GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINSUNNAH-BLOGSPOT.BLOGSPOT.COM


WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA LACCOCI DAGA MALAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI; {mumbarinsunnah@gmail.com]

Thursday, 20 September 2012

SHARRIN HARSHE {2}

KARYA
Karya tana daga cikin manyan aibukan harshe, it ace kuma matattarar kowane sharri, kuma ita ce asalin kowane zargi, karshenta baya da kyau. Sakamakonta mummuna ne.
Allah madaukakin game da sukan makaryata ya ce:
{إنما يفتري الكذب الذين لايؤمنون بئايت الله وأولئك هم الكذبون} النحل: 105
“Wadanda ba sa ba da gaskiya da ayoyin Allah sun e kawai suke kirkirar karya; kuma wadannan da ma su makaryata ne”. (Nahl: 105).
Allah Madaukakin Sarki ya ce:

{ثم نبتهل فنجعل لعنت الله على الكذبين} آل عمران: 61
“Sannan mu shiga yin addu’a don mu sanya tsinewar Allah a kan makaryata” (Al Imran: 61)
Ita karya alama ce ta kaskanci da wulakantar lamari da mummunar zuciya da bacin niyya, da rashin mutunci.
Annabi (S.A.W.) ya ce:

"إياكم والكذب, فإن الكذب يهدي إلى الفجور, وإن الفجور يهدي إلى النار, وإن الرجل ليكذب حتى يكتب عند الله كذابا" متفق عليه:
“Ku kiyayi karya, domin ita karya tana jan mutum zuwa sabon Allah, shikuwa sabon Allah yana kai mutum zuwa ga wuta, hakika mutum ba zai gushe ba yana karya har sai an rubuta shi a wajen Allah cewa shi makaryaci ne”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Ita karya tana cikin alamu na munafukai, kamar yadda Annabi (S.A.W.) ya ce:
"ربع من كن فيه كان منافقا خالصا, ومن كانت فيه خصلة منهن كانت فيه خصلة من النفاق, حتى يدعها, وإذا عاهد غدر". متفق عليه.
Abubuwa guda hudu (4) duk wanda suka zamo tare da shi to shi cikakken munafiki ne, idan kuwa aka samu daya daga cikinsu a tare da mutum to yana da alama ta munafinci har sai ya barta.
1.   Idan ya yi Magana sai ya yi karya
2.   Idan aka amince masa sai ya yi ha’inci
3.   Idan yana jayayya sai ya yi zalunci da kae
4.   Idan ya yi alkawari sai ya yi yaudara.
Shin ya kai dan uwa, zai ka yarda ka zama kana da wadannan sifofi na munafukai? Shin za ka yarda a ce maka kai makaryaci ne? Shin za ka yarda a ce maka kai makaryaci ne? Wani lokaci idan na ga babu mafita, amma ban a yawaita ta ko kuma in fadada ta don kada in saba da ita.
To, ka sani ya dan uwana cewa: karya tana kira ne izuwa sabon Allah, kamar dai yadda Annabi (S.A.W.) ya fada a hadisin da aka ambata a baya. Kuma zai iya yiwuwa karya guda daya ta bata maka duniyarka da lahirarka, an tambayi Khalid dan SUbaih cewaa: Shin za a iya kiran mutum makaryaci idan ya yi karya sau daya kawai? Sai ya ce: E, za a iya
Sannan idan mutane suka gano wata karya bayyananiya guda daya da ka taba yi, to ba za su sake yarda da maganar ka ba har abada. Sai ma su dinga dangana maka karya da kage ko dab a kai ka fada ba, kamar yadda wani mai wake ya ce:
حسب الكذوبة من البلـ *     ية بعض ما يحكى عليه
ما إن سمـعت بكذبــة    *     من غيره نسبت إلـيـه
Ma’ana ya ishi makaryaci bala’I cewa: kadan daga cikin abin da ake fada a kansa shi ne, idan an ji wata karya ko dab a shi ya yi ta ba sai a ce shi ne.
Wani mai waken ya ce:
لقد أخلفتني وخلـفت حـتى
                  إخـالك قد كـذبت وإن صدقنا
حـتى ألا لا تـحلفن على يمين
                  فأكـذب ما تـكون إذا حلفتا
Ma’ana : Ka saba abin da ka rantse a kansa, har ya zama yanzu ina zaton karya ka yi ko da gaskiya ka fada. Ka da ka rantse min domin lokacin da kafi fadar karya shi ne lokacin da rantse.


