi ayau sune natsuwa a gare su, to suna aiki ne da abinda addini ya haramta. Kuma in ya sami jin dadi da wadannan abubuwa da ayke sauraro to, ya zama mai hada abubuwa kyawawa da munana wato mai amfani da mai cutarwa, to mai irin wannan hali yana zaton cewa kyauwawan halinsa za su mamaye munana, to mai wanna hali yana ganin cewa halal ne yake sauraro. Sai malaman sufaye suka ce in ya sami natsuwa to ya zama halas a gare shi. Kuma in ya hada kade-kade na batsa wato na haduwar maza da mata to, yana nuna cewa ya kara sha’awarsa kenan da sabonsa.
Shehu Usman Danfodiyo yace: “Sauraron kade-kade da raye-raye kamar yadda sufaye suka ce yana kara son addini da nutsuwa, wannan yana nuna tsaurin kai ne da keta hukunce-hukuncen Ubangiji, don kuwa da yana da kyau to, da Allah ya umarci annabawa da su rika sauraro da aikatawa kuma suna kwadaitar da mabiyansu don su rika yi. Kuma yace ba wani labari da aka samu daga annabawa ko manyan maluma da suka gabata na cewa wai sauraron kade-kade yana kara sa natsuwa da shiriya ga mai yinsa. Kuma ga shi Allah yace “addinin say a cika, inda yake fadin cewa, “A yau na cika muku addinin ku.” To da ace sauraron kade-kade da wake-wake addini ne, to da Annabi ya fada kafin cikar addinin.
Haka kuma Annabi mai tsira da amincin Allah yace “ina rantsuwa da wanda numfashina yake hanunsa, ban bar abinda zai kai ku zuwa aljuannah ba, kuma ya nisanta ku ga barin wuta said a na umarce ku. Kuma yace ban bar abin da zai kai ku wuta ba, ya nesanta ku ga barin shiga aljannah said a na hane ku, kada ku aikata shi.
Shikah Abubakar Gumi yace, “Duk wadannan maganganu da ake yi akan sauraron kade-kade neb a akan aiki da suba. Kuma ba wani wanda zai ce sauraron Kur’ani da za’azi da karantarwa bai halatta ba, kuma duk wanda ya musanta sauraron Kur’ani da wa’azi da karantarwa cewa ba halal bane to, kafiri ne. Haka ma buga dundufa da wake-wake a loakcin bukukuwa na ranar Idi yadda addini ya nuna.
Kuma abin da aka ce haramun shine, hada kade-kade da raye-raye da ambaton sunan Allah da manzonsa. To, masu yin irin wannankam, sun zama masu aikata munanan ayyuka. Matukar basu bari ba Allah ya yi masu alkawari da yi musu azaba ranar Alkiyama, inda yake cewa, “masu irin wannan kade-kade da wake-wake a masallaci, sallar su bata zama ba, addu’o’in sub a su zama ba a masallaci sai dai sowa da kuma tafi. To, za’a ce musu ku dandani azaba ranar kiyamasaboda izigili da wargi da kuka yi. (Anfal 35).

MATSAYIN DA SUFAYE SUKE BA MABIYANSU
       Yana daga cikin bidi’ah mummuna harma ya kai ga kafrici, na tsarkake kai da malaman sufaye su ke baiwa shehunansu, kamar ace “wannan gausi ne, wanda suke basu matsayin da kuma tsoratar da mutane akan kada su saba wa irin wadannan ko da abinda suka ce ya sabawa shari’ah to, dole ne su yarda. Yadda suke cewa yasan ilimin gaibi, na abin da ke sarari da na boye, kamar su ce suna sa mutum ya yi arziki ko su sa shi ya talauce ko wata cuta ta same shi da makamantansu.
       Sheikh Gumi yace, “duk wadannan abubuwan da ake dangana su ga sufaye ba gaskiya bane, kuma duk ayyuka ne na sahidanun malamai da suke saka shi a cikin addini, kuma abubuwane da suka dauko su daga Yahudu da Nasara, domin kuma duk wanda yake ganin zai iya azurta wani ko ya talauta shi ko ya san wani ilimi na boye da na sarari to, wannan kafirci ne saboda fadin Allah da kuma sunnah da haduwar malamai sunnah.
       Allah yana cewa “kace sama da kasa ba wanda yasan gaibi sai Allah da kuma sunnah da haduwar malami sunnah.
       Allah yana cewa “kace sama da kasa ba wanda yasan gaibi sai Allah. Kuma ba wanda ya san ranar da za’a tada matattu sai Allah.” (Namli 65). Kuma Allah yace ya Annabi “Kai ba ka iya mallaka wa kanka abin da zai cutar da kai, sai abin da Allah ya dora maka, da kasan ilmin gaibi da ka yawaita aikin alheri dab a wani hadari da zai same ka, don haka ne kai mutum ne mai gargadi da albishir ga muminai. (A’araf 188). Allah ya ci gaba da cewa, “wanda Allah ya shiryar, shi ne shiryayye, wanda kuma Allah ya batar to, sune masu hasara. (A’araf 178). Kuma Allah yace wa Annabi mai tsira da amincin Allah, “kai ba ka da ikon shiryar da wanda kake so, sai da Allah shi ke shiryar da wanda ya so, don shi ne mafi sanin shiryayyu”. (Kasas 56). Kuma Allah yace “kace kaifa mai kira ne zuwa ga Allah, ni kuwa b azan hada Allah da kowa ba, kuma ka gaya musu ni ban mallaki batar da ku ba haka shiryar ku, kuma ka gaya musu kai in ka saba wa Allah, ba wanda zai tserar da kai, kuma baka da wata mafaka. Ni dai mai isar da sakon Allah ne kuma manzon Allah, duk wanda ya sabawa Allah da manzonsa makomarsa jahannama ce, kuma zai tabbata har abada”. (Jinnu 19-20). Wadannan sune hujjoji daga wajen Allah cewa ba wanda ya san gaibi ko wani ilimi na badi’ni da zai iya talauta kako azurtaka ko kasha ka ko raya ka, sai Allah.
       Dalilai kuma daga sunnah gasu kamar haka: Daga Abu-haurairah, “Annabi mai tsira da aminci yace “Ba wani wanda aikinsa zai tsear da shi. Sai wani mutum yace “hyar kai ya manzon Allah? Sai yace ‘e’ har ni ma, sai dai in Allah ya lullube ni da rahamarsa, amma duk da haka kowa ya yi kokarin gabatar da ayyuka masu kyau”. (Imam Muslim). Kuma Imam Nawawi yayi Karin bayani cewa wannan hadisi game da mazahabar malaman sunnah ba wani mai tabbatar da hukunci cewa wane dan aljannah ne ko wane dan wuta ne ko halal ne ko harma, sai in shari’a ce ta bayyana haka. Wanda kuma ya dauki matsayin halatta wani abu ko harmata wani abu to ya yi kama da Bayahude ko banasare.
       Saboda Allah ya siffanta Yahudu da Nasara da suke koda kawunan su da cewa “mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa ne” yayin da suke dauki hukunci a hannunsu, inda suka ce ba wabnimai shiga aljannah sai Bayahude ko Banasare. Sai Allah ya musu raddi da cewa “shin baku ga wadanda suka tsarkake kawunansu ba, sukace su ‘ya’yan Allah ne? karya suke yi. Allah ne yake tsarkake wanda yake so, kuma Allah ba zai zalunci kowa ba koda kamar fatar jikin dabino.
