GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINSUNNAH-BLOGSPOT.BLOGSPOT.COM


WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA LACCOCI DAGA MALAN SUNNAH ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI; {mumbarinsunnah@gmail.com]

Thursday, 20 September 2012

SHARRIN HARSHE {3}


GULMA
MA’ANAR GULMA DA YADDA YA KAMATA MUTUM YA YI IDAN AKA KAWO MASA GULMA
         Ita gulma daga cikin manyan laifukan da harshe yake yi ne, abin da ake nufi da gulma shi ne, daukar zancen wani a kai wa wani da niyyar shigar da gaba tsakaninsu, hakan kuwa mabudi ne na sharri, sannan kuma any ace ta barna, Allah Ta’ala ya ce:
{همازٍ مشاء بنميم} القلم: 11
 “Mai zunde mai yawo da gulama: (Nun: 11)
{ويل لكل هُمَزة لُمزةٍ} الهمزة: 1
Alla ya ce: “Bone (azaba) ta tabbata ga duk mai zunde mai rada” (Humaza: 1)
An ce ma’anar kalmar "همزة" mai gulma, Annabi (S.A.W.) ya ce:  
"لايدخل الجنة نمام" متفق عليه.
 “Mai gulma ba zai shiga aljanna ba”. Buhkari da Muslim ne suka ruwaito shi. Gulma tana daga cikin laifukan da suke jawo azabar kabari, wani lokaci Annabi (S.A.W.) ya shie ta wurin wasu kabura guda biu sai ya ce:
"إنهما ليعذبان, ما يعذبان فى كبير, أما أحدهما فكان لا يستتر من بوله, وأما الآخر فكان يمشي بالنميمة". متفقه عليه
 “Hakika wadannan kaburburan gudan biyu ana yi wa mutanen cikisu azaba, ba kuma don wani babban abu ne (a gurinsu) ya sa ake yi musu azabar ba, daya dai bay a tsanewa daga fitsarinsa, dayan kuma yana kai kawo da gulma tsakanin mutane da nufin bata tsakaninsu”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Gulma tana daga laifukan da suke jawo afkuwar musibu da fitintinu masu yawa, wadanda Allah ne kadai ya san karshensu. Sau da yawa an yi yake-yake a dalilin gulma sau daya wa abokan dab a sa rabuwa sun zama makiya saboda ba-sa ga-maciji da juna, saboda gulma, sau da yawa an samu hassada saboda gulma.
Annamiminaci shi ne mafi sharrin abin da aka lalata abu mai daraja da shi, kuma ka tozartar da mutuntaka, Allah ya halakar da magulmacin daya hada gulma da kinibibi, mafi yawancin siffofi marasa kyau suka tattaru a kansu, saboda idan ya dauko karya ya kai wani wuri to ai ya zama makaryaci ga shi kuma idan an ambaci wani abu na aibi ya cira ya kai wani wuri, to a nan kuma yi da wani ya shgo cikin munanan aikinsa.
Wannan mai bataccen hali, bay a rabo da yaudara da ha’inci da kwafa da hassada da wuce gona – da – iri da barna a tsakanin mutane, shi yana cikin mafiya sharrin halattar Allah cikin wadanda suke yawo saboda yada barna a ban kasa.
Yahaya Ibn Uksum ya ce: Mai gulma ya fi mai sihiri sharri, saboda shi mai gulma zai iya yin barnacikin dan lokaci kadan wanda mai sihiri ba zai iya ba.
Hasanul Basri – Allah ya ji kansa – yana cewa: Duk wanda ya kawo maka zancen wani, to zai kai zancenka wajen wani.
Haka nan an ce: Gulma ta dogara ne a kan karya da hassada da munafunci.


