HUJJOJIN ‘YAN AL’KUR’ANIYYUN DA AMSA AKAN KOWACCE
Abu ne sananne cewa, duk wani batacce ko mai da’awa yana samun wadansu abubuwa da zai rike a matsayin dalilai ko madogarar day a say a yarda da wannan da’awa, yake kuma yada ta, kuma yake kiran mutane akanta.
‘Yan Alkur’aniyyun ko ‘yan tatsine ko ‘Yan kala-kato babbar madogarar da suke kafa hujja da ita itace wasu ayoyi daga cikin Al’Kur’ani mai girma da suka fahimcesu bisa kuskure, ga wasu daga cikin wadannan ayoyi, da kuma amsoshin da malamai suka basu akansu.
1. Daga cikin hujjojinsu akwai: Fadin Allah (SWT)
"فبأيِّ حديثٍ بعده يؤمنون" سورة المرسلات 50
Ma’ana “To da wane labari ne bayansa (Alkur’ani) suke yin imani?”(Suratul Mursalat: 50)
Da fadin Allah (S.W.T)
"...فبأيِّ حديثٍ بعد الله وآياته يؤمنون" سورة الجاثية:6
Ma’ana “To da wane labari bayan Allah da ayoyinsa suke yin imani? (Suratul Jathiyah: 6)
‘Yan Al’kur’aniyyun ko ‘Yan tatsine ko ‘Yan kala-kato sukan fassara wadanan ayoyi da cewa “Da wane hadisi bayan Alkur’ani suke yin imani”
Amsa anan ita ce : sun manta da cewa larabci harshe ne mai zaman kansa tun karfin a saukar da Alkur’ani, harshe ne da mutane suke Magana da shi, lokacin da Allah (S.W.T.) ya tashi saukar da Alkur’ani sai ya zabi harshen larabci ya saukar da Alkur’ani da shi, kamar yadda ya bayyana a cikin littafinsa inda yake cewa:
"إنا أنزلناه قرآنا عربيا لعلكم تعقلون" سورة يوسف: 2
Ma’ana “Lallai ne mu muka saukar da shi yana abin karantawa da larabci, domin ku hakalta” (Suratul Yusuf : 2)
A wata ayar kuma ya sake cewa:
وإنه لتنـزيل رب العالمين* نزل به الروح الأمين* على قلبك لتكون من المنذرين* بلسان عربي مبين* سورة الشعراء: 80
Ma’ana: “Kuma lallai ne shi (Alkur’ani) abin saukarwa ne daga Ubangijin halittu, Ruhi amintacce ne ya saukar da shi, Akan zuciyarka domin ka kasance daga masu gargadi, da harshe na larabci mabayyani” (Suratul shu’ara: 192-195)
Duk wadannan ayoyi da makamantansu suna nuna an saukar da Alkur’ani da harshen larabci, kuma shi larabci harshe ne wanda ake Magana da shi kafin zuwan addinin musulunci. tunda Allah (SWT) Ya saukar da Alkur’ani mai girma da harshen larabci, sai ya kasance wadansu kalmomi ya barsu da ma’anarsu ta larabci kamar yadda suke, wadansu kuwa ya canza musu ma’ana suka dauki ma’ana ta shari’ar musulunci, saboda Alkur’ani ya sauko ne domin karantar da shari’ah ba karantar da harshen larabci ba. Don haka a wurare da dama cikin Alkur’ani zamu ga wata kalmar ta larabci wanda muka san ma’anarta da larabci, amma shria’a tab a ta wata ma’ana sabanin ma’anar da muka santa a harshen larabci. Saboda haka idan muka zo bautawa Allah sai mu bauta masa da shari’a bad a yaren larabci kadai ba.
