GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINSUNNAH-BLOGSPOT.BLOGSPOT.COM


WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA LACCOCI DAGA MALAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI; {mumbarinsunnah@gmail.com]

Thursday 20 September 2012

SHARRIN HARSHE {4}


RATSUWA DA WANIN ALLAH
Rantsuwa da wanin Allah yana daga cikin laifuffukan da harshe yake, wajibi a kan musulmi day a kare harshensa daga wannan mummunan laifi, saboda rantsuwa tana cikin nau’in gimamawar dab a wanda za’a yi wa irinta in ba Allah mai girma da buwaya ba, bai halatta rantsuwa da wani mahaluki ba kowa ye kuwa. Annabi (S.A.W.) ya ce:
"إن الله ينهاكم أن تحلفوا بآبائكم, من كان حالفا فليحلف بالله أو ليصمت". رواه البخاري.
“Allah ya hanaku ku dinga rantsuwa da iyayenku, wanda zai rantse ya rantse da Allah ko ya yi shiru”. Bukhari.
Haka nan bai halatta rantsuwa da Annabi ba, ko Ka’abah, ko amana, ko da kan wane ko da girman ko wani waliyyi ko da kabarinsa, saboda fadin Annabi (S.A.W.) :
"من حلف بغير الله فقد أشرك". أحمد
“Duk wanda ya rantse da wanin Allah to ya yi shirka: (Ahmad)
Duk wanda ya sami kansa a cikin laifin rantsuwa da wanin Allah, to ya gaggauta tuba ga Allah Madaukakin Sarki, ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah” saboda fadin Annabi (S.A.W.) :
"من حلف فقال في حلفه: باللات والعزى, فليقل: لا إله إلا الله". رواه البخاري
“Wanda ya rantse da Lata da Uzza a rantsuwarsa, to ya ce: La’ilaha Illallah” Bukhari.

A GUJI FADIN WADANNAN LAFAZAI
Ya dan uwa musulmi, musulunci ya kwadaitar kan mayar da dukkan al’amurra zuwa ga yarda ga Allah shi kadai da tsarin Ubangiji da hukuncinsa, har kowane musulmi sai ya zama yana da cikakkiyar masaniya a kan cewa Allah daya ne, kuma shi ne mai jujjuya al’amura, mai tsara duk abubuwan da suke faruwa, ba wanda yake da hannu a cikin duk wadannan abubuwa, saboda haka Annabi (S.A.W.) ya ce:
"لاتقولوا: ما شاء الله وشاء فلان, ولكن قولوا: ماشاء الله ثم شاء فلان" أحمد وأبو داود.
“Ka da ku ce: In Allah da wane sun so, sai dai ku ce: In Allah ya so, sannan wane ya so”. (Ahmad da Abu Dawud)   
Wannan yana nuna cewa son wani ga wani abu ko yardarsa ga wani abu tana karkashin yardar Ubangiji ne, bawa bashi da yarda tasa ta kansa. Yana daga cikin wannan fadin Annabi (S.A.W.):
"احرص على ما ينفعك, واستعن بالله, ولا تعجز, وإن أصابك شىء فلا تقل: لو أني فعلت كذا كان كذا وكذا, ولكن قل: قدر الله وما شاء فعل, فإن لو تفتح عمل الشيطان". (مسلم)
“Ka yi kwadayi duk abin da zai amfane ka, ka nemi taimakon Allah, ka da ka gajiya, idan wani abu ya same ka, kada ka ce: da na yi kaza da kaza da kaza ya faru, sai dai ka ce: Haka Allah ya kaddara, yadda ya so haka zai yi, domin “da na yi kaza” tana bude aikin shaidan” (Muslim)

