GURARE UKU DA YA HALATTA A ‘DAGA SAUTI WAJEN AMBATON ALLAH MAI GIRMA
Ya zo a cikin Mukhtasarul Khalil, babin jihadi cewa daga sauti wato Allahu Akbar, Allahu Akbar:
1. A wajen yaki. Ya halatta a daga sauti ga mayaki a lokacin day a dau kayan yaki, a lokacin da yake fagen yaki wannan shine alamominsu dare da rana wato fadar a lokacin fuskantar abokan gaba, kuma ana so su yawaita kabarbari.
2. kuma a waje na biyu da za’a daukaka kabbara shi ne lokacin da za’a fita sallolin idi karama da babba tun daga gida har zuwa isa filin Idi da kuma dawowa gida.
3. Waje na uku kuma shi ne, wajen aiki Hajji, tun daga mikati har zuwa karshen aiki, da kuma fadar Labbaika har zuwa karshe.
To, in banda wadannan wurare guda uku, ambatar Allah a boye shi ya fi, saboda fadar Annabi mai tsira da amincin Allah lokacin day a ga wadansu jama’a suna daga muryar su da zikiri sai yace, “wanda kuke kiran nan yana kusa da ku.” Daga Sahihul Muslim, daga Abi Musa, “cewa muna tare da Annabi mai tsira da amincin Allah, sai wasu mutane suna daga sauti a sarari suna cewa Allah! Allah! Da karfi, sai yace musu, “yak u mutane, ku hutar da kawu nan ku, wanda kuke kira ba kurma bane ba bebe bane kuma ba wanda baya nan ban e, don wanda kuke kira mai ji ne kuma yana tare da ku.
Bai halatta bag a kowane mutum ya ke tare haddodin da shari’a ta a jiye cikin maganarsa da aikin sa. An sami hadisi daga Sahihul Muslim a Kitabul Ilmi daga Ahnaf dan Kais daga Abdullahi, yace Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace “masu shis-shigi sun halaka. Annabi ya fadi haka har sau uku, cewa masu shis-shigi sune masu kutsawa su wuce iyakar da shari’a ta ajiye, kuma sune masu guluyi masu wuce iyaka a magangannun su da aikace-aikacensu.
GURAREN AMBTAON ALLAH DA YA KAMATA MUTUM YA RIKA ZAMA IN BA’A BIDI’A A WAJEN
Cewa Abu Hurairah ya rawaito hadisi daga Annabi mia tsira da aminci, cewa “Allah mai girma da daukaka yana da mala’ikunsa matafiya wuri-wuri da ake ayyuka na alheri kamar karatun Al’Kur’ani. Idan suka ga wani waje ana karatun AL’Kur’ani sai su kewaye wajen sashensu da sashensu har ya kai sararin sama, idan an gama karatu an waste, sai su koma wajen ubangiji, sai ya tambaye su alhali ya fi sani daga ina suke, sai yace musu daga ina kuke? Sai su ce “Mun taho ne daga wurin bayinka a bayan kasa suna maka tasbihi suna ambatonka, suna gode maka, kuma suna ambatonka, kuma suna rokoka, sai Allah yace “Me suka roke ni?sai su ce sun roke ka aljanna, sai yace, sun gantane? Sai su ce a’a’ basu ganta ba. To, yaya da sun ga aljannar tawa fa? Sai mala’iku suce, “da sun ganta dab a abinda za su roka sai ita. Suna kuma rokon ka neman tsarinka. Sai yace, “me suke namen tsari daga gare ni? Sai su ce suna neman tsari ne daga wutarka. Sai Allah yace “shin sun ga wutar tawa? Sia su ce? A’a, basu ganta ba. Sai Allah yace “shin da sun ganta fa? Sai mala’iku su ce, “da sun ganta ba wani abu da za su roka sai gafararka. Sai Allah yace, “To, na gafarta musu, kuma na tsare su da abin da suka nemi tsari.” Akwai wani, bawa mai laifi ya zo wucewa, sai ya zauna a cikin su, shi ma gafarar hard a shi? Sai Allah yace, “i, shi ma na gafarta masa, saboda su mutanen alkhairi ne, mai zama da su baya wulakanta.” (Muslim ne ya ruwaito).