Misali :
"ياأيها الذين آمنوا أنفقوا من طيبات ما كسبتم ومما أخرجنا لكم من الأرض ولا تَيَمَّمُوا الخبيث منه تنفقون..." سورة البقرة: 267
Ma’ana : “Yaku wadanda suka yi imani ku ciyar daga dadadan abinda kuka tsiwurwuta da kuma abinda muka fitar muku daga kasa, kada ku nufaci mummuna kuna ciyarwa daga gare shi…” (Surtatul bakara. 267)
Don haka: a harshen larabci idan aka ce “tayammama fulaanun” a na nufin “wane ya tafi, ko ya nufi…” Wannan itace ma’anarta a harshen larabci, amma shari’a ta zo ta dauke wancar ma’anar ta larabci ta mayar da ita wata ma’ana ta daban, shi ne; “yin amfani da kasa a madadin ruwa domin rashin ruwa, ko kuma idan ba za’a iya amfani da rowan ba”. Wannanita ce taimama a shari’ar musulunci. to anan kalmar taimama a larbace ta bada ma’ana ta daban, kuma a shari’ance ma ta bada wata ma’anar ta dabna.
Wani misalign : Kalmar : “Assalatu” wato sallah a cikin harshen larabci tana nufin addu’a kamar yadda Alkur’ani mai girma ya tabbatar, inda Allah (S.W.T) yake cewa:
خُذْ من أموالهم صدقة تطهرهم وتزكيهم بها وصل عليه إن صلاتك سكنٌ لهم والله سميع عليم* سورة التوبة: 103
Ma’ana “Ka karbi sadaka daga dukiyoyinsu ka tsarkake su da ita, kuma ka yi musu addu’a lallai addu’arka nutsuwa ce a gare su, kuma Allah mai ji ne kuma masani” (Suratul Taubah 103).
Ka ga ma’anar “Sallah” a cikin wannan aya tana nufin addu’a ba ma’anar sallah a shari’ah ba domin ita sallah shari’ah ta sanya mata lokuta sannan sabanin addu’a ita bata da wani lokaci da aka iyakance mata. Amma idan muka koma zuwa ga fadin Allah (S.W.T.).
"وأقيموا الصلاة.." سورة البقرة: 43
Ma’ana: “Ku tsayar da sallah” (Surtaul Bakara 43)
Da fadin Allah (S.W.T.)
"أقم الصلاة لِدُلُوكِ الشمس إلى غسق الليل وقورآن الفجر إنّ قرآن الفجر كان مشهودا" سورة الإسراء: 78
Ma’ana: “Ka tsayar da sallah a yayin da rana ta karkata zuwa lokacin duhun dare da kuma sallar alfijir, domin sallar alfijir ta kasance abar halatta ce (na Mala’iku)” (Suratul Isra’i: 78)
Sai shari’ah ta baiwa lafazin “sallah” wata ma’ana sabuwa sabanin ma’anarta ta harshen larabci, sai ya zama sallah a shari’ance itace: “wata ibada ma’abociyar lokaci sannane, wadda ta kunshi ruku’u da sujjada da karatun Alkur’ani da tasbihi da addu’a da tahiya, ana bude tad a kabbara, a rufe tad a sallama.” Ka ga wannan wata bakuwar ma’ana ce shari’ah ta zo da ita, wadda larabawa bas u san tab a a lokacin jahiliyarsu, duk da cewa harshen da aka saukar da Alkur’ani da shi harshensu ne.
Haka nan: kalmar “Zakka” a larabci tana nufin “tsarki” ko “hauhawar abu” amma a shari’ah tana nufin wani yanki sannane na dukiya sanniya da ake bayar da shi ga wasu mutane sanannu. Allah ya ce:
"قد أفلح من زكّاها وقد خاب من دسَّاها" سورة الشمس: 9-10
Ma’ana “Hakika wanda ya tsarkaketa (wato zuciya) ya rabauta, kuma hakika wanda ya turbude ta (da aikin sabo) ya tabe. (Suratul Shams: 9-10).
Zakka a wannan aya tana nufin “tsarki” ba zakka irin ta shari’ah ba, domin ita zuciya ba a fitar da zakkarta, sia da a tsarkaketa a wanke ta daga dattin shirka zuwa ga hasken tauhidi, kuma daga dattin bidi’a zuwa ga hasken sunnah, daga hassada zuwa ga rashin hassada da kaskantar da kai da makamnatansu.
