WAJABCIN KIYAYE HARSHE
Allah madaukakin sarki ya ce
{ما يلفظ من قولٍ إلا لديه رقيب عتيد} ق: 18
“Babu wata magana da zai furta face akwai mai tsaro (a tare da shi) halartacce”. (Daf. 18)
Shahararren malamin tafsirin nan, Malam Ibnu Kasir ya fada dangane da wannan aya: Babu wata kalma dad an Adam zai fada face sai an sa mata wanda zai rubuta ta ya ajiye masa ita. Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:
{وإن عليكم لحفظين} الإنفطار: 10
“Lallai akwai masu kiyaye duk abin da kuka yi masu daraja, marubuta, suna sanin duk abin da kuke aikatawa”. (Infidar: 10-11)
Lallai ya kamata ga duk mai hankali ya kiyaye harshensa ta hanyar tsarkake shi, ka day a yi wata Magana sai idan akwai amfani a ciki, wannan kuwa ba abu ne mai sauki ba, yana bukatar jajircewa da tilasta kai, har sai ya saba da fadar alherin kawai, kuma hakan ta zama dabi’arsa, ya kuma guji fadar sharri tare da kin hakan a zuciyarsa. Muhammad dan Wasi’u ya fadawa Malik dan Dinar cewa: Ya kai baban yahaya, ka sani cewa; kiyaye harshe ya fi wahala a kan kiyaye dinare (Kudi).
Abdullahi dan Abbas – Allah ya kara masa yarda ya gayawa harshensa cewa: “kai harshe! Ka fadi alheri sai rabauta, ko ka yi shiru, kada ka fada sharri, sai ka kubuta”.
Wasu masu hikima sun ce: harshe shi take bayyana girmansa, da darajarsa, ita ce kuma take nuna kaifin hankalinsa, saboda haka, ka karanta maganrka a kan abu mai kyau kawai, kuma kada ka tsawaita.
Wani mai waken Larabci ya ce:
وزن الكلام إذا نطقت فإنما
يبدي عيوب ذوي العيوب المنطق
Ma’ana : ka auna Magana kafin ka yi, domin Magana ita ce take fito da aibin mai aibi”.
YAUSHE YA KAMATAKA YI MAGANA
Imam Annawawi : Allah ya ji kansa ya bayyana inda ya kamata mutum ya yi Magana, ko ya yi shiru, ya ce: “Ka sani cewa ya wajaba ga kowane cikakken mai hankali ya kiyaye harshensa ga dukkan abin da zai fada, ka day a yi Magana sai a kana bin da yake da amfani, ko da Magana mai amfani, abu mafi kyau shi ne mutum ya kame daga yenta domin sau da yawa yin maganar da ta halarta ta kan ja mutum zuwa ga haram ko abin ki. Wani mai waken Larabci ya ce:
الصمت أزين للفتى من منطق في غير حينه
Ma’ana : Kame harshe ya fi zama ado ga saurayi a kan yawaita Magana, ba a lokacin da ya kamata ka yi ba”.
Imamul Mawardi ya bayyana wasu sharadai guda hudu ya kamata mutum ya cika su kafinya yi Magana, idan wadannan sharadaiba su cika ba sai ya yi shiru:
Sharadan su ne:
1. Ya kasance maganar akwai wani abu kwakkwaran dalili da zai sa a yi maganar, ko dai don sanar da wani amfani ko kore wani sharri.
2. Ya fadi alheri a wurin day a dace, ya kuma iya gamsar da abokan maganar.
3. Ya takaita gwargwadon bukatarsa ga maganar.
4. Ya zabi kalomin da zai yi amfani da su
Wani malami ya ce
احفظ لسانك أيها الإنسان
لايلدغنك إنه ثـعبان
كم في المقابر من صريع لسانه
كانت تهاب لقاءة لاشجعان
Ma’ana : ya kai mutum, ka kiyayi harshenka domin shi maciji ne, kada ya sare ka, mutane da yawa an kaisu makabarta sakamakon harshensu, irin mutanen da mazaje ke tsoron arangama da su. Imamu Ibnul Kayyim ya yi Magana akan hadarin harshen ya ce: Ka kiyaye duk zantukan da zaka yi, ka da ka fadi wata kalma mara amfani, ka da ka yi Magana sai a kana bin da kake kyautata zaton samun riba a cikinsa ko kuma karuwar addininka, saboda haka idan za ka yi Magana sai ka duba ka gani akwai riba ko wata fa’ida a ciki? Idan babu riba sai ka yi shiru, idan kuwa akwai riba, to sai ka duba ka gani shin akwai wata maganar da zata kubuce maka wadda tafi wacca za ka yi riba? Don ka da ka bata wancan da wanna. Idan kana son ka san abin da yake cikin zuciya, to ka saurari abin da harshe yake fada, domin shi zai nuna maka abin da yake cikin zuciya ko da mai zuciyar bai so ba.