Ya zo a cikin Ihya’ussunna wa Ihmadil Bidi’a na Shaikh Usmanu dan Fodiyo, abin day a zo daga sahabban Annabi mai tsira da aminci ko tabi’ina ko tabi’ittabi’ina, to ya wajaba ayi riko da shi ayi aiki saboda kaiwan su kololuwa bisa bin Sunnah da nisantar bidi’a.
Shaikha Abubakar Gumi yace, “In an tambaye ka abinda yake da dalili a shari’a, amma ba’a sami wani yayi aiki da shi ba daga cikin magabanta, shin wannan sunnah ne ko bidi’a? sai Ahmad Zaruk yace “wannan yazo a cikin wani littafi mai suna Umda’itul Muridul Sadiqu, Imam Malik ya fada cewa wannan abin bidi’a ne. don su magabata basu bar aiki da shi ba, sai don wani dalili da su kedashi a wajensu, don su sun fi kowa kwadayin alkhairi, kuma sun fi kowa sanin sunnar Annabi mai tsira da amicin Allah. To, wannan ya yi daidai da fadin dan Mas’udu ya yin da yaga wadansu mutane sun taru suna zikiri, sai yace “wallahi, hakika kunzo da bidi’a, abisa zalunci, yanzu ku kunfi sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah ilimi ne? ibnul Hajji ya ambaci wannan cikin littafinsa (Madakhal). Don Karin bayani, a duba littafi mai suna Madakhal.
Haka kuma, Imam Shafi’I yace, “Dukan abin da aka same shi yana da sanadi to, ba bidi’ah bane, ko da magabata basu yi aiki da wannan ba, sabo da kila suna da wani uzuri day a hana su aiki da shi a wannan lokaci. Ko kuma suna da wani dogaro da yafi wancan lokaci a wajensu, ko kuwa sub a su sami wannan hadishin ba, don kuwa da sun samu, da sunyi aiki da shi, shi kuma hukunce – hukunce ana samunsa ne daga shari’a kuma ga shi shari’a ta tabbatar da shi.
To akan wannane suka saba cikin fahintarsu wajen kamar a taru don a sauke Al’Kur’ani, ko kuma irin zikirin nan da ake haduwa ana rangaji da daga murya, ko umarni wajen yin addu’a na cewa a karanta Fatiha da Kulhuwa sau uku – uku da sauransu.
Saboda an sami hadisai da suke nuni da yin addu’o’I to amma ba’a sami cewa a yi a cikin umarni na jam’iba, kamar inda Annabi yace ku roka wa dan’uwanku gafara yayin daya mutu aka je bisonsa amma bai jagorance sub a a yin addu’ar, sai ya bar kowa ya yi addu’a gwargwadon inda zai iya a makabartar.
Kuma Imam Shafi’I ya yi bayani cewa “In dai an sami hadisi cewa Annabi yace a yi to, ko yaya aka yi abin a wajensa an yi daidai.
Shi kuma Imam Malik cewa yayi, “duk wani hadisi da aka bada umarni in har ba’a yi masa kaifiya ba sai wasu suka ba shi kaifiya to, sun yi bidi’ah. Don kuwa akwai shubuha a ciki.
Kuma an samu daga Annabi mai tsira da amincin Allah yace, “kada wani ya yi sallar La’asar sai a Bani Kuraiza, sai La’asar ta yi musu a kan hanya basu isa Kuraiza ba, saboda haka sai wasu daga cikin sahabbai suka yi sallah don fahintarsu da cewa Annabi yana nufin da su yi gaggawa ne, to sai gashi basu yi gaggawa ba har lokaci ya yi, sai suka yi sallah, to, amma wasu basu yi ba, said a suka isa Bani-Kuraiza sannan suka yi sallarsu, don su a fahintarsu Annabi yayi musu umarni ne cewa kada su yi sallah sai a can.