Haka nan idan ka dauki kalmar “Hadisi” da ta zo a wadancan ayoyi da suke kafa hujja da su, za ka ga a larabci kalmar “Hadisi” tana nufn sabon abu, amma a shari’ance ma’anar kalmar Hadisi tana nufin. “Abinda aka jingina wa Annabi (S.A.W.) na Magana ko aiki ko abinda aka yi a gabansa bai hana ba.”Wanna shine ma’anar Hadisi a shari’ance. Kamar yadda Allah (SWT) Yace:
"فبأي حديث بعده يؤمنون"
Ma’ana : “Da wane hadisi ne bayana suke yin imani”
Da fadin Allah (SWT)
"فبأي حديث بعد الله وآياته يؤمنون"
Ma’ana : Da wane hadisi ne bayan Allah da ayoyinsa suke yin imani”
Mai karatu ga wata ‘yar tambaya don Allah me ake nufi da kalmar Hadisi a wadannan ayoyi? Shin ma’anarta ta larabci ake nufi? Ko ma’anarta ta shari’ah? Wannan shine abinda mutane ya kamata su gane.
Abinda kalmar Hadisi take nufi a cikin wadannan ayoyi shine ma’anarta ta larabci, ma’ana: “Da wane sabon abu ne za kuyi imani bayan Alkur’ani” sabon abu kuwa shine abinda ba Alkur’ani ba, kuma ba hadisi ba, domin idan mutum yayi imani da Alkur’ani to, imaninsa da Alkur’ani zai tilasta masa yin imani da hadisan Manzon Allah (S.A.W.), don haka da zarar mutum ya watsar da Alkur’ani da Hadisi to ya zama yayi imani da sabon abu kenan wanda shine ma’anar kalmar Hadisi a larabce ba hadisi a shari’ance ba, wanda wadancan ayoyi suna hana mutum yin imani da hadisis ne a larabce, (wato yin imani da wani abu sabo dab a Alkur’ani ko hadisan Annabi (S.A.W.) ba, ba suna nufin hadisi a shari’ance ba, domin hadisi a shari’ance ayoyin Alkur’ani sun yi kira da cewa mutum yayi imani da shi.
2. Dalilinsu na biyu: wajan bin Alkur’ani kadai ba tare da hadisai ba, shine fadin Allah (SWT)
"أولم يكفهم أنا أنزلنا عليك الكتاب يتلى عليهم إن في ذلك لرحمة وذكرى لقوم يؤمنون" سورة العنكبوت: 51
Ma’ana “shin bai ishe su bane cewa lallai mum un saukar da littafi a gareka ana karanta shi a garesu lallai a cikin wannan akwai rahma da wa’azi ga mutane masu imani.” (Suratul Ankabut 51).
Da fadin Allah (SWT)
..."ونزلنا عليك الكتاب تبينًا لكل شيء وهدى ورحمةً وبشرى للمسلمين" سورة النحل: 89
Ma’ana “Mun saukar maka da littafi domin bayani ga dukkan komai kuma (domin) shiriya da raham da albishir ga musulmai (Suratul Nahl: 89)
Su a fahimtarsu wadannan ayoyi suna nuna a bi Alkur’ani kadai, kuma shi kadai Allah (SWT) ya saukar, ya kuma ce a bi shi!!!
Anan amsar itace : duk wanda yayi ikirarin wadannan ayoyida cewar Alkur’ani kaai za’a yi imani da shi banda hadisai, sai muce. Kololuwar abinda wadannan ayoyi suke nunawa shine abi Alkur’ani, amma ai basu kore abi hadisai ba, domin idan kace sun kore abi hadisai, mu kuma muna da wasu ayoyin wadanda suka nuna a bi hadisai kuam a bi Manzon Allah (S.A.W.), sau da kafa cikin abinda ya umarcemu da kuma wanda ya hanemu, kuma duk a cikin Alkur’ani suke. Ga kadan daga cikinsu, Allah (SWT) yana cewa:
..."وما آتاكم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا واتقوا الله إنّ الله شديد العقاب" سورة الحشر: 7
Ma’ana : “Duk abinda Manzon nan ya zo muku da shi ku rike shi, abinda kuma ya hane ku to ku hanu kuji tsoron Allah lallai Allah mai tsananin ukuba ne” (Suratul hashri: 7)
Wannan aya ta cikin Alkur’ani mai girma tana nuna kenan duk abinda Annabi (S.A.W.) ya zo da shi na aiki ko Magana wajibi ne mu bi shi akan wannan aikin ko maganar, kamar yada yake wajibi ne mu bar duk abinda ya hana mu.
