BAMBANCIN SUNAN ALLAH DA SUNAN DAGUTU
A cikin wannan littafi ya gabata cewa kalmar shahada itace gainshikin addini, kuma da saninta ne kowane ilimi na duniya da na lahira ke ginuwa, ma’anar “la’ilaha illallahu” Ba wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ma’anar Anna nabiyu rasulluha shi ne ‘Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, duk wand aya bautawa Allah bada abin da Annabi Muhamamdu mai tsira da amincin Allah ya zo da shi ba to, Allah ba zai karba ba, kuma ranar tashin kiyama yana cikin tababbu masu asara. Saboda haka ne ma sakon Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah take karshen sako, kuma shi ne cikamakin Annabawa, ba wani Annabi a bayansa. Saboda haka duk waniw anda ya zo da wani sako bayan na Annabi to, ba sako ban e, kuma ba za’a karba masa ba.
Hakakuma Annabi mai tsira da amincin Allah baya amsa fatawa bayan mutwarsa don Annabi bai bar duniya ba saida Allah ya cika addinsa ya kuma cika ni’imarsa ya kuma yarda da cewa Musulunci shine addini. Kuma Allah ya yi alkawari zai tsare wannan addini kamar yadda ya saukar da shi. Don haka godiya ta tabbata ga Allah akan wannan alkawari da yayi mana.
Sheikh Gumi yaci gaba da cewa “ya kamata musan ma’anar Allah da kuma kalmar dagutu”. Wanda ya zo a cikin Al’Kur’ani cewa ba bu tilastawa a addinin don kuwa hakika gaskiya ta bayyana daga bata duk wanda ya kafirce wa dagutu ya yi imani da Allah to ya yi riko da igiya mai karfi wadda ba za tat sin ke ba, Allah kuma mai ji ne kuma masani. (Bakara 256).
Ma’anar “ilahu” ma’anarsa shine duk wani wanda yake halatta wani abu kuma yayi umarni da shi ko ya haramta shi ko ya halatta shi ba tare da wani togo ba ko wani tsoron kowa ba to ilahu ya kasu kashi biyu. Ma’anar na farko shi ne Allah daya aiko Muhamamdu mai tsira da amincin Allah zuwa ga mutane gabaki daya da hujjoji mabayyana da dalilai na yankan shakku to wanna shine ubangiji na gaskiya. Wanda ya bishi shi ne wanda yayi riko da igiya daba ta yankewa wannan mutum ranar tashin kiyama ya tsira.
Ma’anar abin bauta na biyu kuwa abin da Allah bai saukar wa Annabi Muhamamdu mai tsira da amicnin Allah to wannan shi ne dagutu.
Ya zo a cikin littafin Imam Shuyudi mai suna Itikanu fee ulumil Qur’an, yace ma’anar dagutu wani boka ne a Habsha, kuma ya zo a Kamus cewa (khahinu min khahana) ne ka nahara hahana lahu). Ai ma’anar wadannan kalmomi shi ne wanda ya bad a labari da abin da yake boye. Ko kalmar ta zo daga (khahana) daga babin (karuma). Ma’anarsa wanda yana bokanci ko al’adarsa yana bokacni ne
Don Allah yana cewa Allah shi ne waliyin masu imani don yana fitar da su daga cikin duffai kuma izuwa haske wandanda suke kafirai kuma sune waliynasu suna fitar da su daga haske suna kais u zuwa duhu. Wadannan kuwa sune ma’abota shiga wuta suna masu tabbata a cikinta (Bakara 257).
Kuma ya zo a cikin wani littafi na tafsiri cewa kalmar (zulumat) ana nufin kafrici ne (Nuru) kuma ana nufin imani ne kuma bin boka kafircewa ne da Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah.