       Ya ci gaba da cewa “duba kaga yadda suke kirkirar karya su jingina ga Ubangiji? Wannan ya zama musu babban lafifi, mummuna a wajen Ubangiji. (Nisa’I 49).
       Kuma da Bukhari da Muslim suna cewa, Annabi ya ji wani mutum yana yabon wani mutum sai yace, “Amma ka sare wuyan abokinka in ya zama ba yadda zaka yi sai ka yabi wani to, ka ce ina zaton wane mutumin kirki ne, sabdoaba wani wanda zai iya tsarkake wani a wajen ubangiji). Kuma daga Khalifa Umar Allah ya yarda da shi cewa “duk wanda yace shi mumini ne to, shi kafirine, wanda kuma yace, shi malami ne, to shi jahili ne, wanda kuma yace yana da aljannah to shi dan wuta ne. daga Ibnu Khasir a cikin littafinsa. To, wadannan hujjoji sune suka hana mutum ya dauki hukunci a hannunsa na cewa wane dan Aljannah ko dan Wuta ne. 
DAGA LITTAFIN; AL-AKIDATUSSAHIHATA BI MUWAFAKATUS, NA MARIGAYI SHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI {R

HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’A {2}


MUNANAN BIDI’O’I ABIN ZARGI
       Yana daga cikin mummunar bidi’a abin zargi ga mutum yin hukunci da ra’ayi da kuma bautawa Allah bad a abin day a saukar ba, wato “Kur’ani da sunnar Annabinsa” sannan da sabawa fassarar mutanen kirki (Ahlus Sunnah)
       Don haka ne wasu malamai suka ce “wanda ya bautawa Allah don yana son sa kawai to, wannan ya zama mai son kai wato (Zindiki). Haka kuma wanda ya bautawa Allah don tsoransa kawai to wannan dan tafarkin haruriyi ne kawai (wato mai tsaurin kai). Amma wanda ya bauta wa Allah don kaunar rahama, to, wannan dan tafarkin murji ne na darika, amma wanda ya bauta wa Allah don tsoronsa da kuma sonsa da kaunar gafararsa to wannan shi ne cikakken mai imani da tsoron Allah.
       Kuma yana daga cikin bidi’a abin zargi son Allah kawai a cikin zuciya ba tare da aiki ba, don kuma son Allah da fadin haka a baka kawai ba imani bane da zai tserar da mutum a gobe lahira ba, saboda Fir’auna da mutanensa sun san gaskiyar Annabi Musa da Haruna amma bas u yi imani da su ba. Don haka ne Annabi Musa ya gayawa Fir’auna cewa, “Lallai kasan ba wanda ya saukar da wadannan hujjoji sai Ubangijin sama da kasa (Isra’il 102). Tabbata abin gaskiya ne don haka Allah ya kara tabbatar da cewa sun musanta ta alhali kuma zuciyar su ta sakankance gaskiya ce, amma saboda zalunci da wuce iyaka, sai aka halakar dasu “Daba kaga yaya karshen wadanda suka yi girman kai.” (Namli 140).
       Don haka, Ahlul kitabi sun san gaskiyar Annabi Muhammad mai tsira da aminci Allah kamar yadda su ka san ‘ya’yan su, ammamsu kayi gaba da shi.
       Haka ma Iblis bai jahilci al’amarin Ubangiji ba har ma rokon Allah ya yi cewa, “Allah ka jinkirta min tsawon kwanahar zuwa tashin kiyama (Hujrat 36). Kuma shaidan yaci gaba da rokon Allah yana cewa, “Allah saboda halakar da ni da kayi, sai na halakar da bayin ka baki daya sai dai wadanda ka tsarar. (Hujirat 39). Kuma shaidan yaci gaba da addu’a cewa, “Na rantse da zatinka wallahi sai na batar da su gaba daya, sai dai bayin ka da ka tsarkake su.” (Swaad 72).
       Saboda haka, wannan akida itace ake cewa darika ta jahamiya (wato ana son Allah amma kuma ba a bauta masa da gaskiya suna ganin cewa jahilci shi ne kawai kafirci, wai in mutum ya san Allah ko bai bauta masa ba to bai yi laifi ba. Saboda haka wannan itace akidar da wadansu malaman da suke kan su a wadansu garuruwa na Afirka (wato tarbiyyar malaman sufaye wadanda suke cewa suna ganin Allah).
       Haka kuma yana daga cikin bidi’ah mummuna abin zargi cewa bayan an taru a cikin wasu harkoki in an yi addu’o’I da salatin Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah sai kuma a ce sai an rufe da salatul Fatihi, wai cewa it ace ta rufewa don karbar addu’o’in, in aka yi haka shine gaskata abubuwan da suka zo a cikin littafinsu mai suna Jawahirul Ma’ani wa Bulgul Ama’ani juzu’I na daya fasali na biyu, shafi na 140,” inda suka ce an tambayi Shehu Tijjani, shin labarin da Annabi Muhammadu mai tsira da amanci ya bayar bayan mutuwarsa yana dai-dai da abin day a bayar kafin mutuwarsa? Sai Shehu Tijjani yace, “Sako na gaba daya da yake zuwa wajen Annabi mai tsira da aminci, an nade shinfindarsa ya kare (wato ba’a samun sa). To amma wanda yake zuwa wajen mutane na musamman to, shi kan yana nan bai yanke ba, don haka ma salatil fathi limauglika ta fi dukkan aiki na alheri na ibada ta kowace fuska aka yi abin, sake ba wani dabaibayi. Haka kuma ta fi komai sai dai wanda yake cikin da’ira na zikiri fai’da, don wanda ya karanta wannan shine karshe.
       Sannan Shehu Tijjani ya ci gaba da cewa, “sai dai wadanda suke da karancin kwakwalwa in kace haka zai yiwu sai su yi musun wannan maganar da aka fada. Kuma ya ci gaba da cewa, “wanda ya yi musu cewa abin da ake baiwa Annabi lokacin da yake raye ya yanked a kuma wanda yake bayarwa bayan mutuwarsa to, ya jahilci al’amarin Ubangiji, kuma ya munan ladabi ga Annabi mai tsira da aminci, kuma in bai tuba ba to, ana masa zaton zai mutu kafiri.
       Malam ya yi bayani cewa, “irin wannan Magana ko da yake an dangana ta da Annabi mai tsira da amincin Allah, to ta wuce matakin shari’a mai tsarki. Saboda duk abin da bai zamo cikin shari’a ba ba za ayi aiki da shi ba. Saboda Qur’ani da Hadisi suna bayanine akan cewa Annabi yana bin umarni ne wajen isar da sako, ba shi ne yake bada sakon ba. Allah ne yake ba shi. Saboda fadar Allah mai girma da daukaka cewa, “Ya kai Manzo ka isar da sako daga wajen Ubangijnka, in kuma kabar wani abu baka isar da shi ba to shine ba ka isar da skon ka ba. (Ma’idah 67). Kuma Allah yace, “ba a saukar da wani hukunce hukunce sai loakcin rayuwar Annabi mai tsira da amincin Allah lokacin day a ked a rai, saboda fardarsa cewa, “yaku wadanda ku ka yi imani, kada ku tambayi wandasu hukunce hukunce na abubuwa, wadanda idan aka yi muku bayani a kansu za su bakanta muku rai, in kuwa ku kace sai kun tambaya , to lokacin saukar Al-Kur’ani za a yi muku bayanin hukuncin abin lokacin da hukuncin ke sauka. “Saboda haka, wannan aya tana nuna cewa hukunci yana sauka ne lokacin da Annabi mai tsira da aminci yake raye. Al’Kur’ani ya cika, addini ma ya cika kuma wahayi ya yanke.