NAU’O’IN KARYA
Dan uwana, ka sani karya dai duhu ne, wani kan wani, kuma rami neb a wanda yake kutsawa cikinsa sai halakakke. Za a iya karkasa karya kamar haka:
1.   Yi wa Allah da Manzonsa karya, yana daga mafi munin nau’o’in yi musu karya, halatta abin da Allah da Manonsa suka baramta, ko harmata abin suka halatta. Haka nan wanda yake fadar maganar karya da gangan ya kuma danganta ga Allah ko Manzonsa. Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{ومن أظلم ممن افترى على الله كذبا أو كذب بئاتيه إنه لا يفلح الظلمون} الأنعام: 21
 “Babu mafi zalunci kamar wanda ya kirkiri karya ya jingina ga Allah, ko kuma ya karyata ayoyinsa, lallai azzalumai ba za su rabauta ba”. (An’am: 21)
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"من كذب علي متعمدا فليتبوأ مقمده من النار". متفق
 “Duk wanda ya yi mini karya da gangan, to ya tanadi mazauninsa a c ikin wuta” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
2.   Yi wa mutane karya a game da abin da zai shafi mutuncinsu ko dukiyoyinsu ko makamancin haka. Wannan kuwa yana daga cikin mafi girma zunubai kuma ya fi muni ta’addanci da yake cutar da al’umma yana kuma hana adalci da tsari yana kuma ura wutar gaba da kiyayya a cikin jama’a. mafi bayanar alamun wannan nau’I shi ne:
(a)    Yin shaidar karya tana daga cikin manyan zunubai. Annabi (S.A.W.) ya ce:
"ألا أنبئكم بأكبر الكبائر؟ الإشراك بالله, وعقوق الوالدين, وكان متكئا فجلس, ثم قال: ألا وقول الزور, وشهادة الزور". متفق عليه.
 “Yanzu bana ba ku labari ba game da mafi girman zunubai? Yin shirka da Allah (hada wani da Allah wajen bauta) da sabawa iyaye – Annabi yana fada hakan ne yayin da yake kishingide – sai ya tashi zaune ya ce: ku saurara da maganar karya, ku sani da shaidar karya (zur). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Sahabban Annabi (S.A.W.) suka ce: Annabi (S.A.W.) ya yi ta maimaita wannan kalma ta (maganar karya da shaidar karya) har sai damuka ce ina ma dai ya yi shiru haka. 
(b)    Rantsuwa ta karya: ita nau’I ce ta shaidar karya sai dai shi mai shaidar karya a wannan lokaci yana kare shaidarsa da rantsuwar karya. Wannan kuwa mafi tsananin ta’addanci, kuma ya fi shaidar ba tare da rantsuwa ba. Annabi (S.A.W.) y ace:
"من حلف على يمين صبر, يقتطع بها مال امرئ مسلم هو فيها فاجر, لقي الله وهو عليه غضبان". متفق عليه
 “Duk wanda ya yi rantsuwar karya don a bashi dukiyar wani musulmi, to zai gamu da Allah yana mai fushi da shi”,
(c)     Yin karya a cikin saye da sayarwa, kamar wanda yake boyewa mutane aibun abin sayarwarsa, ko ya yi gangancin rantsuwa da alwashi, ya kuma maid a su hanayr tallata kayan sayarwarsa. Annabi (S.A.W.) yana cewa:
"اليمين الكذبة منفقة للسلعة, ممحقة للكسب" متفق عليه.
“Rantsuwar karya tana sayar da kaya (haja) kuma tana kwashe albarkar abin da aka samu”
(d)    Rantsuwa da nufin wasa ko tsokana, wanann ma yana cikin manyan zunubai. Annabi (S.A.W.) y ace:
ويل للذي يحدث فيكذب ليضحك به القوم, ويل له ويل له". رواه أحمد وأبو داود والترمذي.
Azabar wuta ta tabbata a kan wanda yake zance na karya don ya bawa mutane dariya, wuta ta tabbata a gare shi, wuta ta tabbata a gare shi”.
(e)     Karya don a bata tsakanin mutane. Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{فهل عسيبتم إن توليتم أن تفسدوا فى الأرض وتقطعوا أرحامكم} محمد 22
 “Shin kuna fatan idan kun juya bay a (daga umarnin Allah) za ku yi barna a bayan kasa, sannan ku yanke zaumuntarku”. (Muhammadu: 22) Annabi (S.A.W.) y ace:
"من خبب زوجة امرئ أو مملوكة فليس منا" أبو داود وصححه الألباني
 “Duk wanda ya yi karya don ya bata tsaknain mace da mijinta ko tsakaninsa da bawansa, to bashi daga cikinmu”. (Abu Dawud ne ya ruwaito shi. Albani ya ce: Sahihi ne)
3.   YI wa mutane karya cikin abin da bai shafi dukiyarsu ba, ko mutuncinsu. Wannan ko da yake bai kai wancan ba, sai dai shi ma zunubi ne babba. A cikin nau’o’in wannan karyar akwai:
(a)    Yin karya don nuna daukaka ko yin karya don nuna mallakar abin da ba a ba shi. Akan wannan Annabi (S.A.W.) ya ke cewa:
من ادعى ما ليس له فليس منا, وليتبوأ مقعده من النار". البيهقى
 “Duk wanda ya yi da’awar abin da ba shi da shi, to baya daga cikinmu, kuma ya tanadi wurin zamansa a wuta”. Baihaki.
(b)    Bada labarin mafarkin karya a kan hakan Annabi (S.A.W.) ya na cewa:
"من تحلم بحلم لم يره كلف أن يعقد بين شعيرتين ولن يفعل". رواه البخارى
 “Duk wanda ya fadi mafarkin karya, to za a tilasta masa day a daura tsakanin siraran gashi guda biyu, kuma ba zai taba iyawa ba”, (Bukhari ne ya ruwaito shi).