MA’ANAR MUSULUNCI DA MA’ANAR SHARI’A
Ma’anar Musulunci itace rayuwa da Allah ya shar’anta ta, ta harshen Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah, shi kuam ya dauko ta zuwa gare mu. Duk wanda ya bit cikin dukkan almarinsa na’ibada da mu’amalarsa, to, shi ne muslmi, wanda ya riki Allah shine ubangijinsa, kuma majibincin al’amrainsa. Wanda kuma ya saba wa wanin wannan to, ya riki wanine, kuma Ubangijinsa ba Allah bane, kuma wani ne zai jibanci al’amarinsa. To, kowane Alkali da zai hukunci ga abinda Allah ya saukar, sai yayi bad a shiba, to ya zama fasiki, in ya kudurta haka
Haramun ne. amma in y ace “wadan da basu yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba to, sune kafirai. Kuma Allah yace “wandannan sune azzalumai. Haka kuma wadanda basu yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, wadannan sune fasikai”. { Suratul ma’ida, aya ta 44 zuwa ta 47}.
Haka kuma hukuncin yake wanda ya kai kara wajen alakali da yasan ba musulmi ba, kuma ya san akwai wanda yake musulmi to, in ya kudurce cewa hakan bai halatta ba to, ya zama mai saba wa Allah. Kuma a cikin aikinsa shi fasiki ne. in kuam ya halatta yin hakan halal ne to, shi kafiri ne, sai dia in ya tuba. Don yarda da kafirci, kafirci ne, saboda fadar Allah cewa “Baka ga wadanda aka basu rabo na littafi, amman suna imani da bokiacni da sihiri suna cewa wadanda suka kafirta cewa kune kuka fi shiriya daga muminai da suka yi imani da Annabi mai tsira da aminci Allah. To, wadannan masu yin wannan Magana sune wadanda Allah ya tsine musu, wanda Allah ya tsine masa kuma to ba, shi da wani mai taimakonsa a wajen ubangiji. (Suratul Nisa’I, aya ta 51-52).
Ma’nar “Dagutu” shi ne boka. Ma’anar “Jibtu” kuma shi ne, shaidanin malami ko mai sihiri. Kuma Imamu suyudi ya fada a cikin littafinsa mai suna “(Ittikanu)” hadisin da Abi Khatib ya fitar cewa ma’anar Dagutu shine wani shaidani ne a kasar Habasha. Haka Abdullahi dan Khumairi, ya sami hadisi daga Ikhramata cewa ma’anar Jibtu da yaren habasha shi ne shaidan. Haka kuma an fitar daga.
Ibnu Jarir daga Sa’idu dan Jubairu, cewa abin da ake nufi da Dagugu a yaren habasha shine, sahiru (wato Dan damfara). Sheik Gumi yace “shi sha’idan shine wanda ya san gaskiya kuma yaki aiki da ita to shi ne shaidan, wanda ana samunsu daga mutane da kuma aljannu. Yazo a cikin Al’kur’ani mai girma, Allah yace “A cikin suratul (Jasiyah) Allah ya halicci sammai da kassai da gaskiya don ya saka wa kowace raid a abin da ta aikata, alheri kuwa ba za’a zalunci kowa ba” kuma Allah ya ci gaba da cewa “ko kaga wanda ya riki son zuciyarsa ta zamo masa ubangiji, kuma Allah ya batar da shi bisa saninsa ko a bisa ilimansa, kuma ya rufe jinsa da zuciyarsa, kuma ya sanya wani rufi a ganisa, to wanene zai iya shiryar da wannan in ba Allah ba, me yasa ba kwa wa’azantuwa? “(Suratul Jasiyah aya ta 22). Daga nan ne za’a iya ganin cewa duk wanda ya dauki krarsa yakai wa wanin Allah hakika ya kafirta. Haka kuma hukunci bada littafin Allah, ba, to ka fircine. Kuma duk wanda aka fada to, ibada ne wanda bai halatta a bi wanin Allalh ba a cikinsu. Kuma a wannan ban garen musulmi da yawa sun bace wadanda suka bar addinsu tsayayye kuma suka yi jayayya a tsakaninsu, sai karfinsu ya karye kuma kwarjininsu ya bace. Allah ya dawo musu da karfinsu.
Wadansu malamai suna cewa “al’umma ba za ta gyaru ba said a abin day a gyaru na farko, wannan kuma jarabawa ce wadda ta game kassashne musulmai (wato barin aiki da shari’ar Allah).