Malam Yahya dan Mu’az ya ce: zuciya kamar tukwane ne da suke tafasa abin da yake cikinsu, harshe shi ne ludayin debo abin da yake cikin tukwanen.
Abu Tamam ya ce:
ومما كانت الحكماء قالت * لسان المرء من تبع الفؤاد
Ma’ana: Yana daga cikin abin da masu hikima suka fada: Harshen mutum yana bin zuciyarsa ne. *Ya kai dan uwa musulmi, ka ji tsoron Allah Madaukakin Sarki a kan kanka, ka kiyaye harshenka daga dukkan abin dab a shi da kyau, ka sani cewa kai abin tambaya ne a gaban Allah a kana bin da duk harshenka ya fada. Allah Madaukaki ya ce:
{يوم تشهد عليهم ألسنتهم وأيديهم وأرجلهم بما كانوا يعملون} النور: 24
“Ranar da harsunansu da hannayensu da kafafuwansu za su ba da shaida akan abin da suke aikatawa” (Nur: 24).
HADISAN ANNABI DA SUKE MAGANA A KAN HATSARIN HARSHE DA WAJABCIN KIYAYESHI
An karbo hadisai daga Annabi (S.A.W.) masu yawan gasket, wadanda suke nuna, hatsarin harshe, suke kuma kira zuwa ga gujewa sharrinsa, da takatsantsan wajen sakinsa ba tare da yi masa linzami ba, daga ciki akwai:
1. Daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda cewa ya ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: “Hakika bawa yana iya magan ba tare day a lura daabin da yake fada ba, sai maganar ta yi masa sanadin shiga wuta, mai zurfi day a fi tsawon abin da ke tsakanin gabas da yamma”. Bukhari da Muslim.
وعن عقبة بن عامر رضى الله عنه قال: قلت يا رسول الله! ما النجاة؟ قال: "امسك عليك لسانك, وليسعك بيتك, وابك على خطيئتك". الترمذي وقال حديث حسن.
2. An karbo daga Ukbatu dan Amir – Allah ya kara masa yarda ya ce: Na ce ya Manzon Allah (S.A.W.) mece ce hanyar tsira? Sai ya ce”: “Ka kiyaye harshenka, ka yi zamanka a gidanka, kuma ka yi kuka sabdoa zunubanka”. Tirmizi ne ya ruwaito shi, y ace: Hadisi ne mai kyau.
وسأل سفيان بن عبد الله رسول الله صلى الله عليه وسلم: عن أخوف ما يخاف عليه. فأخذ النبى صلى الله عليه وسلم بلسان نفسه. ثم قال: هذا" مسلم.
Sufyanu dan Abdullahi ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.) dangane da abin day a fi jiye masa tsoro? Sai Annabi (S.A.W.) ya kama harshensa, sannan ya ce: “Wannan”. Muslim ne ya ruwaito shi.
وسئل النبي صلى الله عليه وسلم عن أكثر ما يدخل النار. فقال: الفم والفرج. رواه الترمذي وقال صحيح غريب وصحح الحاكم.
3. An tambayi Annabi (S.A.W.) akan abin day a fi shigar da mutane wuta. Sai ya ce: “Baki da farji” Tirmizi ne ya ruwaito shi. Ya kuma ce” Hadisi ne ingantacce garibi. Hakim ya inganta Shi
4. Mu’azu dan Jabal – Allah ya kara masa yarda ya tambayi Annabi (S.A.W.) a game da aikin da zai shigar da shi aljanna, ya kuma nesanta shi daga wuta. Sai Annabi (S.A.W.) ya bashi labari a kan ginshikan al’amarin day a yi tambaya a kansa, da tsololuwarsa,sannan sai Annabi (S.A.W.) ya ce: Shin ban a baka larabin abin daya fi wannan ba gaba daya? Sai ya ce: Bani labari ya Manzon Allah. Sai ya kama harshensa, sanna ya ce: Ka rike wanna. Sai Mu’az ya ce: Shin za kama muda abin da muke fada? Sai Annabi (S.A.W.) ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka, ai ba komai yke afkar da mutane taka ko a kan fuskokinsu cikin wuta ba face abubuwan da harsunansu suka girban musu. Ahmad da Tirmizi ne suka ruwaito shi.
5. Annabi (S.A.W.) ya ce:
لاتكثروا الكلام بغير ذكر الله, فإن كثرة الكلام بغير ذكر الله قسوة للقلب, وإن أبعد الناس من الله, القلب القاسي".
“Ka da ku yawaita Magana ba tare da ambaton Allah ba, domin yawan Magana ba tare da ambaton Allah ba, yana kawo kekashewar zuciya, kuma mutum mai kekasasshiyar zuciya ya fi nesa da Allah”.
6. Annabi (S.A.W.) ya ce:
أن جميع أعضاء الإنسان تخاطب اللسان كل صباح, قائلة: اتقوا الله فينا, فإنما نحن بك, فإن استقمت استقمنا, وإن اعوججت اعوججنا" رواه الترمذي وصححه ابن خزيمة.