Don haka, da suka dawo sai suka baiwa Annabi labari cewa wasu sunyi sallah kafin su isa saboda ganin lokaci ya kure amma wasu ba suyi ba saboda bin umarni cewa sai sun kai kamar yadda kace. Sai Annabi yace “Shi kenan kowa sallarsa ta yi daidai. Wannan ya na nuna wa kenan cew ain an sami sabanin fahinta akan abu to, ba’a zarginsa indai an sami asalinsa daga sunnah kamar yadda hadisin ya nuna.
Sai Shaikh Abubakar Gumi yace “yana daga cikin bidi’ah mummuna a yi aiki da nassi ko da an sami nassinsa daga sunna in dai an karkatar da shi bisa son zuciya, kamar yadda wadnsu suka dauka cewa a buga dundufa (ganga) don sanar da aure, sai suka ce ya halatta a yi kade-kade a lokaci shagalin aure, kamar masu buga mandiri a loakcin da suke wani biki saboda fadar cewa za’a buga tambari ko dundufa don sanar da shagalin aure. Malam ya ci gaba da cewa masu wannan fahinta sun yi kuskure, don buga tambari ko dundufa ana yinsa ne a lokacin sanar da aure, saboda haka karkatar da mandiri a kan irin wannan akwai wargi a ciki don ba shi ne wasan da aka bada umarni ba. Kuma mulamai basu yi wani sabani a kai ba. Saboda haka ba addini bane. Saboda haka buga tambari ko dundufa yana da asali, amma mandiri ba shi da wani asali a shari’a don haka ya zama wasa, wato wargi kenan a cikin addini, abin daya zamo wargi, Usman Dan Fodio yace “ai kuwa wargi a cikin addini bidi’ahne.
Kuma Shehu Usman dan Fodiyo ya fada a cikin littafinsa mai suna Ihya’ussunnah wa Ikhmadul Bid’ah “wace kade kade da raye – raye bidi’ah ce harantacciya. A lokacin da yake ambataon bidi’o’I haramtattu yace” yana daga cikin bidi’o’I haramtattu, akan irin abin da mutane suka haddasa akan babul-ihsan (wato raye-raye da) wake-wake da kade-kade da shirya kasidodi, wai kyuaktatawa ne a wajen sufaye. Sai shehu Usman Dan Fodiyo yace “a wajen janhuran malami wannan bidi’ah ce harambatacciya a shari’ah.
Wani Malami mai sun Izzudin acikin littafin sa, Kawaidul Ahkami, y ace malaman sufaye suna da matsayi wajen sauraron:
(1) Akwai wandan da ilimi yak an zo musu da natsuwa da halaye masu kyau a lokacin da suke sauraron Al-Kur’ani to wadannan sune mafifitan masu sauraro.
(2) Masu martaba ta biyu, sune wadanda suke samun abubuwa na nutsuwa ta hanyar sauraron wa’azi da tunatarwa sai suji sun nutsu kuma su ji da di.
(3) Martaba ta uku kuma akwai malaman sufaye da suke samun nutsuwa ta hanayr zikiri da wake-wake da karanta kasidodi wai akwai jin dadi da hutawa ta haka.
(4) Masu martaba hudu kuwa cewa suke yi wai “dadi na zuwa musu ta hanyar sauraron kade-kade da wake-wake ta hanyar buga ganga kamar mandiri da sauransu. Sai dai malam yace duk wanda ya tabbatar haranmunne, amma dai yafi samun nutsuwa in yana sauraron haka, to wannan ya zama mai kuskure. Wanda kuma yace ta halatta saboda koyi da malaman da suka ce wannan sauraro haka ne to ya bar tsantseni ga sauraronsa amma mai kyautatawa ne ga iliminsa da halaye na wannan abu.
