GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINSUNNAH-BLOGSPOT.BLOGSPOT.COM


WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA LACCOCI DAGA MALAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI; {mumbarinsunnah@gmail.com]

Monday 17 September 2012

‘YAN ALKUR’ANIYYUN (‘YAN TATSINE, KALA-KATO) TARIHIN KAFUWARSU DA AKIDUNSU {2}


ASALIN ‘YAN ALKUR’ANIYYUN DA TARIHN KAFUWARSU

Wannan mummunar akida ta samo asali ne daga wadannan kungiyoyi wadanda sune suka fara kin bin hadisan Manzon Allah (S.A.W.) da kin yin aiki dasu tun a karni na farko, sune manyan kungiyoyi kamar haka :
1.   Kungiyar Rawafidh (‘Yan shi’a)
2.   Kungiyar Mu’utazila (Mu’utazilawa)
3.   Kungiyar Khawarij. (Khawarijawa)

Wadannan kungiyoyi su suka fara bore ko tawaye akan yin aiki da hadisan Annabi (S.A.W.) duk da cewa wadansu daga cikinsu ba dukkan hadisan suka yi wa tawaye ba, sun dai raba sun dauki wasu, sun kuma watsar da wasu.


Misali:
       Kungiyar Shi’ah; su mabiya kungiyar shi’ah, babban dalilin day a jefa su cikin wannan hali, shine kafirta mafi yawa daga cikin sahabban Manzon Allah (S.A.W.), wannan kowane hadisi idan ka biyo salsalarsa, (wane-yaji-daga-wane) yana tukewa ne zuwa ga sahabbai kamarsu Abu Hurairata, Abdullahi bin Umar, Abubakar Siddiq, Umar bin Khattab da dai sauransu (Allah ya kara masu yarda), duk wadannan shabban a wurin ‘yan shi’ah kafirai ne, saboda haka hadisan da suka rawaito ya rushe kenan, tun da matattakalar karshe bata inganta ba. To da wannan ne ‘yan Shi’a suka hallaka kuma suke hallkarwa, suka watsar da mafi yawa daga cikin hadisan Manzon Allah (S.A.W.), kuma ta dalilin hakan suka kafirta.
       Imamu Malik bin Anas (R.A.) ya bada fatawa cewa “Rawafidh” (‘yan shi’ah) kafirai ne, saboda bayan Allah (S.W.T) ya bayyana darajar Annabinsa (S.A.W) da daraja sahabbansa da irin abinda ya siffanta su da shi a cikin littafin Attaura da Injila, sai Allah (S.W.T) ya bayyana dalilin basu wannan daraja da matsayi da cewa :