WANI LABARI MAI BAN MAMAKI
Hammadu Ibn Salama ya ce: Wata rana wani mutum, ya kai bawansa kasuwa don sayarwa, sai wani mutum ya zo zai siya, sai ya ce masa; Wannan bawan ba shi da wata matsala sai ta gulma. Sai mai sayen bawan nan ya ce: Zan siye shi a hakan ba komai. Bayan ya kawo shi gida yana yi masa aiki, waarana sai ya ce da matar mai gidansa “na fahimci mai gidan nan nawa watau mijinki, bay a sonki yana so ya kawar da kai daga kanki, saboda haka ina son in taimaka miki, ki dauki aska idan ya yi bacci ki yanko min gashin gemunsa, zan hada miki wani Magana wanda zai sa mai gida ya komo da hankalinsa kanki, sai matar da amsa ta kuma yarda da abin da ya gaya mata.
Sai kuma bawan nan ya koma wurin mai gidan y ace masa lallai na fahinci cewa matarka tana da wani masoyi saboda haka yanzu tana son ta kasha, ka don ta je ta auri wancan mutumin, don haka yau kada ka yi bacci don za ta zo ta kasha ka, sai mai gida ya je ya fara baccin gangan, sai ya ga matarsa ta dauko wuka ta nufo shi, sai ya yi firgigit, ya tashi ya kame hannunta, ya yi ta dukanta har ta mutu, sia dangin matar suka zo suka kasha wannan mutumin, a sakamakon haka yaki ya kaure tsakanin dangin mijin da dangin matar.
Duk fa wannan fa ya faru ne sakamakon gulma annamimi.

ABIN DA YA WAJBA A KAN WANDA AKA KAWO MASA GULMAR WANI
Abin day a kamata wanda aka kawo wa labarin wani na gulma ya yi shi ne kamar abin da Abu Hamid al Gazali ya ce: “Duk wand aaka dauko zancen wani aka kawo masa misali aka ce da shi: wane ya ce da kai abu kaza ko ya yi maka kaza ko kuma aka ce da kai yana kokarin bata maka harkarka, ko wane yana cikin manyan makiyanka, ko kuma aka gaya wani abu daban wanda ba wanda aka fada ba, to akwai abubuwa guda shida ya kamata ya yi:
1.   Ka day a gasgata shi, sabodamai gulma fasiki ne, ba a karbar shedarsa.
2.   Ya hana shi wannan aiki, sannan kuma ya yi masa nasiha, sannan ya nuna masa munin aikin
3.   Ya yi kishi, saboda mugun aikinsa na sabon Allah.
4.   Ka day a dauki mugun zato a kan wanda aka ce ya ce da shi kaza.
5.   Kada kuma hakan ya sa shi ya yi bincike da sa – ido a kansa da bibiyar da niyyar ko zai tabbatar da abin da aka kawo masa gulmar dan uwansa a kansa.
6.   Ya kula kada ya yarda ya zama shi ma ya aikata abin da aka hana mai gulma ya yi, shi ne ya bad a labarin wannan gulmar kamar ya ce: wane an kawo min labarin kaza da kaza.
"شر الناس ذو الوجهين"
 “Mafi sharri a cikin mutane shi ne mai fuska biyu”
Dan uwa musulmi ka sani cewa Allah Madaukakin Sarki ya ce game da munafukai:
{مذبذبين بين ذلك لا إلى هؤلاء ولا إلى هؤلاء ومن يضلل الله فلن تجد له سبيلا} النساء: 143
 “Su ne masu kai kawo tsakanin (imaini da kafirci) suba sa ga (muminai) kuma ba su ga (kafirai)”. (Nisa’i:143).
Mai fuska biyu yana kama dawadanna, amma ya fi mai gulma mummunan hali, domin shi mai gulma, an ba shi wannan suna ne saboda daukar zancen wani ya kai wa wani, amma mai fuska biyun nan da can, sai ya zo wa wadannan da wannan zance, wadancan kuma da wannan zance.
Tambaya: Sau da yawa mutane suna Magana da fuska biyu a kaina ko a kan wani na, shin shiru zan yi in kyalesu, ko zan gaya musu cewa na ji abin da suke fada?
Amsa : Bai halatta a yi Magana dafuska biyu ba, saboda hanin Annabi (S.A.W)
"تجدون شر الناس ذا الوجهين, الذي يأتي هؤلاء بوجه وهؤلاء بوجه"
Ma’ana : “Ma fi sharrin mutane shi ne mai fuska biyu, wanda zai zo wa wadannan da wannan fuskar, wadannan kuma da wata fuskar”
Abin da ake nufi shi ne: ka da ya bi mutum a gabansa da nufin banbadanci, sannan bayan nan ka yi ta sukansa a wajen mutane kana aibata shi, kai ta yin haka ga duk wanda bai yi maka ba. To a nan wajibi ne duk wanda ka sani da wannan hali kai masa nasiha, ka kuma tsoratar da shi, ka hana shi irin wannan aiki na muanafukai, sannan yau-da-gobe ba makawa mutane za su gane shi, su fahimci wannan aiki nasa abin kin e, sai su guje shi, su kuma dau mataki a kansa, su yi nesa da abokantaka da shi, duk abin da yake so ba zai samu ba. In kuma har bai ji nasihar da aka yi masa ba, ya yi aiki da ita, to lallai ne a fadakar da mutane dangane da irin mugun halinsa ko da kuwa a bayan idonsa ne.
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"اذكروا الفاسق بما فيه كي يحذره الناس".
 “Ku fadi laifin mai sabo don mutane su guje shi” (Ibnu Jabran ne ya ruwaito shi).
Ya Ubangiji! Afuwarka dukkan mai laifi yak enema, kuma kai ne mafi daukakar wanda ya yi afuwa kuma ya yafe.
Ya Ubangiji Ba wani aiki da nake fatan kubuta sanadiyyarsa, sai dai kaunar tausasawarka.
Duk lokacin da na zo gunka ya Ubangiji da wani babban zunubi, to sai na sami afuwarka ta fishi girma.