(5) Wasu kuma sunce wadanda nutsuwa take zuwa musu da jin dadi yayin sauraron irin wadannan kade-kade da raye-raye kamar sauraron jita da algaita ko kakaki da sauraron abubuwan kade-kade na zamani da ake yi ayau sune natsuwa a gare su, to suna aiki ne da abinda addini ya haramta. Kuma in ya sami jin dadi da wadannan abubuwa da ayke sauraro to, ya zama mai hada abubuwa kyawawa da munana wato mai amfani da mai cutarwa, to mai irin wannan hali yana zaton cewa kyauwawan halinsa za su mamaye munana, to mai wanna hali yana ganin cewa halal ne yake sauraro. Sai malaman sufaye suka ce in ya sami natsuwa to ya zama halas a gare shi. Kuma in ya hada kade-kade na batsa wato na haduwar maza da mata to, yana nuna cewa ya kara sha’awarsa kenan da sabonsa.
Shehu Usman Danfodiyo yace: “Sauraron kade-kade da raye-raye kamar yadda sufaye suka ce yana kara son addini da nutsuwa, wannan yana nuna tsaurin kai ne da keta hukunce-hukuncen Ubangiji, don kuwa da yana da kyau to, da Allah ya umarci annabawa da su rika sauraro da aikatawa kuma suna kwadaitar da mabiyansu don su rika yi. Kuma yace ba wani labari da aka samu daga annabawa ko manyan maluma da suka gabata na cewa wai sauraron kade-kade yana kara sa natsuwa da shiriya ga mai yinsa. Kuma ga shi Allah yace “addinin say a cika, inda yake fadin cewa, “A yau na cika muku addinin ku.” To da ace sauraron kade-kade da wake-wake addini ne, to da Annabi ya fada kafin cikar addinin.
Haka kuma Annabi mai tsira da amincin Allah yace “ina rantsuwa da wanda numfashina yake hanunsa, ban bar abinda zai kai ku zuwa aljuannah ba, kuma ya nisanta ku ga barin wuta said a na umarce ku. Kuma yace ban bar abin da zai kai ku wuta ba, ya nesanta ku ga barin shiga aljannah said a na hane ku, kada ku aikata shi.
Shikah Abubakar Gumi yace, “Duk wadannan maganganu da ake yi akan sauraron kade-kade neb a akan aiki da suba. Kuma ba wani wanda zai ce sauraron Kur’ani da za’azi da karantarwa bai halatta ba, kuma duk wanda ya musanta sauraron Kur’ani da wa’azi da karantarwa cewa ba halal bane to, kafiri ne. Haka ma buga dundufa da wake-wake a loakcin bukukuwa na ranar Idi yadda addini ya nuna.
Kuma abin da aka ce haramun shine, hada kade-kade da raye-raye da ambaton sunan Allah da manzonsa. To, masu yin irin wannankam, sun zama masu aikata munanan ayyuka. Matukar basu bari ba Allah ya yi masu alkawari da yi musu azaba ranar Alkiyama, inda yake cewa, “masu irin wannan kade-kade da wake-wake a masallaci, sallar su bata zama ba, addu’o’in sub a su zama ba a masallaci sai dai sowa da kuma tafi. To, za’a ce musu ku dandani azaba ranar kiyamasaboda izigili da wargi da kuka yi. (Anfal 35).
MATSAYIN DA SUFAYE SUKE BA MABIYANSU
Sheikh Gumi yace, “duk wadannan abubuwan da ake dangana su ga sufaye ba gaskiya bane, kuma duk ayyuka ne na sahidanun malamai da suke saka shi a cikin addini, kuma abubuwane da suka dauko su daga Yahudu da Nasara, domin kuma duk wanda yake ganin zai iya azurta wani ko ya talauta shi ko ya san wani ilimi na boye da na sarari to, wannan kafirci ne saboda fadin Allah da kuma sunnah da haduwar malamai sunnah.
Allah yana cewa “kace sama da kasa ba wanda yasan gaibi sai Allah da kuma sunnah da haduwar malami sunnah.