A wani wurin Allah (SWT) tsoratarwa ya yi akan saba wa Manzon Allah (SAW) inda yake cewa:
"فليحذر الذين يخالفون عن أمره أن تصيبهم فتنة أو يصيبهم عذابٌ أليم" سورة النور: 63
Ma’ana : “To, wadanda suke sabawa daga umarninsa (wato Manzon Allah) su kiyayi kansu daga wata fitina ta same su, ko kuma wata azaba mai radadi ta same su” (Suratun Nuur 63)
Kenan a wadannan ayoyi guda biyu ana maganar hadisai ne kadai, ba’a kawo maganar Alkur’ani ba.
A wani wurin ma Allah (SWT) cewa ya yi :
"فلا وربك لايؤمنون حتى يحكموك فيما شجر بينهم ثم لا يجدوا في أنفسهم حرجا مما قضيت ويسلموا تسليما" سورة النساء: 65
Ma’ana : “A aha, ina rantsuwa da Ubangijinka cewa ba za su zama masu imani ba, har sai sun sanya ka mai hukunci a cikin abinda ya faru a tsakaninsu, sannan kuma kada su samu wani kunci a cikin zukatansu daga abinda ka hukunta, sannan su mika wyua (gareka) (Suratul Nisa’i: 65)
A wannan aya ma Allah (SWT) yana nuna cewa a bi Hadisan Annabi kadai, har ma yak ore imani ga wanda bai yarda da hukuncin Manzon Allah (S.A.W) ba.
A wani wurin Allah (SWT) cewa ya yi.
"وما أرسلنا من رسول إلا ليطاع بإذن الله ولو أنهم إذْ ظلموا أنفسهم جاءوك فاسغفروا الله واستغفر لهم الرسول لوجدوا الله توابًا رحيما"
سورة النساء: 64
Ma’ana : “Bamu aiko wani Manzo ba face domin a yi masa biyayya da izinin Allah, kuma da dais u a lokacin da suka zalunci kansu sun zo maka sannan suka nemi gafarar Allah kuma Manzon Allah ya nema musu gafara, hakika da sun samu Allah mai karban tuba ne mai jinkai” (Suratul Nisa’I 64)
A wannan ayar ma Allah (SWT) yana nuna cewa ba a turo wani Manzo ba sai don a bi shi da izinin Allah. To anan idan mutum yana son kansa da zama lafiya da rashin fadawa cikin dirkaniya da halaka, sai ya fahimci cewa ayoyin da suka ce a bi ALkur’ani ba kishiyoyin wadannan ayoyi ban e wadanda suka ce a bi Hadisai, don haka sai a hada su duka biyun a yi aiki da su, wato a bi Alkur’ani da hadisai, sai wannan fahimta ta mayar damu zuwa fadin Allah (SWT):
"من يطع الرسول فقد أطاع الله ومن تولى فما أرسلناك عليهم حفيظا"
سورة النساء: 80
Ma’ana : “Duk wanda ya I biyayya ga Manzon Allah to, hakika ya yi biyayya ga Allah ne (wato ya bi ALkur’ani da hadisi) kuma wanda ya juya baya to bamu aiko ka domin kazama mai kiyayewa a gareshi ba. (Suratul Nisa’I 80).
Da fadin Allah (SWT):
"ومن يطع الله والرسول فأولئك مع الذين أنعم الله عليهم"
سورة النساء: 69
Ma’ana : “Duk wadanda suka yi biyayya ga Allah da Manzonsa to wadannan suna tare da wadanda Allah yayi musu ni’ima…. (Suratun Nisa’I 69)
Don haka, idan mutum ya hada ayoyin farko wadanda suka nuna a bi Alkur’ani da kuma wadanda suka nuna a bi hadisai wato ayoyin na biyu kenan, sai ya sami kyakkawar fahimtar bin Allah da Manzonsa, wato Alkur’ani da Hadisai, kuma ya kansace babu tufka da warwara a cikin fahimtarsa, domin ayoyin Alkur’ani basa cin karo da juna, sai dai su gaskata junansu.