"ليغيظ بهم الكفار"     الفتح 29
Ma’ana “Domin (Allah) ya fusatar da kafirai da su” (suratul Fathi: 29)
       Saboda haka Imamu Malik ya dogara da wannan aya wajan kafirta “Rawafidh” (‘yan shi’ah) kuma Malamai da dama sun goya masa baya akan haka.
       Kungiyar Khawarij; su kuma mabiya kungiyar khawarij akidar data hallakar da su itace su aganinsu, a lokacin halifancin Abubakar Siddiq da Umar Faruk da Usman bin Affan dukkanin sahabbai a tsabtace suke, kuma sun yarda da dukkanin hadisansu, amma daga lokacin halifancin Aliyu dan Abi Dalib da aka samu rashin fahimtar juna tsakaninsa da Mu’awiya Dan Abi Sufyan (Allah ya yarda da su gaba daya), sai suak tsame kansu daga cikin musulmi suka kafa wannan kungiya ta khawarijanci, sannan suka tsarawa kansu cewa duk wanda ya shiga cikin wannan rikici na tsakanin halifa Aliyu bin Abi dalib da Mu’awiyya bin Abi Sufyan ya zama kafiri.
       Sannan suka sake tsarawa kansu cewa duk hadisan da sahabbai suka fada ba abin yarda bane saboda faruwan wannan rikici, daga nan ne suka hallaka kuma suka hallakar. Allah ya kiyayemu. Amin.
       Kungiyar Mu’utazila; su mabiya wannan kungiya babbar matsalarsu itace gabatar da hankali akan nassi wajen tabbatar da abu ko koreshi a cikin addinin, duk abinda hankali ya gay a yi daidai to daidai ba, to ba daidai ba ne, ko da nassi ya tabbatar da shi ko yak ore shi, don haka suka dauki wannan ka’ida akan kowane hadisi, cewa idan ya dace da hakalinsu sai su yi aiki da shi, in kuma bai dace da hakalinsu ba sai su yi watsi da shi, da wannan mummunar akida suka fake suke karyata hadisan Manzon Allah (S.A.W.) suka bata kuma suke batar da la’ummar musulmi masu yawa. Allah yak are mu daga bin son zuciya, amin.
       Wadannan sune kungiyoyin da suka fara kin aiki da hadisan Manzon Allah (S.A.W), sai dai ba a fili suka fito suka fada ba, sun bi wadansu ka’idoji ne da hanyoyi da suka kirkira kamar yadda muka yi bayani a baya wanda ta hakane suka kai ga wadancan munanan akidun da suka halakar dasu.
       A lokacin da wadannan mutanan akidu suka bayyana Manya – Manyan malamai magabata sun mayar masu da martini a rubuce, da kuma wuraren gabatar da darussa da fatawa, wannan ya sa galibin littattafan da aka fara wallafawa a lokacin suke kunshe da raddi ga wadannan munanan akidu.

Misali :
       Imamul Bukhari ya kulla babi – babi masu yawa (a cikin littafinsa) don raddi ga irin wadancan akidu, sannan daga cikin littattafan da malami suka wallafa aka haka, sun hada da “Assunnah” na Imamul Khallal, da “Assunnah” na Imamul-Aajurriy, da “Al’ibana” na Ibn Baddah, da makamantansu. Kuma duk wadannan littattafai daga mai shekara dubu sai sama da haka, ko kasa da haka kadan; duk kuma an yi sun e don mayar da martini akan wadanda suke inkarin Hadisan Manzon Allah (S.A.W) da sauran bidi’o’I da suka saba wa tafarkin Annabi tsira (S.A.W.).

TARIHIN ‘YAN ALKUR’ANIYYU A WANNAN ZAMANI
       Wadanda suka fara inkarin hadisan Manzon Allah (S.A.W) a wannan zamani sun kasu kashi biyu:

Kaso na farko : Sune ‘Yan kala-kato ko ‘Yan tatsine zalla, saboda sun fito fili da bakinsu suna cewa bas u yarda da hadisan Manzon Allah (S.A.W) ba.