       Saboda fadar Allah Madaukakin Sarki, “A yau kafirai suka debe tsammani daga addininku don haka ne ka da ku ji tsoronsu, sai dai ku ji tsoro na ni kadai. A yau ne na ciki addininku na ciki muku ni’imata a gareku, mun zaba muku Musulunci shien addininku.” (Ma’idah 3).
       Kuma Allah mai girma ya yi bayani cewa Annabi ba shi ne mai shar’anata shari’a ba, sai dai shi dan aike ne da yake isar da aike. Kuma Annabi ba shi da ikon ya kara wani abu daga fadar Allah Madaukakin Sarki cewa, “Al’Kur’ani saukakkene daga Ubangijin Talikai da Annabi ya kara wani abu a cikin sakon Allah, dam un kama shi da hannun dama mun tsinke masa jijiyar laka ta wuyansa, kuma ba wani daga mutane da zai iya tsirar da shi daga wannan kamu da za mu yi masa.” (Haakah 43-47).
       Kuma Allah ya shaida cewa Annabi mai tsira da aminci ya isar da wannan sako ba dadi ba ragi, inda yake cewa, “Baya Magana da son zuciyarsa, sai dai idan wahayi ne aka aiko masa. (Najmi aya 4). To, wannan ya nuna cewa ba wani abin da zai zo daga Allah bayan wannan.
       Sheikh ya ce, “Ba a sami wani hadishi da yake nuna cewa bayan mutuwar Annabi akwai wani abu da zai zo bayansa ba sai dai ma Annabi mai tsira da aminci ya yi tsawa cewa duk wani abu da aka ce shi ya fada a bayansa to bata ne. don kuwa akwai wani hadisi daga Irbadu ibn Sariyata ya ce, “Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce, nah ore ku da bin sunnata da sunnar mamayana (Khalifofi na)- Abubakar, Umar, Usman da Aliyu – su shiryayyu ne masu shiryarwa. Ku yi riko da ita sosai, kada ku sake ta. Kuma na hane ku da bin fararrun abubuwa da aka kirkire su, kowace bidi’ah bat ace, kuma batacce a wuta yake.” (Mutane hudu ne suka ruwaito, sai dai Nisa’I, Tirmizi da ibn Hibban sun inganta shi).
       An karbo daga Shuraiful Khuza’I, Allah ya kara masa, yarda y ace, Annabi mai tsira da amincin Allah ya fito gare mu sai yace, “wannan Al’Kur’ani da ayke hannunku, gafensa yana hannun Allah ne, kuma gafensa yana hannunku in ku kayi riko da shi to ba za ku bata ba har abada. (Dabra’ni).
       Haka kuma ba wani daga cikin malamn hadisi da ya ruwaito Salatil Fatihi. Haka kuma ba wani daga cikinsu day a dangana Salatul Fatihi cewa daga Annabi ta ke, haka kuma ba wani daga Tabi’ina da tabi’ittabi’ina da ya danganta shi cewa daga Annabi yake, balle a gaskata shi kuma duk wani aiki da ba’a same shi daga wadannan ba to, bi’di’ah ne kuma bidi’ah bat ace, saboda haka duk a bin da yazo ba daga Manzon da Sahabbansa ba to, bata ne. kuma duk wanda ya canja wani abu daga addini, ba zai sha rowan Al’kausarar ba ranar tashin Kiyama don ya zo a cikin littafin Risalah ta Abi Zaidi Al-Kirawani, Allah ya yi masa Rahama yace, “A yi imani da abin da Allah ya saukar, wadanda suka yi imani za su sha rowan Al-Kausara, sai dai wanda ya can za addini wato ya zama dan bidi’ah ba zai sha ba.
       Kuma an samu daga Sahihul-Muslim a cikin babin Guraban Alwala, cewa jama’a za su zo da haske a guraben da suke alwala don su sha rowan Al-Kausara sai mala’iku su hana su suna koransu. Sai Annabi mai tsira da aminci yace, “Ku zo ku sha ai jama’atane. “Sai mala’iku su ce “Ai kuwa bayan ka sun yi bidi’ah sun canja addini, sai Annabi mai tsira da aminci ya ce, “To ayi nesa dasu, ayi ne sa da su.
       Haka kuma wanda ya raya cewa Annabi mai tsira da aminci ya boye wani abu a rayuwarsa don ya isar da wani bayan mutuwarsa to, hakika an tauye mutuncinsa don an tuhumi Annabi, wannan kuwa kafirci ne a sarari a wajen dukkan malaman sunnah.
       Saboda haka, irin wadannan maganganu na Salatuk Fatihi suna nan da yawa a cikin littattafan ‘yan darika wanda bai halattaba ayi aiki da su. Saboda duk wanda yayi aiki da su to, ya bi son zuciyarsa, kuma ya bata, ya kuma yi koyi da Yahudu da Nasara. In da Allah yace, “lokacin da Manzo ya zo da sako daga wajen Allah yana mai gaskata abinda ya tarar da su, sai wasu jama’a daga ma’abota littafi suka jefar da littafin a bayansu kamar basu san cewa Allah ya saukar da wani littafi ba, sai suka bi abin da shaidanun malamai suke yadawa akan mulkin Annabi Sulaimanu alhalin shi Annabi Sulaimanu bai kafirta ba sai dai su shaidanun malaman ne suka kafirya don suna koyar da sihiri kuma suka yada cewa Haruta da Maruta suke koyarwa mutane sihiri sai Allah ya karyata su don kuwa Haruta da Maruta basu koyar da sihiri ba don kuwa sihiri kafirci ne kuma lokacin da mutum zai koyi sihiri sai mala’iku su ce kafirci ne fa ka yarda a koyar da kai?
       In ya ce yarda sai su karnatar da shi, sai Allah ya karyata masu cewa mala’iku sun koyar da sihiri kuma ya ce mala’iku bas u koyar da kowa sihiri ba balle su ce masa wannan fa fitina ce kada ka kafirta. Kuma Allah ya ci gaba da cewa mala’iku bas u koyar da sihiri, sai dai masu koyarwa miyagun malamai masu koyar da abin da zai bata tsakanin miji da mata kuma su malaman ba za su iya cutar da kowa ba said a izinin Allah Madaukakin Sarki. Kuma duk wanda ya koyi sihiri to, zai cutar da shi neb a zai amfanar da shi ba, kuma su sani tabbas duk wanda ya koyi sihiri ba shi da rabo a lahira, saboda fadar Allah cewa, “ir da abin da suka koyar da kawunansu da shi, da sun sani dab a su yi ba. Da a ce sun yi imani da abin da Allah ya saukar, suka kuma ji tsoron Allah shi kadai to da ladan da za su samu daga wajen Allah, da yafi musu koami lada inda sun sani? (Bakara 100 – 103).