Amma idan mutum ya dauki ayoyin farko, ya rife Alkur’ani kafai ya watsar da Hadisai, to, yaya zai yi da sauran ayoyin da suka ce a bi Hadisai kadai basu yi maganar Alkur’ani ba.
Idan kuma mutum ya dauki ayoyin da suka ce a bi Hadisai kadai, to, yaya zai yi da sauran ayoyin da suka ce a bi Alkur’ani? Ka ga dole a samu tufka da warwara, kuma kafirce wa aya daya kamar kafirce wa dukkan ayoyi ne. don haka imanin mutum da Alkur’ani ba zai yi amfani ba idan ya kafirce wa aya daya daga cikinsa, ko da yayi imani da sauran.
Haka imani da dukkan Alkur’ani ba zai yiwu ba idan mutum ya kafirce wa Hadisai. Allah (SWT) Ya riga ya hukunta a cikin Alkur’ani cewa rike wani sashi na Alkur’ani da barin wani sashi shi ne asalin kafirci. Inda yake cewa:
"إنّ الذين يكفرون بالله ورسوله ويريدون أنْ يفرقوا بين الله ورسله ويقولون نؤمن ببعض ونكفرُ ببعض ويريدون أن يتخذوا بين ذلك سبيلا* أولئك هم الكافرون حقًا وأعتدنا للكفرين عذابا مهينًا"
سورة النساء: 150-151
Ma’ana : “Lalle ne wadanda suke kafirce wa Allah da Manzanninsa, kiuma suna nufin su rarrabe tsakanin Allah da Manzanninsa, sannan suna cewa mun yi imani da wani sashi (na Manzanni) kuma mun kafirce wa wani sashi, kuma suna nufin su riki wata hanya a tsakanin haka, hakika wadannan sun e kafirai na hakika, (cikakku) kuma mun yi tattalin azabar wulakanci ga kafirai” (Suratun Nisa’I 150 – 151)
Saboda haka, idan mutum yana son ya fahinmci Alkur’ani to yayi kokari ya fahimce shi gaba daya, kada ya fahimce shi rabi da rabi.
Da wannan bayani ne zamu gane cewa duk wanda yake da akidar ‘yan tatsine ko kala-kato ko Alkur’aniyyun za a same shi yana cikin dayan biyu, ko dai a same shi kasurgtumin jahili, ko kuma yana da sani na wani yanki na ilimin book zalla wanda ba a hada shi da tarbiyyar addinin musulunci ba, a a maimakon ya sassauto ya ajiye girmankansa da jahilci ya koyi ilimin addini a wurin wadanda suka karance shi, sai ya ki, sai dai ya koyi addini da hankalinsa. Allah yak are mu.
3. Yana daga cikin hujjojinsu cewa: Littafin Allah ya ishe mu, saboda ya yi bayanin komai dangane da al’amuran wannan addini, don haka musulmai bas a bukatar wani hadisi ko wata sunnah wajen fahimtar addini.
Amsa akan wannan : Babu sabani kan cewa Alkur’ani ya tattaro dukkan tushen addini gaba daya, ya yi kuma nuni zuwa ga wasu abubuwa a dunkule. Amma cewar Alkur’ani ya yi bayanin komai babba da karami filla-filla, to wannan Magana ce da take nuna jahilcinsu a fili, saboda hakikanin abinda ke cikin Alkur’ani yana karyata wannan Magana, domin da gaskiya ne da mun ga addinin raka’o’in sallah a cikin Alkur’ani, dam un ga nisabin zakka a cikinsa, dam un ga adadin dawafi a cikinsa da makamantansu. Saboda haka maganganun Annabi (SAW) da ayyukansa (wato hadisai) fassara ce da bayani na Alkur’ani, dole said a su za’a fahimce shi.