YI DA MUTANE
Yaya za ka yi idan ka san cewa wani mutum yana yin mganaarka, a wurare daban-daban, yana yi da kai yana fadar aibunka da laifuffukanka da sirrinka? Shin za ka yarda da abin da wannan mutum yake aikatawa? Wane mataki za ka dauka a kansa? Da me za ka kwatantashi? Ba makawa cewa za ka ji haushin wannan mutumin, kuma za ka yi kokarin kore wannan cutarwa ta sa daga kanka ta kowacce hanya, ko da ta hanayr zuwa wajensa ne kai masa kashedi ka tsoratar da shi.
Yi da mutane laifi ne mai hatsari daga cikin laifukan harshe wanda Allah Mahallicinmu ya hana mu cikin littafinsa, ya kuam kwatanta mai aikata wannan laifi da mai cin naman dan uwansa matacce, wannan kuwa tsanatawa ne wajen nuna irin bakin munin wannan aki da tsananin ta’addancinsa. Allah ta’ala ya ce:
{ولا يغتب بعضكم بعضا أيحب أحدكم أن يأكل لحم أخيه ميتا فكرهتموه} الحجرات: 12
 “Kada sashinku ya yi da sashi, yanzu dayanku zai ko ya ci naman dan uwansa matacce” (Hujrat: 12).
Al Iman Ibnil Kayyim – Allah ya ji kansa – ya ce: sauda yawa zaka ga mutum mai tsantsenin aikata sabo ko zalintar mutane, amma harshensa yana iya kage cikin cin mutuncin mutane rayayyu ko matattu, bai kuma damu da abin da yake fada ba.
Masu aikata irin wannan laifi bas u san cewa kalma daya tana iya bata musu dukkan ayyukansu na alheri ba, ta kuma bata duniyrsu da lahirarsu. Annabi (S.A.W.) ya sanar da shabbansa, shin kun san me ye yi da mutane? Sai suka ce: Allah da manzonsa sun e suka fi sani. Sai ya ce: Yi da mutane shi ne, ambaton dan uwanka da abin da ba ya so.
Mai yiwu wan e wasu su yi zaton cewa hakan zai zama abin kin e kawai, idan ya zama karya kake masa da kage. Amma idna abin da ka fada a kansa haka ne to ba shi ban e. wannan zaton kuwa kuskure ne, saboda an tambayi Annabi (S.A.W.) a wurin day a yi wancan bayani, aka ce da shi. Shin idan abin da na fada a kan dan uwana haka ne fa? Sai Annabi (S.A.W.) ya ce: idan ya kansace abin da ka ke fada a kansa haka ne to ka yi da shi ne nan, idan abin da ka fada a kansa ba haka ba ne, to ka yi masa kage. (Muslim ne ya ruwaito shi) Annabi (S.A.W.) ya ce:
"لما عرج بي مررت بقوم لهم أظفار من نحاس يخمشون وجوههم وصدروهم, فقلت: من هؤلاء يا جبريل؟ قال: هؤلاء الذين يأكلون لحوم الناس, ويقعون في أعراضهم". (أبو داود وأحمد وصححه الألباني)
 “Lokacin da aka yi tafiya da ni zuwa sama na wuce wasu mutane suna da farata na farin karfe, suna kartar fuskokinsu da kirazansu, sai na ce da Jibril su wane ne wadannan? Sia ya ce: Wadannan su ne wadanda suke cin naman mutane suke kuma keta musu mutuncinsu. (Abu Dawud da Ahmad ne suka ruwaito shi).
Yi da mutane yana daga alamun munafukai da ayyukansu, saboda haka Annabi (S.A.W.) ya tabbatarwa da masu wannan aiki jin kunya a nan duniya kafin su je lahira, Annabi (S.A.W.) ya ce:
يا معشر من آمن بلسانه ولم يدخل الإيمان قلبه, لا تغتابوا المسلمين ولا تتبعوا عوراتهم, فإنه من ابتع عوراتهم اتبع الله عورته ومن يتبع الله عورته يفضحه في بيته". أبو داود وأحمد وصححه الألباني.
Ya ku taron wadanda suka yi imani da harasansu alhali, imanin bai ratsa zukatansu ba, kada ku yi da mutane musulmi, ka da ku bibiya al’aurarsu, domin duk wanda ya bibiyi al’aurar musulmi, Allah zai bibiyi al’aurarsa, duk wanda Allah ya bibiyi al’aurarsa kuwa to zai tozarta shi a cikin gidansa. (Abu Dawud da Ahmad. Albani ya ce sahihi ne).