KARIN BAYANI AKAN TAFSIRIN AYOYI UKU DA SUKA GABATA
       Shaikh Abubakar Muhmdu Gumi yace, Tafsirin wadansu ayoyi a ganina, Allah shi ne mafi sani, cewa Yahudawa suna daga cikin al’adun suna daga cikin ka’adun su na saba alkawari, wanda duk loakcin da aka yi alkawari da su sai sun saba, saboda sun kasance sun san gaskiyar Annabi Muhammadu mai tsira da aminci yadda aka ambata a cikin littafin Attaura, Annabi Musa cewa ya fada musu duk Annabi da ya zo a bayansa to, su yi imani da shi, sai ga Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah ya zo musu, ko kuma wadansu daga cikin annabawa sai suka karyata su. Sai Allah ya bada labari akan su ya ce, “wasu daga cikin ma’abota littafi sun jefar da littafin Allah a bayan bayansu kamar ma basu san Allah ya saukar da wani abu ba, sai suka bi abubuwa da shaidanun malamai suke yadawa na mulkin Annabi Sulaiman bai kafirce ba, sai dai shedanun sun e suka kafrice don suna koyar da mutane sihiri kuma suna cewa Haruta da Maruta sune suka koyar da sihiri a garin Babila to, sai Allah ya karya ta su cewa ba’a saukar da wadansu mala’iku biyu Haruta da Maruta a Babila kuma ba su koyar da wani sihiri ba a Babila. Suma malaman Yahudu da sun san haka, da kuwa ba zasu bata lokacinsu wajen neman sanin ilimin sihiri ba.
       Malam ya yi Karin bayani cewa karya da ake yadawa na cewa Annabi Sulaiman ya mllaki mutane da sihiri to, anyi ta bayanin cewa Annabi Sulaiman bai yi sihiri ba, balle ya mallaki mutane da shi, don kuwa mulkinsa daga Allah yake, kuma yak ore karya cewa Haruta da Maruta sun yi sihiri. Yaya za’a ce mala’iku sun yi sihiri? Kuma ayar ta kara bayyana cewa yin sihiri kafirci ne wanda yayi ya kafirta.

DALILIN DA SUKE BAYARWA NA NEMAN ILIMI SIHIRI                                
       Cewa lokacin da Allah ya aiko Annabawa yana basu wadansu mu’ujizoji din ya karfafa su isar da sakaonsa tare da gajiyar da wanda yake musun Annabawa. Su kuma waliyai, akwai karamomi da ake basu wadanda suka saba da al’adun jama’a don taimaka musu kan tsayuwa da kiran da suke yi zuwa ga Allah da tsayar da addini. Amma suma basu san da afkuwar abin ba, sai dai yardarm su da cewa Allah baya lalata aikin masu aiki na gari. To, da wannan zamu gane bambancin mu’ujizar Annabawa da karamar waliyai.
       Domin shi Annabi yana samun sako daga wajen Allah, amma shi waliyi baya samun sako daga wajen Allah, sai dai ya bi abinda aka saukarwa Annabi daga wajen Allah.
       Kuma akwai wasu halaye batattu da suka bayyana daga wajen wadansu mutane shakiyai, wadanda za kaga ga abubuwa na ban mamaki, na rufa ido, da za su rika yin a jayo hankalin mutane don su yarda dasu, kamar dujal da ‘yan damfara da bokaye da suke neman wadansu dabarbaru don su wawantar da hankulan mutane don su yarda dasu, wannan hanya kuma itace ta sihiri da zai nuna wa mutane cewa abin da yake yi din nan gaskiya ce, kamar nuna takarda yace zai maid a ita kudi ko igiya yace zai maid a ita macijiya da makamantansu to, wadannan sune sihiri, kuma masu irin wadannan abubuwa ko day a zama kamar gaskiya ne wato abin ya kasance to daga baya Allah zai bata abin domin Allah baya gyara aikin mai sihiri kuma baya karbarsa kuma duk abin day a zo da shi ba zai yi nasara ba har abada.    

KASHE KASHEN SIHIRI
       Iman Razee ya ambaci kasha – kashen sihiri guda takwas kuma ya fadi kyawawan halaye, sannan ya fadi munana dabi’u tare dasu, wanda a cikin ya ambaci kambun baka daga cikin sihirin sai dai shi Shaikh Gumi ya cire kambun baka daga cikin sihiri saboda dogaro da cewa Annabi yace. “Tofi bai halatta ba sai wanda aka yi wa kambun baka ko wani abu kamar sarar maciji ko kunama daya sari mutum to, anan kam ya halatta a yi tofi.
       Saboda haka a ganin Shaikh Gumi kasha – kashen sihiri saura bakwai kamar haka :
(i)                  Sihiri na makaryata kamar “kashdaniyuna” (wato wasu mutane ne masu bautawa taurari a lokacin Annabi Ibrahim tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kuma taurarin guda bakwai ne suna raya cewa sune masu juya al’amura suna zuwa da alkhairi da kuma sharri sune wadanda Allah ya aiko Annabu Musa da Annabi Ibrahim (AS) don ya bata wannan akida tasu ta wannan mazhaba. Duk da hadisin da suke hana irin wadannan amma har yanzu akwai wadansu da suke yin haka. Wato suna duba da taurari ta hanyar bokanci.
(ii)                Akwai kuma masu duba da aljanu sai su rika neman hanyoyin da za su rika saduwa da aljannu ta hanyar sanya turaren wuta da kuma hawa bushiya da yin tsirara. Irin wannan nau’o’in sihiri sune ake kira da (a aza’ima) wato masu Magana da aljanu ko masu cire aljannu. Shi ma wannan aiki ne na shihiri, kuma a halin yanzu ya yi yawa a cikin mutane a yau.
(iii)              Tahayilat (raya wa mutum ganin wani abu a sarari), shi ma nau’I ne na sihiri wanda ake ce masa rufa-ido da damfara da kame idanun mutane. Yadda ake aiwatar da irin wannan sihiri shine mutum yana yin wani abu ba tare da an gan shi ba daga nan sai a ga an kawo wani abu a gaban mutane ba tare da an ga lokacin da aka yi shi ba, kuma a halin yanzu sunanan da yawa anan yinsu. Kuma shi ne irin sihirin mutanen Fir’auna.
(iv)               Karama (amma bata waliyai ba), wani irin sihiri ne da wasu suke ganin cewa akwai nuna wata karama da suke ganin cewa za su iya dora su ko ta kowane hali. Irin wadannan masu sihiri suna iya kawo hadisi na karya su ce ya halatta a yi haka duk da cewa sun san Annabi mai tsira da aminci ya ce “duk wanda ya kagi wata karya ya jingina da ni to, ya tanadi mazaunin sa a wuta.” Kuma ya ce, “ku bada labari a kai na amma kada ku yi mini karya don duk wanda ya yi mini karya to, zai shiga wuta.” To a wannan ka shi masu yin kariku sun shiga ciki da suke cewa an baiwa mutum al-jannah, ko in ya ga wane an gafarta masa alhali kuwa addini ba’a yinsa da maganar wani sai dai abin da Allah ya saukar a lokacin da Annabi yake raye shi kuma ya sanar wa sahabbai, su kuma sahabbai suka sanar ta hanyar dangataka mai kyau har zuwa garemu.