7. Hakika dukkanin gabobin mutum suna gaya wa harshe kowacce safiya suna cewa: Ka ji tsoron Allah game dam u, hakika muna tare da kai idan ka daidaita, to za mu daidaita, idan kuma ka karkace to muna za mu karkace”. Tirmizine ay ruwaito.
8. Annabi (S.A.W) ya ce:
المسلم من سلم المسلمون من لسانه ويده". متفق عليه.
“Musulmi shi ne wanda musulmi suka kubuta daga hatsarin harshensa, da illar hannunsa”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
9. Annabi (S.A.W.) ya ce:
من كان يؤمن بالله واليوم الآخر, فليقل خيرا أو ليصمت" متفق عليه.
10. Annabi (S.A.W.) ya bad a labari:
قال: عليه الصلاة والسلام: لا يستقيم إيمان عبد حتى يستقيم قلبه, ولا يستقيم قلبه حتى يستقيم لسانه". أحمد.
Hakika masomin imani shi ne daidaituwar harshe, Annabi (S.A.W.) ya ce: Imanin bawa bay a tabbata har sai zuciyarsa ta daidaita, zuciya kuma bat a daidaituwa har sai harshe ya daidaita”. (Ahmad ne ya ruwaito shi).
11. Annabi (S.A.W.) ya da labari cewa:
"أكثر خطايا ابن آدم في لسانه". أخرجه الخطيب وهو في السلسة.
“Mafi yawancin laifukan dan Adam a harshensa ne” (Al Khadib ne ya ruwaito shi).
12. Annabi (S.A.W.) ya ce: "زنا اللسان النطق"
“Zinar harshe shi ne Magana”. Yana nufin ta hanyar zance mara kyau da alfasha da batsa, saboda haka Annabi (S.A.W.) ya hana mace ta siffanta wa jijinta kamanni da sifofin wata mace kai kace gat a yana ganinta, saboda Annabi (S.A.W.) ya ce:
"لاتباشر المرأة المرأة فتنعتها لزوجها كأنه ينظر إليها"
“Kada mace ta kadaita tare da wata macen, ta yadda za ta sifantawa mijinta ita kamar yana kallonta”.
13. Annabi (S.A.W.) ya ba da labari game da alamomin masharranta cikin al’umma ya ce:
شرار أمتي الثرثارون المتشدقون المتفيهقون" البخارى في الأدب وحسنه الألبانى
“masu hatsari a cikin al’ummata su ne; masu suturu masu cika baki da raini da wuce-gona da – iri” bukari ne ya rawaito shi a cikin adabul mufrad. Kuma albanu ya ce: hasan ne.
Su dai masu suturu masu cika baki sun e tsawaitarwa da fadada madana ba tare da kula ba ko daukar mataki ba cikin maganar.
WASU MAGANGANUN GAME DA HATSARIN HARSHE DA WAJABCIN KYAYE SHI
1. An ruwaito cewa Sayyidina Abubakar – Allah ya kara masa yarda- ya zama yana zuba yashi a bakinsa don ya hana kansa yin Magana, yana kuma nuna harshensa yana cewa: Wannan shi ne wanda ya jefa ni ramikan da na fa da”.
2. Abdullahi dan Mas’ud – Allah ya kara masa yarda yana cewa: Na rantse da Allah wanda babu abin bubuwa da cancanta sai shi, babu wani abu da ya fi bukatar da a tsananta tsaro a kansa irin harshe”.
3. Mallam Dawus ya ce: Harshena damisa ne, idan na sake shi sai ya cinye ni.
4. Hasanul Basri ya ce: Duk wanda bai kiyaye harshensa ba, to bai fahimci addininsa ba.
5. Malam Muhammad dan Wasi’u ya gayawa Malik dan Dinar: ya baban Yahya! Kiyaye harshe ya fi zama wahala a wajen mutane a kan kiyaye kudadensu.
6. Imam al Asma’iy ya ce: Magana tana cikin komarka kafin ka fade ta, idan ya rigaya ya fada to sai ya koma cikin komarta.
7. Dan Mubarak ya yi wake ya ce:
اغتنم ركعتين زلفى إلى إلـ
ـه إذا كنت فارغا مستريحا
وإذا هممت بالمنطق الباطـ
ـل فاجعل مكانه تسبيحا
إن بعض السكوت خير من النطـ
ـق وإن كنت بالكلام فصيحا
Ma’ana: Ka ribaci maka’o’I biyu don samun kusanci ga Allah a lokacin da ka ke zaune kawai, kana hutawa, babu abin da ka ke yi. Idan kuma ka yi nufin yin mummuna zance to ka canza shi zuwa yi wa Allah tasbihi. Hakika yin shiru a wasu lokutan ya fi Magana zama alheri ga mutum, ko mutumin mai fasaha ne a cikin zancensa.
No comments:
Post a Comment