YANDA ZA KA KI A WAJEN DA AKE YI DA MUTANE (GIBA)
Ya dan uwa musulmi, ya kamata a gareka da farkon farawa kada ka halarci wani wuri wanda ake yi da musulmi. Saboda zuwanka wajen yana cikin taimakawa bisa sabon Allah, da shisshigi da ma hadin gwiwa cikin mugun aiki, kamar yadda yi da mutum bai halatta ba, haka nan ma jin bai halarta ba.
Idan ka halarci wani wuri da ake yi da wani musulumi to ya wajaba a gareka ka hana wannan abin, sannan kuma ka tsoratar da mai aikin ka kuma tsoratar da shi azabar Allah da nesantar da shi radadin ukubarsa.
Sheikh Ibn Baz ya ce: Wajibi ne a kan kowane musulmi da musulma su kiyaye kansu daga yi da mutane kuma yin umarni da barinsa, don biyayya ga Allah da manzonsa, da kuma kwadayin musulmi na suturce ‘yan uwansa da kin bayyanar da laifukansu. Saboda shi yi da mutum yana daga sababin samara da kiyayya da gaba da rarraba kan al’umma. Wajibi ne kin zama da wanda yake yi da musulmi tare da yi masa nasiha da hana shi wannan aikin, saboda fadin Annabi (S.A.W.)
"من رأى منكم منكرا فليغيره بيده, فإنه لم يستطع فبلسانه, فإن لم يستطع فبقلبه, وذلك أضعف الإيمان". (مسلم)
Duk wanda ya ga abin ki daga cikinsu to ya canja shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, idan ba zai iya ba to ya ki shi da zuciyarsa, hakan kuwa shi ne mafi raunin imani”. (Muslim ne ya ruwaito shi).
Idan kuwa baibi abin da aka nuna masa ba, to ka har zama da shi, saboda haka shi ne cikar yi masa inkari.