(v)                 Al-Isti’ana bil Adawiya (wato magance wata cuta ta hanyar shan wani magani). Wannan ma wani irin sihiri ne na karbar wasu magunguna ana sakawa a cikin abinci ko wasu abubuwa na shad a sunan cewa zai hana wuta ta kone ka ko maciji ba zai sare ka ba, ko wuka ba za ta kama ka ba ko bindiga da makamantansu, cewa yana da wannan sihiri wanda zai bayar, irin wadannan mutane suna nan kuma wasu sun yarda da su.
(vi)               Ta Allukul Kalb (wato camfi). Irin wannan sihiri shi ne a rataya zuciyar mutum akan wata addu’a ace ta musamman cewa wani malami yasan ismillahi al’a’azamu, wato sunan Allah daya fi kowane girma wanda idan an roki Allah dashi kamar yankan wuka ne da cewa aljanu har ma suna yi musu da’a, idan sun sami wasu dolaye masu karmar kwakwalwa sai su rika dauka da gasket ne har zuciyarsu ta kama gamagam suna tsoronsu. Daga nan sai shi wannan mai sihiri ya mallake su har su rika ganin duk bain day a musu zai same su. Wanda in ya ga sun yarda da shi har suna jin tsoronsa sai ya rika cewa zai musu hanyar da zasu samu arziki ko wani matsayi da za su dawwama akai. To amma mai hangen besa ub ab gata masa ba zai amince da wannan ba, don haka shi kam ba za su iya cutarsa ba. Wannan shi irin damfara na zamanin nan irin su “Cash splash” na cewa a bad a kamar dubu goma bayan wata daya su koma dubu ahsirin ko fiye da haka, daga baya idan suka ga an gane su, su gudu bat re da an samu biyan bukatar ba. To shima yana cikin sabon sihiri da bai kamata Musulmi ya yarda da shi ba.
(vii)             Namima (wato yawo da gulma) wannan wani irin nau’in sihiri ne na masu yawo suna gulmace – gulmace ta hanyar annamimanci, don hada fada tsakanin mata da mijinta ko tsakanin aboki da aboki. An samu daga tafsir na iman ibnu Khasir cewa “ASnnamimanci” ya kasu kashi biyu kamar haka Akwai masu daukar maganar wani su kai wa wani ta hanyar gulma don su hada su husuma, to wannan haramun ne kuma bai halatta ga Musulmi ya aikata haka ba. Don Annabi yace “wani nau’in gulmace gulmace sihiri ne. (wato maganganu da za’a hada husuma tsakanin aboki da aboki duk sihri ne, kuma wanda ya yi sihiri ya bata).
Amma kashi na biyu shine wanda za’a yi a gyara tsakanin mutane don a daitaita tsakaninsu to, wannan ba shi da laifi. Saboda Annabi yace “wanda ya yi wata gulma domin ya sasanta tsakanin wani don a ci nasara da suka bata to, wannan ba laifi bane”, kuma Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce, “yaki dan dabara ne”.
Duk wandanan abubuwa da ake ambata sihiri ne sabdoa akwai wawantar da hankulan mutane; da masu wala-wala da dabara a ciki. Kuma mugayen muluma sun shiga cikin irin wadannan ayyuka suna yaudarar mutane suna cutar su bisa karya da sunan addini. Da haka suka batar da mutane suka sa asara ninki biyu ta imani da kuma dukiyarsu. Allah ya tsare mud a bin mungayen malami, ya datar dam u da bin littafin Allah da sunnar Annabinsa mai tsira da amincin Allah.
RADDI AKAN ABUBUWA MASU RIKITARWA
       Inda wani ya yi tambaya cewa shin abubuwan da Shehu Tijjani ya fada gaskiya ne, na cewa shi abin da Annabi ya bayar bayan mutuwarsa daidai yake da abin day a bayar loakcin da yake da rai daidai ne? sai Shehu Tijjani ya ce ‘e’ daidai ne, sai dai wanda ake baiwa kowa da kowa wannan ya yanke daga rasuwar Annabi mai tsira da aminci, ammamwanda ake baiwa wasu mutane na musuamman shi yana nan baya yankewa, don haka ma yace, “Salatul-Fatihi ilma Ugulika tafi dukkan ayyukan alheri da ibada lada, don haka ma ita salatul Fatihi ta fi kowan ne irin aikin ibada lada.
       Sheikh Abubakar Gumi ya bada amsa da cewa. “Tun da ita Salatil Fatihi ta zama al’amari ne na wasu mutane na musamman to, mai yasa ta zama yanzu ta kowa da kowa kuma ana gaya musu falarta? To wannan a hankalce ma ya nuna cewa bidi’a ce. Annabi mai tsira da aminci yace “wanda ya farar da wani aiki a cikin al’amarin mu na addini, abin da baya cikin sa, to za’a mayar masa ba’a karba ba.” Kuma Annabi mai tsira da aminci yace, “Na hane ku da bin fararrun abubuwa domin duk abin da aka fare shi to, bidi’ah ce, kuma dukkan bidi’ah bat ace.” To mai yasa Annabi mai tsira da amincin Allah bai ce sai sakon da yazo daga wasu mutane na musamman ba, don ya bambance lokacin rayuwarsa da bayan mutuwar sa? In ba’a bada wata amsa akan wannan ba, to duk abin da yazo bayan Annabi mai tsira da aminci bdidi’a ne. sai mutum ya yi kiyasi da wannan Magana ta Annabi.
       Khalifofi da Annabi ya yi umarni a bi su kuma ayi riko da hanyar su gam-gam, malamai gaba daya, magabata da mamaya sun ce su hudu ne wato: Abubakar, Umar, Usman, Aliyu yardar Allah ta tabbata a gare su. Duk kuma wanda ya sabawa abin da la’umma gaba daya take akai to ya halaka. Saboda fadin Allah madaukakin Sarki daya ce, “Duk wand aya bi wata hanya bata manzo ba bayan gaskiya ta bayyana a fili, kuma ya bi abin dab a hanya ce ta muminai ba to, za mu jingine shi ga abin day a jibinta, kuma za mu kona shi da wutar jahannama. (Nisa’I 115)
       Wannan bayani yana nuna cewa, duk wanda ya saba maganar Allah da ta manzonsa to ya halaka. 
DAGA LITTAFIN; AL-AKIDATUSSAHIHATA BI MUWAFAKATUS, NA MARIGAYI SHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI {R}

HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’A {1}


DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Tsira da amincin Allah su tabbaat ga fiyayyen manzanni, shugabammu, Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, da abokan sad a mutanen gidansa baki daya. Yardarm Allah Madaukaki ta kara tabbata abisa shugabanni mabiyansa, da kuma malamai masu aiki da saninsu, da shugabannin mazhabobi hudu – Imam Abu Hanifa, Imam Maliki, Imam Shafi’I da Iamam Ahmad ibn Hambali – da masu koyi da su har zuwa ranar tashin Al-Kiyama.