KURARUWA MUTUWA
Yak e ‘yar uwa musulma, yin kururuwa ga mamaci yana daga laifukan da harshe yake, kuma musulunci ya yi kwakkwaran hani ga yinsa, domin yin haka yana cin karo da yin hakuri da yarda da hukuncin Allah, saboda haak Annabi (S.A.W.) ya kirga rashin kururuwa yayin mutuwa a cikin sharadan mubaya’a
Annabi (S.A.W.) ya siffanta yi kuka yayin mutuwa da cewa yana cikin al’amurran jahiliyya sannan ya ce:
"التائحة إذا لم تتب قبل موتها, تقام يوم القيامة وعليها سر بال من قطران ودرع من جزب". (مسلم).
“Mai yin kururuwar mutuwa idan bata tuba kafin ta mutu ba, za ta tashi ranar alkiyama tana sanye da rigar narkakken karfe, da zanin tartsatsin wuta” (Muslim)
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"ليس منا من ضرب الخدود وشق الجيوب ودعا بدعوى الجاهلية". متفق عليه.
“Duk wanda ya mari kuncinsa, ko ya kekketa rigarsa ko ya yi ihi irin ihun Jahiliyya (lokacin mutuwa) to ba shi daga cikinmu”. Bukhari da Muslim.
Lallai Annabi (S.A.W.) ya tsinewa masu yakusar fuskokinsu ko masu yayyaga rigunansu, da masu ihun na shiga ukuna lalace (Ibn Majah.)

ROKO BA TARE DA BUKATA BA
Ya dan uwa musulmi, mutanen kirki suna ganin kaskanci ne da tozarta kai rokon wani ba Allah ba, saboda haka su ba su komawa wajen kowa sai Allah.
Sauban Allah ya kara yarda da shi – ya kasance daga cikin irin wadannan mutanen, domin ya ji Annabi (S.A.W.) yan cewa:
"من يتقبل لي بواحدة أتقبل له بالجنة؟ قال ثوبان أنا فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "لا تسأل النسا شيئًا. فكان ثوبان يقع سوطه وهو راكب فلا يقول لأحد ناولنيه حتى ينـزل فيأخذه". (أحمد وأبو داود)
“Waye zai min alkawarin riko da abu daya, ni kuma zan masa alkawarin Aljanna? Sai Sauban ya ce: Ni zan yi. Annabi (S.A.W.) ya ce: ka da ka tambayi mutane komai”. Daga ran nan Sauban bay a tambayar mutane komai, ko da bulalarsa ta fado yana kan doki to sai ya sauko ya dauka ba zai ce da wani, miko min bulalata ba. (Ahmad da Abu Dawud).

A yau da yawa daga cikin mutane bas u damu da wannan al’amarin ba, za ka gansu suna rokon mutane ko da suna da abin da zai ishe su, suna yin hakan ne kawai saboda kwadayi, Annabi (S.A.W.) ya gargadi masu irn wannan hali da wuta, ya ce:
"من سأل الناس أموالهم فإنما يسأل جمرا فليستقل أو ليستكثر". (مسلم)
“Duk wanda yake rokar mutane dukiyoyinsu don ya tara to yana rokar garwashin wuta ne, ruwansa ne ya daina ko ya ci gaba” (Muslim) Annabi (S.A.W.) ya ce:
"من سأل وله ما يغنيه جاء يوم القيامة خدوشا أو كدوشا في وجهه". (أحمد وصححه الألباني).
“Wanda yak e rokar mutane alhali yana da abin da zai ishe shi, zai zo ranar alkiyama fuskarsa a kurje” (Ahmad).

KA MALLAKI HARSHENKA
Ya dan uwa musulmi! Wani mutum ya zo wurin Salman – Allah ya kara yarda da shi – sai Salman ya ce: Ya baban Abdullahi yi min wasiyya? Sai Salman ya ce: Ka da ka yi Magana. Sai ya ce: ai ba yadda za a yi wanda yake rayuwa a cikin mutane kuma baya Magana. Sai Salman ya ce: To idan ka yi Magana ka fadi gaskiya ko ka yi shiru. Sai ya ce: kara min. sai Salman ya ce: Ka da ka yi fushi. Sai ya ce: Ka umarce ni kada na yi fushi. Amman wani lokacin fushin yakan fi karfina. Sai ya ce: idan ka yi fushin to ka mallaki harshenka da hannunka.