HUKUNCIN YI DA FAJIRI
Tambaya: wani zaka samu bay a sallah kuma yana aikata ayyuka munana wadanda suke sanya son Allah da Manzonsa su yi fushi da shi, shin ya halatta a fadi halayensu saboda mutane su san mugun halinsu ko a’a?
Amsa: ya wajaba a yi wa wadannan masu irin halayensu nasiha da su dinga aikata abin Allah ya yi horo da shi, kuma hana su aikata abin da Allah ya yi hani a kansa, idan sun bi ko da sannu – sannu ne, to sai a ci gaba da yi musu naishar dai yadda za a iya don samun kariya dga sabon Allah da nesa da mugun aiki. Sannan kuma za a iya yin bayanin abin da suke yin a aikata sabo da mugun aiki, idan da akwai bukatar yin wannan bayani da nufin yi musu kwaroroto don mutane su yi taka tsantsan da halayensu.
Haka nan ya wajaba a kanka fadin halin mutum idan wani ya nemi shawararka a game da hada surukuta da shi, ko hada wani kasuwanci da shi, ko sa shi wani aiki, ko kuma kai da kanka ka ji tsoron wani ya fada cikin tarkonsa ya gamu da ketarsa, to a wannan lokacin ya wajaba bayanin halinsa, saboda kubutar da mutanen kirki daga sharrukansa. Haka kuma yana sa mai sharrin shiga taiyayinsa ganin cewa mutane sun gane shi sun guje shi.
Duk da haka bai kamata ka dau ambaton laifukansa ka mayar abin hirarka da debe kewar abokan zamanka ba. Ko kuma ya zama hirarsa wani abin tsokana ne da ha bad a dariya a dabar hira. Hakan kuma sai ya zama wani nau’I ne na yada harri da koyar da mutane kalolin ta’addanci, har akan ya janyo zukata su saba da jinsu sai su aina kyamatarsu.
Sannan kuma bai halatta ka kirkiri laifuka wadanda bay a aikata sub a ka dora masa saboda wai a kara bata shi da muzanta shi, haka kuwa karya ne da kage gare shi, Annabi (S.A.W.) kuwa ya yi hani akan yin hakan.


WURAREN DA AKE YI DA MUTUM
Mun yi bayanin abin da ake nufi da mutum, mun ce ka ambaci ko ka fadawa wani abin da baya so ta hanyar kaskanta shi cikin illar da ke jikinsa ko cikin tsatsonsa (danginsa) ko ta hailittarsa ko ta hanayr kwaikwayar salon wani aikin nasa ko mganarsa ko ambata shi dangane da addininsa ko lamarin duniyarsa, kai ko da ka fadi kalar shan wuyar rigarsa ko fasalin gidansa ko abin hawansa da niyyar kaskantarwa ko aibawa kamar ka ce: Malam makaho ko mai harara garke, wani gajere, ko misali bararoji da niyyar kaskantarwa ko aibatawa ko kuma kace wne ba shida kirki halinsa ba shi da kyau, ko ka ambaci mutum da narowaci ko matsoraci, ko maha’inci, ko ka ce sana’arsa wulakantacciya ce da nufin tozarta shi ko ka ce wane mai riga da dauda (kazanta) ko gidansa ba tsafta ko duk wasu kalmomi da suka yi kama da wadanna.
Yi da mutum ba kawai ya tsaya a Magana da harshe ba ne a hard a nuni da hannu ko da ka ko ka fada ko ido ko baki, har ma ta hanyar rubutu ko motsi, a takaice dai dukkabn wata hanya da za a fahimci kana aibata mutane, ko kana wulakanta su, to ya shiga cikin yi da mutum. Allah kuwa da manzonsa sun hana, yana kuma cikin manyan zunubai. 

No comments:

Post a Comment