       Bayan haka, wannan itace hanya ingantacciya ga wanda yake bukatar nasiha cikin ‘yan uwa da masoya. Kuma hanya ingantacciya bat a tabbata sai ta yi daidai da shari’a. wannan ne yasa na sakawa wannan littafi suna “HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’A”. Na rubuta shine don ni kai na da sauran ‘yan uwa Musulmi, saboda bin ingantacciyar hanya, da neman Allah ya amfane ni dasu.
       Ban yi nufin rubuta wannan littafi don tada wata fitina ga al’ummar Musulmi ba sai dai don dogaro da fadar Allah Mabuwayi cikin littafinsa mai girma. Al’kur’ani, inda yake cewa “wadan da suke boye wani abu daga abin da muka saukar na daga hujjoji da bayanai na shiriya, bayan mun bayyana shi ga mutane a cikin littafi, to sune wadanda Allah ya tsine musu kuma duk wani mai tsinuwa ya tsine musu, sai dai wadanda suka tuba, kuma suka gyara kurakuransu, sannan suka ci gaba da bayyanawa mutane gaskiya, to su kam zan karbi tubansu, domin ni mai karbar tuba ne mai tausayi; (Bakara 159 – 160) Kuma ya zo daga cikin hadisi na Abu Hurairah cewa, “Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yace wanda aka tambaye shi wani ilimi, sai ya boye to za’a masa linzami na wuta ranar tashin al-kiyama. Tirmizi da Abu Dauda sun inganta shi. Wata ruwaya daga Ibn Majah tace, “Ba wani mutum da zai haddace wani ilimi kuma yaki karantar da shi, sai an zo da shi a daure da linzami na wuta a ranar tashin kyama.
       Kuma, ina neman dacewa daga wajen Ubangiji Madaukakin Sarki. Haka kuma, malam yaci daga da cewa, “ku sani” sanin addini yana dogara ne kan sanin kalmar shahada wato “La’ilaha Illahllahu Muhammadurrasulullah,” ma’ana ba wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne, dan aikensa ne. ya ci gaba da cewa, ma’anar kalmar shahada shi ne, ba wani abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ma’ana Annabi Muhammadu kuma manzon Allah ne, shi ne, wanda aka aiko don muyi koyi da shi cikin bauta. Ita kuma bautar bat a yiyuwa da son ran wani bawa sai yadda Allah yake so don haka ne ma ya aiko manzo ya karantar da yadda za mu bauta masa. Saboda haka duk wanda yake so ya bi karantarwar Manzonsa, tsira da amincin su kara tabbata a gare shi. Kuma duk wanda ya bauta wa Allah bad a abin da Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi ya zo da shi ba, to a gaskiya bai bauta wa Allah da gaskiya ba. Saboda fardar Allah mai girma, “wanda bai riki Musulunci addini ba to ba za’a karbi ibadarsa ba.” (Ali Imra’na 85). Kuma Musulunci baya zama musulunci na gaskiya sai wanda Annabi mai tsira da aminci ya tababtar a lokacin rayuwarsa saboda fadar Allah mai girma. “Yak u wadanda kuka yi imani, ka da ku tambayai wadansu abubuwa don in kuka tambaya za’a bayyana muku, kuma in aka bayyana muku za su munana muku zuciya. In kuma kuka dage sai kun tambaya a lokacin da Al-kur’ani yake sauka to, za’a bayyana muku hukuncin abin, kuma duk abin da Allah bai bayyana muku ba, to, ya muku sauki ne, don Allah mai gafara ne mai tausayi.” (Ma’idah 101)
       Kuma Annabi mai tsira da aminci ya ce, “Rayuwata alkhairi ce a gare ku, kuma mutuwa ta ma alkhairi ce a gare ku. (abin nufi a nan shine: rayuwarsa alkhairi ce saboda shiryarwa da alhhairi da ake samu a wajensa, haka ma mutuwarsa alkhairi ce, saboda hukunce hukunce ya tsaya kenan a kammu). Allah shi ne masani a kan haka. To, wannan ya nuna cewa ba wani abin da zai zo bayan mutuwarsa, in kuma wani y ace ga wani abin ya zo to, ya yi shishshigi kenan wa addini. Don ba wani abu da zai sake zuwa na sako, don kuwa Allah ya nuna cewa shi ne karshen manzo da zai zo ba wani kenan. Saboda Allah ya ce, “Annabi ba mahaifin daya cikamakin Annabawa. Allah ya kasance masanine akan komai”. (Ahzah 40)
       Kuma Annabi mai tsira da aminci yace: “Misali na da Annabawa da wandanda suka gabace ni, kamar misalign Katanga ce da aka gama ginata tayi kyau ta ba da kayatarwa sai tubali daya ya rage a ciki katangar inda kowa ya zo ya ga ni sai yace, ina ma wannan tubalin a ciki shi don ta cika kawata? Sai Annabi yace to. Ni ne wanda aka cike wannan guri na tubalin daya  rage, sai ya ambata cewa nine wannan tubalin, da ni aka cika wannan ba wani Annabi bayana. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
       Annabi mai tsira da aminci yace, “Ni ne mai share duhu, kumani ne Allah yake share kafirci, kuma nine wanda za’a tara mutane a gabana, ni ne kuma karshen Annabawa wanda ba wani Annabi a bayana. (Bukhari da Muslim). Annabi mai tsira da aminci yace, “A cikin jama’ata za’a sami makaryata guda 30, kowanne yana cewa shi Annabine to, kada ku yarda da su. Karya su ke yi. Ba wani Annabi bayana.” (Abu Dauda da Ahmad da wassunsu).
       Kuma an sami Hadisi daga Imam Muslim cewa Annabi mai tsira da aminci yace, “An fifita ni akan Annabawa da abubuwa shida:
(i)                  An bani matattarar Magana.
(ii)                An bani ikon duk inda zanje yaki sai an jarrabe su da tsoro.
(iii)              An halatta mini cin ganima
(iv)               An sanya mini kasa ta zama masallaci kuma guri mai tsarki
(v)                 Kuma an aiko nig a dukkan talikai baki daya (Iman Tirmizi). Kuma yace Hadisi ingantacce ne.
(vi)               Nine kuma cikamakin Annabawa, ba wani Annabi bayanni.

MA’ANAR ANNABCI, DA MANZANCI DA WALITTAKA.
       Mafiyawan abin day a batar da mutane shine rashin sanin wanene Annabi, wanene manzo kuma wanene waliyyi?
       Bambamcin wadannan kalmomin da aikinsu sune kamar haka: -
       Malamai da yawa sun fadi maganganu da yawa akan wanene Annabi kuma wanene Manzo. Ga ra’ayoyinsu kamar haka: - Mafi kyawun fassara shine: wanda Allah ya aiko masa da wahayi daga sama cewa yayi wani aiki kuma yayi umarni da ayi to, shine manzo. Kuma wanda aka masa umarnin yayi aiki shi kadai to, shine Annabi. Kuma kowane manzo Annabine, amma ba kowane Annabi bane yake zama manzo. Shi manzo sakonsa na dukkan al’ummarsa ne to, amma Annabi kuwa sakonsa ya kebanta ne gareshi kawai.