JIFAN KAMAMMUN MATA MUMINAI
Munafikai da makiyan musulunci suna kokarin bata muminai kamammu mata, suna lika musu munanan tuhume – tuhume, suna jifansu da abin da zai taba mutuncinsu, ta hanyar karya, kage, shaidar zur, har suka hana wasu matan lazimtar hijab, da riko da tsarki da kamewa, domin sukan irin wadannan matan yana taimaka wa wasu matan wajen ci gaba da barna da bata.
Dalilai daga Alkur’ani da hadisan Annabi masu yawa sun yi Magana kan haramcin jifan muminai mata, kamammu:
{إن الذين يرمون المحصنت الغفلت المؤمنت لعنوا في الدنيا والأخرة ولهم عذاب عظيم} النور: 22
“Wadanda suke jifan kamammu wadanda bas u damu da kowa ba, an la’ance su a duniya da lahira, kuma azaba mai girma ta tabbata a gare su” (Nur: 23).
An karbo daga Abu Huraira Annabi (S.A.W.) ya ce:
"اجتنبوا السبع الموبقات: وذكر منهن قذف المحصنات المؤمنات الغافلات".
“Ku guji manyan zunubai masu hallakarwa guda bakwai. Daga cikinsu akwai: Jifan kamammun mata muminai wadanda ba su da mu da kowa” (Bukhari da Muslim)
Jifan kamammun mata muminai yana daga cikin laifuka masu hallakarwa, in dai mai yinsu bai tuba bay a koma hanyar tsira da daidaituwa.
Ka da ka gaskata abubuwan da makiya musulunci suke yadawa (Yahudadawa da Nasara da Munafukai) akan ‘yan uwa muminai mata,  wajibi mutuncin mata muminai, kada ka bar wadannan lalatattun mutane su ci gaba da yada munanan labarai wadanda ba wanda yake amfanuwa daga su sai makiyan musulunci. Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{والمؤمنون والمؤمنت بعضهم أولياء بعض يأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر ويقيمون الصلوة ويؤتون الزكوة ويطيعون الله ورسوله أولئك سيرحمهم الله إن الله عزيز حكيم} التوبة: 71
“Muminai maza da muminai mata, sashinsu yana jibintar lamarin sashi, suna umarni da kyakkyawan aiki, suna hani mummunan aiki, suna tsayar da sallah, suna bad a zakka, suna bin Allah da Manzonsa, wadannan Allah zai musu rahama, lallai Allah mabuwayi ne mai Hikima” (Taubah: 71)

JAYAYYA, MUSU DA NEMAN RIGIMA
Wadannan duk suna cikin laifukan harshe a wannan zamanin, musamman tsakanin ma’abota addini. Annabi (S.A.W.) ya hana yin jayayya. An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W.) ya ce:
"أنا زعيم بيت في ربض الجنة, لمن ترك المراء وإن كان محقا". أبو داود
“Ni ne shugaban wani gida a aljanna na wanda ya bar jayayya ko da kuwa yana da gaskiya”. (Abu Dawud).
Dan Mas’ud –Allah ya kara yarda da shi – ya ce: Kubar jayayya domin ita ba a fahimtar hikimarta, kuma ba a amincewa fitinarta”.
Jayayya ita ce: Suka ga maganar wani don bayyana rauninsa, ba tare da bukatar hakan ba, face neman wulakantar da shi, da nuna fifiko a kansa.
Amma musu shi ma an hana yinsa in dai ba shi da amfani kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{ما ضربه لك إلا جدلا} الزخرف: 58
“Ba su buga maka wani misali ba face don su yi musu da kai” (Zukhruf: 58).
Musu shi ne kokari gajiyar da mutum da nuna rauninsa ta hanyar sukan zancensa, da dagan zancensa, da dagantashi ci baya da jahilci nau’I ne na wulakanci wanda ba ya tabbatar da gaskiya ko bata karya, sai dai ya kara sabbaba riko da barna ga masu riko da ita da kuma kokarin kareta.
Ita kuwa husuma ko neman rigima Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{ومن الناس من يعجبك قوله فى الحياة الدنيا ويشهد الله على ما فى قلبه وهو ألد الخصام} البقرة 204
“Daga cikin mutane akwai wadanda maganarsu za ta birge ka a rayuwar duniya, amma Allah ya san abin da yake cikin zuciyarsa shi ne mafi tsanani neman rigima”
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"أبغض الرجال إلى الألد الخصيم". متفق عليه.
“Mafi kin mutane a wurin Allah shi ne mafi neman rigima” bukhari da Muslim.
Shi ne wadda yake kaiwa matuka wajen neman rigima yakuma yawaita ba tare da yarda da gaskiya bad a rankwafawa da sallamawa ga gaskiyar.