Allah yana cewa “kace sama da kasa ba wanda yasan gaibi sai Allah. Kuma ba wanda ya san ranar da za’a tada matattu sai Allah.” (Namli 65). Kuma Allah yace ya Annabi “Kai ba ka iya mallaka wa kanka abin da zai cutar da kai, sai abin da Allah ya dora maka, da kasan ilmin gaibi da ka yawaita aikin alheri dab a wani hadari da zai same ka, don haka ne kai mutum ne mai gargadi da albishir ga muminai. (A’araf 188). Allah ya ci gaba da cewa, “wanda Allah ya shiryar, shi ne shiryayye, wanda kuma Allah ya batar to, sune masu hasara. (A’araf 178). Kuma Allah yace wa Annabi mai tsira da amincin Allah, “kai ba ka da ikon shiryar da wanda kake so, sai da Allah shi ke shiryar da wanda ya so, don shi ne mafi sanin shiryayyu”. (Kasas 56). Kuma Allah yace “kace kaifa mai kira ne zuwa ga Allah, ni kuwa b azan hada Allah da kowa ba, kuma ka gaya musu ni ban mallaki batar da ku ba haka shiryar ku, kuma ka gaya musu kai in ka saba wa Allah, ba wanda zai tserar da kai, kuma baka da wata mafaka. Ni dai mai isar da sakon Allah ne kuma manzon Allah, duk wanda ya sabawa Allah da manzonsa makomarsa jahannama ce, kuma zai tabbata har abada”. (Jinnu 19-20). Wadannan sune hujjoji daga wajen Allah cewa ba wanda ya san gaibi ko wani ilimi na badi’ni da zai iya talauta kako azurtaka ko kasha ka ko raya ka, sai Allah.
Dalilai kuma daga sunnah gasu kamar haka: Daga Abu-haurairah, “Annabi mai tsira da aminci yace “Ba wani wanda aikinsa zai tsear da shi. Sai wani mutum yace “hyar kai ya manzon Allah? Sai yace ‘e’ har ni ma, sai dai in Allah ya lullube ni da rahamarsa, amma duk da haka kowa ya yi kokarin gabatar da ayyuka masu kyau”. (Imam Muslim). Kuma Imam Nawawi yayi Karin bayani cewa wannan hadisi game da mazahabar malaman sunnah ba wani mai tabbatar da hukunci cewa wane dan aljannah ne ko wane dan wuta ne ko halal ne ko harma, sai in shari’a ce ta bayyana haka. Wanda kuma ya dauki matsayin halatta wani abu ko harmata wani abu to ya yi kama da Bayahude ko banasare.
Saboda Allah ya siffanta Yahudu da Nasara da suke koda kawunan su da cewa “mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa ne” yayin da suke dauki hukunci a hannunsu, inda suka ce ba wabnimai shiga aljannah sai Bayahude ko Banasare. Sai Allah ya musu raddi da cewa “shin baku ga wadanda suka tsarkake kawunansu ba, sukace su ‘ya’yan Allah ne? karya suke yi. Allah ne yake tsarkake wanda yake so, kuma Allah ba zai zalunci kowa ba koda kamar fatar jikin dabino.
Ya ci gaba da cewa “duba kaga yadda suke kirkirar karya su jingina ga Ubangiji? Wannan ya zama musu babban lafifi, mummuna a wajen Ubangiji. (Nisa’I 49).
Kuma da Bukhari da Muslim suna cewa, Annabi ya ji wani mutum yana yabon wani mutum sai yace, “Amma ka sare wuyan abokinka in ya zama ba yadda zaka yi sai ka yabi wani to, ka ce ina zaton wane mutumin kirki ne, sabdoaba wani wanda zai iya tsarkake wani a wajen ubangiji). Kuma daga Khalifa Umar Allah ya yarda da shi cewa “duk wanda yace shi mumini ne to, shi kafirine, wanda kuma yace, shi malami ne, to shi jahili ne, wanda kuma yace yana da aljannah to shi dan wuta ne. daga Ibnu Khasir a cikin littafinsa. To, wadannan hujjoji sune suka hana mutum ya dauki hukunci a hannunsa na cewa wane dan Aljannah ko dan Wuta ne.
DAGA LITTAFIN; AL-AKIDATUSSAHIHATA BI MUWAFAKATUS, NA MARIGAYI SHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI {R
No comments:
Post a Comment