GUBA DA AKA SA A CIKIN LITTATTAIFAI DA WAYEWA IRIN TA TURAWA
Makiyan musulunci su na ta kawo hari gabas da yamma, kudu da arewa don su yi nasara akan musulunci da musulmai, amma sun gagara yin nasara sai dai ta hanayr yin yaudara, kuma suna ganin wanda bai yi koyi da ci gabansu ba to, ba wayayye bane. Don haka ne sai suka bi ta hanayr ilmin book suka dasa musu guda da za su karkatar da su a bisa koyon addini sai dai ilmin neman duniya kawai. Kuma suka karkatar da su wajen koyon luggar Larabci wacce itace hanyar koyon addinin musulunci, kuma wanda ya jahilci ta to, hakika ya jahilci addinin musulucni, suka dogara da wasu rubuce-rubuce na bata tarbiya da halaye na gari kuma suna rushe sunna. Wasu littattafanm ma aka yi su ta hanyar wasu darikoki daban daban da sunan (“Kashfu”) walwilyat” (wato mai yayewa da wattsaka). Suna dasa su ta hanayr shehunai na kungiyoyin dariki daban-daban har ana girmama su, ana basu iko na kololuwa da martabobi masu girma, sailaka canza ilmin addini wajan karantarwa dawasu littattafai na sirruka da wake-wake don bata addini. Sai aka bar bin shari’a ta gaskiya aka koma ga bin son zuciya, aka koma cikin bata, wanda aka bar hanyar gaskiya, aka koma ga bin kame – kame.
Kuma a bangare na biyu, Turawa suka giggina makarantu manya manay don koyar da ilimin book saboda su dasa munanan akidu a zukatan ‘ya’yan musulmi a ko’ina cikin kasashen musulunci na duniya. Wanda da farko suka dauki iyayen Arna masu tafiya tsirara wadanda basu san wadansu dabi’u masu kyau ba balle ma sanin mutuncin kansu, sai suka sanya su sune shugabanin a manya-mayan makarantun da ska gina da kuma manya – mayan ma’aikatun da suka gina da masana’antu, na gwamnati ya ma sune manya, wanda ya zanna komai zaka nema a kasar ku sai ka bi ta hannunsu, sia suka zama sun wayi gari sune ‘yan mulkin mallaka, kuma sun mamaye komai har suka mamaye zukatan musulmai wadanda suka yi barci cikin rafkana da raye-raye da kirkire-kirkire na karya.
Lokacin da musulmai suka farka daga mummunan barici da suke yi mai nauyi sia suka ga komai yana hanun makiyansu, wanda ya zama dole su dauki ‘ya’yansu su saka su a hannu wadannan makiyan na su don ko za su kubuta, kuma tanan ne suka gwamatsa ‘ya’yansu har suka tashi da munanan dabi’o’I na Turawa wajen ha’inci da kin shawara da rashin tsoron Allah na su Turawan da magoya bayansu harda fasikanci da shangiya da neman mata. Wanda wannan shi ne ya gurbata ‘ya’yann musulmi, wanda suka bata musu komai da komai na tarbiya. Sai ya zamanto sun ta shi da dabi’o’insu kuma suka mayar da su Karen farauta ko kuma danko na kama kuda, wanda da ga karshe aka mayar da giya da taba da kwayoyi ba abban kyama bane ga duk wadanda suka koyi wadannan dabi’oin na karatunsu. Sai aka sanar da su kamar yadda ake koyar da kare na yadda zai kamo abin farauta a hannun maharba daga cikin gida har zuwa kasashen Turai. Sai wasu musulmai suka zamo ‘yan kanzagin turawa, sai ka ga mutum musulmi ne, amma yana sukan musulmi da musulunci cewa duk wanda bai yarda da ta’ada na turawa ba, to shi ba wayayye bane, sunha kiran irin wannan cigaba wai (civilization) wato wayewa.
Saboda haka, zaka ga musulman da aka dasu musu wadannan gaba a zukatansu, za su rika sukan musulunci kamar ba musulman ba. To tan wannan hanyace kadai Turawa suka sami nasara, in ma sun samu din. Saboda yadda musulunci ya gano irin wadanan miyagun dabi’un a cikinsa, da izinin Allah sai ya yi mganin irin wadannan makircin su kamar yadda yace “hakika rundunar mu inji Allah sune masu rinjaye.