YABO DA TUMSANCI
Yabon da aka hana shi ne wanda ake wuce gonad a iri saboda fadin Annabi (S.A.W.)
"لا تطروني كما أطرت النصارى ابن مريم, إنما أنا عبد, فقولوا: عبد الله رسوله". البخارى
“Ka da ku wuce – gona da iri wajen yabona, kamar yadda Nasara suka yi a kan dan Maryam, kawai ni bawan Allah ne, kuma manzonsa ne”. Bukhari.
Amma yabon abu mai kyau ko aiki mai kyau ga wani mutum to ba zai shiga cikin wanda aka hana ba, mafi kyau ma a yi shi. An karbo daga Abu Bakrata (R.A) cewa: Lallai wani mutum a wajen Manzon Allah (S.A.W.) sai aka yabe shi, sai Annabi (S.A.W.) ya ce: “Kai kayanke wuyan dan uwanka ya yi ta fadan hakan ya ce: Idan dayanku lallai sai ya yabi wani, to ya ce: Ina zatonsa kaza da kaza, ba ma tsarkake wani a wajen Allah”. Bukhari da Muslim.
Wajibi ne a kan kowane musulmi ya fadaka lokacin da yake yabon waninsa, kada ya wuce gonad a iri wajen yabon. Domin hakan zai iya jawo wanda ake yabon ya yaudaru, sai girman kai ya shige shi, har ya halaka.
"إذا المرء لم يمدحه حسن فعاله
                  فمادحه يهذي وإن كان مفصحا
Ma’ana: Idan mutum kyan aikinsa bai yabe shi ba, to duk wand aya yabe shi shirme ya yi ko da yana da fasaha.

HANYAR TSIRA DAGA LAIFUKAN HARSHE
Za ka iya gujewa sharrin harshe ta hanyar:
1.    Tuba zuwa ga Allah. Sharuddan tuba kuwa guda hudu ne:
(a)    ya bar yin wannai aiki kwata – kwata
(b)    Ya yi nadamar aikata wannan aiki
(c)     Ya yi niyyar cewa ba zai sake komawa irin wannan aiki ba har abada.
(d)    Ya hana harshensa yi da mutane ko gulma ko karya, ko kazafi, ko isgilanci da wulakanci, idan ya ji tsoron cutarwa wajen bad a labari to kada ya bayar, kuma wajibi ya yi ta neman gafarar Ubangiji ya yi kokarin yabo wannan mutumin a wuraren day a bata shi.
2.    Ya san munin laifukan harshe, ya san cewa Allah zai iya yin fushi da shi, sakamakon wannan lafin, kuma zai iya jawo masa azabar Allah mai rafadi.
3.    Ya san cewa yin irin wadannan laifuka za su iya rusa ayyukan alherin da ka yi ranar lahira, kuma za su nauyaya ma’aunin zunubanka.
4.    Kada mutum ya zauna a wuraren da ake nikata irin wadannan ayyuka, irinsu yi da muttane gulma, karya waka-zagi, isgilanci, wulakanci, don hada ya taimaka wajen yin barna da samara da kiyayya.
5.    Ya nuna kyamarsa a kan wadanda suke cin mutuncin mutane, suke kuma kirkira masu karya, wannan zai taimaka masa wjaen tserar da harshensa.
6.    Ya damu da aibukan kansa don ka day a shagala da aibukan mutane.
7.    Ya dinga nemarwa ‘yan uwansa musulmi uzuri, ya kuma karbi uzurinsu, domin haka zai sa shi rashin sukansu da yi da su da gulmarsu.
8.    Ya sowa ‘yan uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kamar yadda bay a son mutane su zage shi da harshensu to shi ma kada ya yardarwa waninsa, Annabi (S.A.W.) ya ce: .
"لايؤمن أحدكم حتى يحب لأخيه ما يحب لنفسه" متفق عليه.
9.    Ya dinga yawaita yi wa kansa hisabi domin hakan zai say a gane aibukan kansa, ya tunatar da shi hakkin ‘yan uwansa.
10. Ya yanke hulda da duk abin da zai janyo aikata irin wadannan laifuffuka, kamar yawan fushi, hassada, girman kai, alfahari, jiji da kai, tsarkake kai, neman taimakon wanin Allah, ya yi kokarin magancewa kansa wadannan cututtuka wanda harshe yake yi.

Muna rokon Allah Madukakin Sarki ya gyara mana ayyukanmu, ya kuma tsarkake zukatanmu da harsunan mu, ya sanya mu cikin masu soyayya sbaoda girmansa, wadna yake sa su a cikin inuwarsa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa. Karshen addu’ar godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Allah ya yi salati da albarka ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa, ya kuma kara amince gare su.    

No comments:

Post a Comment