Kuma da Alkur’ani ya yi bayanin komai babba da karami daki-daki da Allah (SWT) bai yi umarni ga Manzonsa ba da ya yi bayanin Alkur’anin, haka kuma da bai umarce mud a yin biyayya ga Manzonsa ba. Kamar yadda yake cewa :
"وأنزلنا إليك الذكر لتبين للناس ما نزل إليهم ولعلهم يتفكرون"
سورة النحل: 44
Ma’ana : “Kuma mun saukar da Anbato (Alkur’ani) zuwa gare ka domin ka yi wa mutane bayanin abinda aka saukar zuwa gare su saboda suyi tunani”
Da fadin Allah cewa:
"... وما آتاكم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا واتقوا الله إنّ الله شديد العقاب" سورة الحشر: 7
Ma’ana : “Kuma duk abinda Manzon Allah ya zo muku da shi to ku yi riko shi, kuma abinda ya hane ku to ku hanu kuma kuji tsoron Allah, lallai Allah mai tsananin ukuba ne”. (Suratul Hashr: 7)
4. Daga cikin hujjojin akwai: Inkarin samuwar wani wahayi wanda ba Alkur’ni ba, don haka su a wurinsu hadisai ba wahayi ba ne, maganganu ne kawai aka kirkiro aka danganasu ga manzon Allah (S .A.W).
Amsa : Alal hakika wannan Magana ta ci karo da fadin Allah (SWT) inda yake cewa:
"وما ينطق عن الهوى* إنْ هو إلاّ وحي يوحى" سورة النجم: 3-4
Ma’ana : “Ba ya Magana akan son zuciya, duk abinda zai fada wahayi ne da aka yi masa”.(Suratul Najm 3.4)
A wadannan ayoyi Allah (SWT) yana tabbatar mana cewa manzonsa ba ya fadin Magana akan abinda ya ga dama sai dai duk abinda ya fada wahayi ne daga wurin Allah. Saboda haka Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) suma wahayi ne daga Allah (SWT)
Awata ayar ma Allah cewa ya yi:
"إنا نحن نزلنا الذكر وإنا له لحافظون" سورة الحجر: 9
Ma’ana : “Hakika mune muka saukar da Ambato (wato Alkur’ani) kuma mune zamukiyaye shi”.(Suratul Hijr: 9)
Wannan aya tana tabbatar mana cewa Allah (S.W.T) ya yi alkawarin kare Alkur’ani mai girma,kuma yana daga cikin kare martabar Alkur’ani mai girma kare Hadisan Manzon Allah (SAW), domin suna yin bayani abinda Alkur’ani ya kunsa ne, don haka karesu da kiyayesu yana daga cikin abinda Allah (SWT) ya yi alkawari a cikin wannan aya mai albarka.
A dalilin haka, Allah ya samara da matamai wadanda suka bad a rayuwarsu wajen kare Hadisan Manzon Allah (S.A.W) da tace wadanda suka tabbata zuwa gareshi (na gaskiya) da kuma wanda aka jingina masa (na karya), saboda haka babu wata karya da aka dangana wa manzon Allah (S.A.W.) face sunyi bayaninta filla – filla ga al’ummar musulmi.
5. Yana daga cikin hujjojinsu cewa: Bin Hadisai hade da Alkur’ani shirka ne a cikin hukunci suna masu dogaro da fadin Allah (SWT) inda yake cewa:
"... إنِ الحكم إلاّ لله ..." سورة الأنعام: 57
Ma’ana : “Hukunci a hannun Allah yake shi kadai….” (Suratul An’am: 57)
Amsa : dukkan abinda Manzon Allah (S.A.W.) ya yi ko ya fada, ko ya tabbatar da shi, to daga wurin Allah (SWT) ya samo shi, kuma umarni ne daga wajen Allah, sannan ba yadda mutum zai zama cikakken mumini sai idan ya yi imani da Manzon Allah (S.A.W.), don haka bin Manzon Allah (S.A.W.) bin Allah ne babu wani shirka a cikin hakan. Kumar yadda ayoyin da suka gabata suka nuna.
Wadannan sune mafi karfin hujjojin da masu akidar ‘yan tatsine ko ‘yan kala – kato ko Alkur’niyyun suke dogaro da su wajen kin yarda ko aiki da Hadisan Manzon Allah (S.A.W.), wanda kuma da wannan dan takaitaccen bayani ya tabbatar mana cewa abinda suke kai bata ne. allah ya kare mu daga bacewa bayan shiriya.