HANYOYIN DA AKABI DON A TANTANCE LITTATTAFAI MASU KYAU DAGA LITTATTAFAN DA AKA DASA MUSU GUBA IRIN NA TURAWAN YAMMA
Mai martaba Muhammadu Bello dan Shehu Usman Dan – Fodiyo Allah ya jikansa ya fada a cikin littafinsa, cewa “Bai halatta ga dalibi ya shagalta karanta irin wadannan littattafai ba, saboda mafi yawan abin da ke cikinsu ya saba wa shari’a. Shiekh Gumi yace “irin wadannan littattafai” suna nan da yawa a hannun mutane wadanda ma wasu basu saniba cewa batattune har ma sun fi littattafan addini na gaskiya yawa ba za ma a iya sanin iyakarsu ba saboda yawansu. Amma ga lamomin da ake iya gane wadansu daga cikinsu.
Duk wani littafi da yake nuna mukamomin waliyai, kamar ace ai wane (kudubi) ne, ai wane (gausi ne), yana iya ganin Allah ko zai iya lamunce maka aljanna, da duk littafin da zia nuna maka ga yadda za ka yi mubaya’a da wani Shehi don ka sami amincewar Allah, da kuma duk wani littafi daya ke maka nuni da cewa ga yadda zaka yi ka kai matsayin ka tattuna da Allah, da kuma wani littafin daya ke maka nuni ga yadad zak ayi Magana da Annabi har ka kai ga ganin Allah. To, musalin wadannan littattafai sune “Fiyudati rabbaniyatu fil ma’asiri walauradil kadiriyyah” wanna littafi ne dake koyar da darikar kadiryya. Da duk wani littafi mai koyar da darikar Tijjaniyya amma ba irin wanda Shaikh Tijjani ya rubuta da kansa ba. Da kuma kowane littafi da ke koyar da Kadiriyya, amma ba wanda Shaikh Abdulkadir ya rubuta da kansa ba. Kamar littafin jawahirul ma’ani na ‘yan Tijjaniyya, da duk wani abin da aka fitar a cikinsa, basu da kyau a guje su.
Haka kuma duk wani littafi da ke hana karanta karatun addini ko Larabci wadannan sune tsayuwar addini amma a hana karanta shi, da kuma duk wani littafi da yake karantar da cewa wai a yi wa wani Shehi hidima don ka sami lamirin cewar Ubangiji, wanda har ma suna cewa ka zauna a gaban Shehinka kamar gawa a hannun masu mata manka, wato sai abin da Shehi yace ka yi tukun zaka yi. Da duk wadansu littattafai na maluma da ke nuni akan bin bidi’o’I da son zuciya, wadanda suke nuni da cewa in ka I abu ka za, zaka sami wani abu na dukiya ko mata da sauran abubuwa na alheri ko sharri. To wadannan duk littattafai ne da suke dora mutane akan sharri da shiga duhu da fitar da su daga haske zuwa duhu. Alhali kuwa Allah yana kiranku zuwa ga gidan aminci, kuma shi ke shiryar da wanda yake so zuwa ga gidan aminci. Kuma wadansu za su tambaye ka cewa yanzu dk wadannan abubuwa da aka fada gaskiyane? To, ka rantse da Allah cewa “na ranste da ubangijina cewa gaskiya ne an fada kuma idan kunki to, ba za ku gagari Allah ba a duk inda kuke.
Sheikh Abubakar Gumi ya rufe da cewa “wadannan nasihohi da na fada na fade sune don mutane su farka daga barcin da sukayi da fatan ya zama jagora da aiki da shi ga duk wanda ya karanta. Kuma ina rokon Allah ya sa nayi don neman yardarsa ne, kuma mun gode Allah daya shiryar damu, kuma bamu isa mu shiriya ba, ba don Allah ya shiryar damu ba. Wanda yace mun saukar da Al’Kura’ni abin wa’azi da gargadi, kuma mune za mu kiyaye shi, Allah yayi gaskiya.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin dukkan Annabawa Annabi Muhamamdu mai tsira da aminci kuma cikamakin Annabawa shugaban manzanni da mutanen gidansa da abokansa da duk masu bin umarninsa da kyautatawa har zuwa ranar tashin alkiyama. DAGA LITTAFIN;
No comments:
Post a Comment