       Kuma ita annabtaka yanki ne na sako, kuma sako ta dauki annabataka. Saboda haka annabtaka babban abu ne, amma manzanci kuwa na gaba daya ne. kuma Annabawa suna da yawa, amma na karshensu shi ne Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah, shine cikamakinsu, kuma limaminsu na tsoron Allah kuma shugaban manzanni. Haka kuma duk wanda yace an ba shi wani sako daga Allah bayan Annabi Muhammadu mai tsira da aminci to, bata ne kuma son zuciya ne, bai halatta a bi shi ba, wanda kuma ya bi shi ya bata. Allah yayi mana tsari da su.
       Amma ita walitttaka, misalince ta imani, saboda haka duk wani mai imani kuma yana tsantsar tsoron Allah a sarari da boye kuma shine masoyin Allah mai girma, kuma asalin walittaka asalinta daya ne, sai dai akan sami cikkake da kuma mai rauni. Kuma walittaka cikakkiya tana kasancewa ga muminai masu tsoron Allah na gaskiya, wato tsantsa, kamar yadda kuma walittaka dacewa ce da abin da Allah yace, “ku saurara lailai akwai waliyai, kuma waliyan Allah ba wani tsoro agaresu, kuma ba za su yi wani bakin ciki ba, sun e masu imani da matukar tsoron Allah, kuma ana musu albishir a rayuwarsu ta duniya da makoma lahira.” (Yunus 62-63- da 64).
       Don haka walittaka tana nan ga masu tsoron Allah sune aka yi musu alkawari da wadannan ayoyi uku, kuma walittaka dacewa ce da abin da Allah yake so ga masu bin umarninsa. Saboda haka ba yawan sallah da azumi n eke sa walittaka ba, (abin da Allah yake nufi da musu bishara duniya da lahira shine bushara ta lahira itace Aljanna kuma bushara a duniya shine yin mafarki mai kyau ko wani ya gane masa abu mai kyau). Kuma daga Abuzarri, Allah yarda da shi yace, “Ya Manzon Allah, mutum yana aiki mai kyau har mutane suna yabonsa kuma suna gode masa to menene matsayin sa? Annabi mai tsira da amincin Allah yace: “wannan busharace ta duniya don nuna mutumin nan na kirki ne. (Imam Muslim).
       A wata ruwaya kuma Annabi mai tsira da aminci yace, mala’iku zasu zo suna masa bushara da kada yayi bakin cikin don shi dan aljannane. Haka kuma an rawaito cewa mala’iku zasu sauko ranar mutuwar mutumin kirki suna masa bushara. Saboda fardar Allah Madaukakin Sarki, “wadan da suka ce Allah shine ubangijimmu kuma suka daidaitu akan imani, mala’iku suna sauka alokacin daukan rayukansu sun ace musu kar kuji tsoro, kuma kada kuyi bakin ciki, muna muku albishir da aljannar da aka muku alkawari, mune majibinta al’amuranku a duniya da kuma lahira, duk abin da kuke so zaku same shi an tanadar muku na abubuwan da zukatan ku suke so, wannan masauki ne daga Allah mai yawan gafara da tausayi.” (Husiat 30-23)
       A wata bushara kuma da Allah yace, “ita ce girgiza mai girma ba zata firgitasu ba, kuma mala’iku suna gaya musu wannan ranace ta ku da aka muku alkawari da shiga al-jannah.” (Anbiya’I 103).
       Allah mai girma da daukaka yace, “ranar tashin kiyama, ran ace da za’a ga munini da mumina haske yana tafiya a gaban su da bayansu, dama da hagu, ana musu albishir su a wannan rana makoma itace aljannaha wadda koramai ke gudana acikinta, zasu tabbata cikin ta har abada, wannan babban rabo ne a gareku.” (Hadi 12) (Tafsir na ibn Khasir na ayoyi guda uku da aka ambata).
       Saboda da haka, idan an gane wadannan ayoyi to waliyi shine mai tsoron Allah, bambancin anan shine, wanda yafi karfin imani. Don kuwa karuwar imani da raguwarsa shine karuwar aiki da tsoron Allah, haka kuma yana raguwa ne da raguwar tsoron Allah. Allah yace, “Ubangiji shine waliyin wadanda suka yi imani yana fitar dasu daga duhu zuwa haske, amma kafirai waliyansu sune shedanun malamai suna fitar dasu daga haske zuwa duhu. (Bakara aya 257).
       Kuma Allah Madaukakin Sarki yana cewa, “mumina mace da mumini namiji sashe da sashe waliyan juna ne. “(Taubah 71).
       Shaikha ya yi Karin bayani cewa, “Allah kuma shine waliyinsu kuma majibincin al’amuransu. Kuma Allah zai jibinci bayin sa muminai don yana sonsu su kuwa suna yarda da shi, don haka ne duk wanda ya yi gaba da waliyin Allah to, ya fito yin yaki ne da shi gaba da gaba, kuma wannan walittaka bada wani ne yake ba a a, rahama ce ta ubangiji da kyautatawarsa ga wanda yake so, ba wani walittaka ce ta wani ba, tsakanin mutum da mutum ba saboda wata bukata da yake so. Saboda fadar sa a cikin Al-Kur’ani mai girma, “Kace godiya ta tabbata ga Allah wanda bai riki da ba; kuma ba shi da abokin tarayya a mulkinsa; kuma ba shi da wani waliyi saboda kaskancinsa; saboda haka ku girmama Allah iyakar girmamawa.” (Isra’I 111). Saboda haka, Allah ba shi da wani waliyi don gazawarsa, saboda gaba daya buwaya ta Allah ce, sabani da sarakuna masu rike wadansu don suyi karfi dasu, saboda kaskancinsu da bukatar suna taimako ga wanda zai aimakesu. Allah kuma ba haka yake ba.

BAYANI AKAN IMANI
       Imani shi ne gaskatawa a zuciya da kuma tabbatarwa a aiki, cewa duk abin da yazo daga Annabi mahammadu mai tsira da aminci, gaskiyane. Kuma shi imani abu daya ne, kuma daidai wa daidai da suke, fifiko kawai yana karuwa ne da tsoron Allah, da kuma sabawa son zuciya, da kuma abin da yake mafififci wajen bin Allah. Saboda haka su muminai, wajen fifikonsu kamar gain ne, don kuwa wani ganinsa mai karfi ne, kuma wani ganinsa mai rauni ne kamar mai sa tabarau ga mai raunin gain da wanda baya sawa wajen ganin to, haka imani yake. Haka kuma daidaituwa wajen imani, wasu daga mutane imaninsu wajen kalmar Lailaha illallahu kamar rana yake, kuma wasu kamar watane da kuma taurari wajen haske na imani. Amma kuma wasu kamar fitila yake, mai haske da marar haske, wajen imanin su. Don haka a ranar tashin Kiyama haka za’a ga wasu hasken sun a imani ya fina wasu. Duk lokacin da wannan haske yayi rauni sai a ga sha’awa sha’awe ya say a yi rauni, to, amma ga wasu sai yayi ta karuwa. Saboda haka duk lokacin da imani ya yi haske sai kaga hasken ya koma wasu sha’awe sha’awe har imani ya yi ta karuwa kamar wutar daji da ta sami dama. To wannan shine wanda gaskiyar tauhidinsa ya tabbata. Wanda ya gane wannan zai fahimci fadin Annabi mai tsira da yardarm Allah day ace, “La’ilaha-ilallahu” da neman yardarm Allah ga fadin haka.” (Bukhari da Muslim)
       Haka kuma duk wanda yace “La’ilaha-illallahu” to ya haramta ga shiga wuta.” (Buhkari da Muslim). Don haka ayyuka bas u fifita da kamanninta ko yawanta, sai dai tana fifita ne da niyar da aka aikata aikin a cikin zuciya. Haka kuma hankali, shi ma yana karbar fifiko a bisa aikin Allah, don haka za’a ga kowa yana da hankali, wani yafi wani yafi wani. Haka kuma wajen wajibi da harmaci, dukkansu wani fi wani wajen aikin. Amma shi karuwar imani ta fuskar karuwa wanda ya zauna da Annabi lokacin da yake raye, to akwai bambanci da wanda labari ya zaike masa daga baya, kamar najjashi da kamarsu domin shi karuwar imani yana karuwane wajen zuciya da aiki da gabbai kamar malamin da yake aiki da saninsa da malamin da yake ya sani amma baya aiki da saninsa. Don haka rashin aikin malami da saninsa, yana nuna raunin iamaninsa.