HADARIN SABA WA SUNNAR MANZON ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wa Sallam)
Babu shakka saba wa Manzon Allah (S.A.W.) yana da matukar badari ga duk wanda ya samu kanshi a cikinsa. Daga cikin irin wadannan munanan hadurra.
1. Komawa kafirci bayan musulunci, wannan kuwa ko shakka babu duk wanda ya sanya kin abinda manzon Allah (S.A.W.) ya zo da shi, da inkarin ingantattun hadisansa a gaba, to ya kama hanyan kafirci, kuma in ba Allah ya nufe shi da tuba ba, to zai mutu ba imani. Allah ya kiyaye mu, amin.
2. Gamuwa da azaba da ukuba tun a nan duniya kafin lahira. An karbo hadisi daga Salamatu bin Al’akwa’I Allah ya kara yarda a g aer shi yace:
"إن رجلا أكل عند رسول الله – صلى الله عليه وسلم – بشماله فقال: {كل بيمينك}. قال لا أستطيع قال: {لا استطعت}. ما منعه إلاّ الكبر. قال فما رفعها إلى فيه" رواه مسلم
Ma’ana : “Wani mutum yana cin abinci da hannun hagu a gurin Manzon Allah (S.A.W.) sai Manzon Allah yace: “Ka cid a hannun dama”, sai yace: b azan iya ba, sami Manzon Allah yace: “Kada ka iya din” Ba abinda ya hana shi sai girman kai, don haka bai kara iya daga hannunsa ba zuwa bakinsa” (wato hannun ya shanye). (Muslim ya ruwaito).
Haka nan sarki kisra na kasar Farisa lokacin da Manzon Allah ya aika masa wasika yana kiransa zuwa ga addinin musulunci, sai ya ga wasikar, wannan ya sa Manzon Allah ya yi addu’a yace
"اللهم مزق ملكه" اخرجه بن سعد
Ma’ana: “Ya Allah ka yaga mulkinsa”. (Ibnu Sa’ad ne ya fitar da shi)
Wannan ya sa Allah ya keta mulkinsa ya hallaka shi.
Wadannan kadan kenan daga cikin irin abinda Allah yake azabtar da wanda duk yake saba wa Manzon Allah (S.A.W) da kin yin abinda ya zo da shi, don girman kai da nuna isa.
3. Gamuwa da dimuwa da dirkaniya da rashin makama wajan addini, domin kuwa an bar tushe, don haka za ka ga irin masu wannan mummnar akida a karshen lamarinsu suna daina addini, domin sun rasa abin kamawa.
4. Mummunan karshe, saboda Allah bay a kyale duk wanda ya saba wa umarninsa.
5. Wulakantawa a duniya da lahira, a nan duniya Allah Ya kan tozarta su, ya kuma bayyana batar su ga mutane a fili su gane su, sai su rika yi musu munanan addu’o’i. A lahira kuma su gamu da azba mai tsanani. Allah ya tseratar dam u daga irin wannan hallaka.
Wadannan kadan kenan daga cikin hadarin kin sunnar Manzon Allah (S.A.W.) da saba mata.
RUFEWA
A karshe mu sani ya ‘yan uwa musulmi bamu, da wata hanyar tsira duniya da lahira sai ta bin abinda Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi. Mu ji tsoron Allah, mu koyi addini a wurin malami na Allah, na gaskiya, don mu bauta wa Allah (SWT) irin bautar da yake so kuma ya yarda da ita, wannan ne kadai zai sa mu rabauta a duniya da lahira.
Sannan wajibi ne mu nisanci dukkan wata bidi’a, domin kuwa bidi’a bat ace, kuma hanya ce ta zuwa wuta. Don haka duk ibadar da Manzon Allah (S.A.W) da ita ba, kuma sahabbai basu bauta wa Allah da ita ba, to ba ibada bace, mu nisance ta, mu koma kan littafin Allah da sunnar Annabinsa Muhammad (S.A.W) a bisa hasken fahimtar magabantanmu na kwarai wato sahabbai da tabi’ai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranan sakamako.
BY SHEIKH JA’AFAR MAHMUD ADAM
No comments:
Post a Comment