TSINUWA DA ZAGI
Ya dan uwa musulmi, za ka fahimci hatsarin tsinewa mutane ta cewa duk wanda ya tsinewa wani to yana tabbatarwa da korarsa da nesanta shi daga rahamar Ubangiji, domin ma’anar tsinuwa shi ne korar mutum daga rahamar Allah, tare da nesantar da shi daga rahamar da baiwar Ubangiji ke nan.
Yin hakan yabnake hukunci ne a kan Allah, cewa ya aikata hakan, wannan idan mai tsinuwar karya yake, ka gay a gayawa Allah abin da bai sani ba, ya kuma kirkirawa Allah karya. Wannankuwa babu shakka yana cikin manyan zunubai masu halakarwa. Shi dai tsinewa musulmin da bai yi abin tsinuwa ba haramun ne a kan kowane musulmi.
An samu hadisai masu yawa game da sukan tsinuwa da hana yenta da bayanin muninta, Annabi (S.A.W.) ya ce:
"لعن المؤمن كقتله" . متفق عليه.
 “Tsinewa mumini kamar kasha shi ne” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Haka ma Annabi (S.A.W.) ya ce:

"ليس المؤمن بالطعان ولا اللعان ولا الفاحش ولا البذيء"
“Mumini bay a tsine-tsine baya soke-soke,bay a alfasha, baya mugun zance”
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"لا يكون اللعانون شفعاء وشهاداء يوم القيامة". (متفقه عليه)
 “Masu tsine-tsine ba za a bas u dammar yin ceto ba, kuma ba za su zama cikin shahidai ba ranar Alkiyama”
Saboda hatsarin tsinuwa da manufar addinin musulunci tsarkake harshen musulmi, tare da tsabtace shi a kan dukkan abin da zai fada, Annabi (S.A.W.) ya yi hani a kan tsinuwa kowane irin abu da bai cancanta a tsine masa ba, ko da kuwa ba mutum ba ne.
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"إن العبد إذا لعن شيئا صعدت اللعنة إلى السماء فتغلق أبواب السماء دونها, ثم تهبط إلى الأرض فتغلق أبوابها دونها, ثم تأخذ يمينا وشمالا, فإذا لم تجد مساغا رجعت إلى الذي لعن فإن كان لذلك أهلا وإلا رجعت إلى قائلها". أبو داود.
 “Idan ba way a la’anci wani abu sai la’anar ta hau sama sai a rufe mata kofofin sama, sai ta dawo kasa sai a rufe mata kofofin kasa, sannan ta duba dama da hagun idan bat a sami mashiga ba, sai ta nufi wwajen wanda aka tsinewa, idan ta same shi ya cancanci tsinuwar sai ta fada kansa, idan kuma bai cancanta ba, to sai ta koma kan wanda ya yi ta”. (Abu Dawud ya ruwaito shi).
Sabdoa haka, Annabi (S.A.W.) ya hana tsinuwa ko da kuwa dabbobi ne ya kuma hana tsine wa iska. Bai halatta a tsinewa wani mutum ba saboda yana aikata sabo, tun da dai wannan sabon bai fitar da shi daga musulunci ba, bai kuma mutu a kan kafirci ba, domin watakila ya tuba, ko ya musulunta kafin ya mutu, duk kuwa wandaya tuba Allah zai yafe masa.