Kaso na biyu : sune wadanda ta dabara da hankali suke kore hadisan, idan aka ce musu  ‘yan tashine ko ‘yan kala-kato sai su ce: “sub a ‘yan tatsine bane kuma ba ‘yan kala-kato bane”
       Farkon wanda ya fito da wannan da’awa a fili aka santa shine mutumin da ake kira “Gulam Nabiyu” sunansa na hakika Abdullahi Jakralawiy, ya kafa wannan kungiya ta shi a garin da ake kira “Lahur” a can cikin kasar Pakistan a yau, a shekara 1902AC.
       Ya samu goyon bayan wani mutum da ake kira “muhibbud-deen Azeem Abadi” wanda yake yafi shi Abdullahi Jakralawiy ilimi, sai dai shi Jakralawiy yafi shi saboda shi ne ya kafa kungiyar.
       Muhibbud-deen ya rubuta littattafai akan wannan da’awa kamar “Minhajul-Kakki”. A cikin Balagul-Hakki ya fito fili karara ya yi inkarin hadisan Manzon Allah (S.A.W). Sannan ya fito da littafin fili a garin Karachi dake kasar Pakistan.
       A daidai lokacin da Abdullahi Jakralawi ya kafa wannan kungiya ta sa, a daidai lokacin kuma Mirza Ahmad Al-kadiyani wanda aka fi sani da (Ahmad Gulam) shi ma ya kafa ta sa kungiyar mai suna “Ahmadiyyah”, a dalilin haka fitinu guda biyu suka bullo a lokaci guda daga wannan yanki. Ahmad Al-kadiyani yana da’awar shi Annabi ne! shi kuma Abdullahi Jakralawiy yana cewa “bai yarda da Manganar Annabi ba gaba daya (wato hadisi).
       Wani abin mamaki a wannan lokacin shi ne, yadda Turawan Ingila suak goyi bayan wadannan mutane guda biyu, saboda goya musu baya zai dakushe wa musulmi karfinsu na fuskantar su (Turawan) da yaki da mulkinsu na mallaka, domin yawan musulmai kadai a Indiya ya fi yawan mutanen Najeriya gaba daya. Saboa haka suka ga hanyan da za su cigaba da mulkin mallaka itace su goya wa wadannanmutanen guda biyu baya, saboda haka, a lokacin da Ahmad Gulam ya fito da da’awarsa, sai suka goya masa baya yaci gaba da yadata da sunan “Ahmadiyya”, shi ma jakralawiy suka goya masa baya ya ci gaba da yada kin hadisan Manzon Allah (S.A.W), duk kuma sun yi haka ne a karkashin siyasarsu da suke cewa:
"فَرَّقْ تَسُدْ"
Ma’ana “Raba kan mutane sai ka mallake su
      
       Wadannan mutane sune suka fito da wannan da’awa a wancan loakci a shekarar 1902 AC, sun kuma samu goyon bayan malamansu daban – daban, wadanda suka yada wannan mummunar akidar, daga cikinsu akwai.
1.   Ahmad-deen Ibul Khawaja, wanda ake kira Mayyan Ibnu Muhammad Ibnu Ibrahim, wanda aka Haifa a shekara ta 1861AC.
2.   Alhafiz Aslam Jerasbuji wanda aka Haifa a shekara ta 1880AC
3.   Gulam Ahmad Baar Wazeer Ibnu Fadi Ibnu Raheem Ibnu baksh wanda aka Haifa a shekara ta 1903AC da dai sauransu.

Wannan akida taita yaduwa har zuwa lokacin da shugaban kasar Libiya Ma’amar Gaddafi ya fito fili ya bayyana ta tare da nuna goyon bayansa ga wannan mummunar akida a wurin wani taron maulidi day a yi a shekarar 1978AC. Inda ya fito fili yace:
Babu yadda za’a a yi duniyar musulmi ta cigaba har sia an kona dukkan littattafai an bar Al’kur’ani kadai
       Bayan Gaddafi ya bayyana wannan akida ne, sai kungiyar Rabidatul Alamil Islami da ked a cibiya a kasar Saudi Arebiya suka tura masa wadanda za su yi masa nasiha, wanda a cikinsu akwai babban malaminmu Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Allah ya jikansa) kuma yana daya daga cikin malaman da suka kausasa masa Magana saboda tsananin kishinsu da sunnah, da kuma sanin hadarin wannan akida.
       Daga nan sai wani dan asalin kasar Misra mai suna rashad Khalifa ya bullo wanda yake zaune a kasar Amurka ya rungumi wannan akida, ya shiga yadata ta hanyar rubuce-rubuce da harshen turanci, dama shi yayi karatun lauyanci, daga karshe ma wasu rubuce-rubucen nasa suna nuna cewa shi ma yana da’awar Annabta, kuma a yanzu haka yana da magoya baya a wannan kasa tamu ta Nijeriya, a Jihar Kano yana da su a wasu unguwanni har ma suna sallar Juma’a a wani shago, haka kuma a Maiduguri a unguwar Danbuwa Road, a nan Kaduna ma akwai magoya bayansa.
       Wannan a takaice shine tarihin kafuwar wannan mummunar akida a wannan zamani da kuma wadanda suka yada ta. Allah ya kare mu.
BY SHEIKH JA’AFAR MAHMUD ADAM

No comments:

Post a Comment