       Saboda fadin Annabi mai tsira da aminci cewa, “wanda aka ba shi labari bai zai zama dai-dai da wanda ya gain ba haka a wani fadi yace, “labari baya zama dai-dai da wanda ya gain.” (Iman Ahmad ya rawaito).
       Kuma ga wani labarin day a karfafa mana cewa Annabi Musa day a sami labarin cewa mutanensa sun koma ga bautar dan maraki, bai zubar da allunan Attaura ba, said a ya zo ya gansu da idonsa sannan ya zubar da allunan saboda gigicewa. To anan ai ba yana nuna cewa Annabi Ibrahim mai tsira da aminci yace, “Allah ka nuna mini yadda kake tada matattu,” Allah yace masa, “ya Ibrahim ba ka yadda bane?” Sai Annabi Ibrahim yace, “na yarda sai dai ina neman zuciyata ta natsu ne.” (Bakara 260). Haka kuma wanda Hajji ta wajaba a gareshi to, wajibi ya san yadda ake yin aikin hajji don in an sami ikon zuwa ayi aikin daidai, saboda ita Hajji wajibi ne akan kowane Musulmi sai dai tana wajaba ne akan wanda yake da halin zuwa, da halin yin Zakka ga wanda ya sami ikon bayarwa, to, amma wajibi ne mu yi imani da Hajji da Zakka ko da ba mu da halinsu. Haka kuma wanda ya zo zai Muslunta to, sai a ‘LAKKABA’ masa Kalmar “La’ilaha illallah” to, amma ba za ka ce sai ya yi ayyukan ibada dai-dai ba sai daga baya in an koya masa yadda zai yi. Kuma duk lokacin da wata matsala ta taso na addini sai a sanar da shi har ya zama yasan hukunce hukuncen addinin. Saboda haka ba yadda za’a yi mutane su daidaita cikin imaninsu. Kuma lallai duk wanda ya tashi cikin ayyuka na kwarai to zai kara imaninsa.
       Saboda haka a kullum ana so mutum ya yi kokarin ayyuka da za su kara masa imaninsa don ayyuka sun a kara wa imani karuwa kuma rashin yin sa yana rage imanin mutum. Don haka Manzon rahama mai tsira da amincin Allah yace, “mazinaci baya zina yayin da yake da imani,” (Bukhari da Muslim). Abin nufi anan shi ne lokacin da mutum yake yin zina to ba shi da imani sai in y agama imaninsa ya komo masa, sai ya yi nadama in yana da rabo ya tuba ga sake aikatawa. Domin su masu tsoron Allah in shaidan ya shafe su da yin wani mummunan aiki sai su tuno da ubangiji, sai ga shi suna gane shaidan ne ya shafe shi daga nan sai su tuno da Allah, suna masu barin wannan aikin.” (Araf 30)
       Haka kuma daga Imam Laisi ya ji daga Muyahid ya fassara wannan aya da cewa, lokacin da zai yi niyar aikata wani laifi sai ya tuno da laifi ne sai ya bari tun kafin ma ya aikata. Sai Shaikh yace, “dukkan laifuka in mutum ya yi sha’awar yi sai ya tuno kuma ya bari, don sha’awa da fushi sune mafarin laifi, a lokacin da mutum ya gano haka sai ya gaiya janye ta. Kuma Allah y ace, “shaidan na karfafa batattu cikin bata bas a ragewa. (A’ararf aya ta 202).
       Abin nufi anan shi ne shaidanu suna taimakon mutum cikin bata da laifi, kuma ibn Abbas ya ce, “shi mutum baya jinkirin aikata laifi kuma shaidanu bas a ragar masa, in har bai gane ba sai idanunsa su makance cikin aikata laifin, sai ya halaka. Kuma shaidan sai ya kara tunzura shi cikin aikatawa. Ko da yake shi mutum ya san cewa abin da zai aikata ba mai kyau bane, don kuwa ya san abin ba mai kyau bane, wannan ya nuna cewa haka darfin imani yake ga mutum kamar mutum ya rufe idonsa amma ya san shi ba makaho ba ne, to, haka zuciya take runtsawa wajen aikata laifi kamar makantar kafiri.
       Wannan bayani ansamo shi daga wajen fadar Annabi mai tsira da aminci cewa, “idan bawa zai yi zina sai a zare masa imaninsa, kuma idan ya tuba sai a dawo masa da imaninsa (Abu Dawuda)
       Malam ya ce wannan shine maganar masu hikima cewa, ba’a kafirta Musulmi don ya aikata wani laifi na zunubi kamar zina ko shan giya ko caca sai in ya halatta cewa abin halal ne, to, ya zama kafiri, amma ban da shirka. Saboda fadin “Allah baya gafarta wa wanda ya masa kishiya cikin aiknsa, amma yana gafarda wa wanin wannan ga wanda yaso.

YADDA AKE SAMUN DARAJOJI
       Game da darajoji ya dauko mataki-mataki ne, da farko duk wanda ya yi furuci da Kalmar Shahada to, Musulmi ne, kuma za’a yi mu’amala da shi na abubuwan da suka shafi musulnci tsakaninsa da ‘yan uwansa musulmi. Kuma wand aya yi imani da abubuwan da Annabi tsira da aminci ya zo da shi to, wannan muminine a sarari, don kuwa ana aiki ne da abin da ya kasance a fili, saboda Allah shine masanin abin day a ke boye. Amma su muminai darajarsu ba daya bace, don kuwa wani ya fi wani a gwargwadon ayyukansa da kuma gaskatawarsa da kuma ayyukansa na tsoron Allah, don haka mumini day a fi karfin zuciyarsa da sha’awar kawace – kawace na kare kansa daga dukkan wani laifi da kuma hadiya fushinsa to, wannan shine waliyi a cikin muminai, saboda fadar Allah mai Girma da Daukaka na cewa, “Su waliyan Allah ba tsoro a garesu kumna ba za su yi bakin ciki ba, su ne wadanda suka yi imani da kuma tsananin tsoron Allah, kuma basa saba masa a cikin dukkan ayyukan su.” (Yunus, aya ta 63
DAGA LITTAFIN; AL-AKIDATUSSAHIHATA BI MUWAFAKATUS, NA MARIGAYI SHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI {R}