Ya halatta a tsinewa wadanda suka siffanta da wasu siffofi na barna da kafirci, ba tare da ambaton suna ba, kamar ka ce: Allah ya tsine wa Yahudawa da Nasara, ko Allah ya tsine wa azzalumai, Allah ya tsine wa masu kirkirar gumaka, ko Allah ya tsine wa wanda yake aikata irin aikin mutanen Annabi Bud ko Allah ya tsinewa wanda ya canja iyakokin kasa, ko Allah ya tsine wa wanda ya yi yanhka ba don Allah ba, ko Allah ya tsinewa wanda yake sa kayan mata, ko macen da take sa kayan maza, da dai sauransu.
Ya dan uwa musulmi zagi yana jaw saurin fushi da rshin hankali, da tsine wa, da wawanci, musamman idan aka yi shi inda bai dace ba.
Annabi (S.A.W.) ya ce:
"سبباب المسلم فسوق, وقتاله كفر" (متفق عليه)
“Zagin musulmi fasikanci ne, yakarsa kuma kafirci ne”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Imamu Annawawi – Allah ya ji kansa – ya ce: Daga lafizai munana da ake amfani da su a al’ada kamar mutum ya ce: kai jaki! Kai bunsuru! Kai kare! Wannan yanda da muni ta hanya biyu, na farko karya ne, na biyu kuma cutar da musulmi ne. Annabi (S.A.W.) ya hana zagin ko da na dabbobi ne ya ce: ka da ku zagi zakara, domin yana farkar da mutane lokacin sallah”
Shin ba ka ga yadda sahabbai suka yi mamakin yadda za a iya zagin iyaye ba, saboda suna ganin hakan ba zai yiwu a wajen ‘ya’yansu ba, to yaya ken an da sun tarar dam u a wannan zamanin su ga wanda yake dukan iyayensa, ya kuma kore su daga gidansa, ko ya kaisu gidan gajiyayyu ya manta da su har karshen rayuwarsu.

ISGILANCI DA RAINI
Ya dan uwa musulmi ka sani raunanan mutane suna fakewa da yin isgilanci da raini a matsayin hanyar dauke hankalin jamaj’a daga kansu, ko su yi amfani da kambama aibukan mutane wannan kuwa haramun ne, saboda ba a samun gyara ta hanyar isgili ko raini, watakila ma ya zamo hanyar kara sabo da barna, Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{يأيها الذين ءامنوا لا يسخر قوم من قوم عسى أن يكونوا خيرا منهم ولا نساء من نساء عسى أن يكن خيرا منهن ولا تلمزوا أنفسكم ولا تنابزوا بالألقب بئس الإسم الفسوق بعد الإيمان}الحجرات: 11
“Ya ku wadanda suka yi imani ka da wasu mutane su wulakanta wasu, watakila su zama mafiya alheri daga su, (masu isgilancin) kada ma mata su wulakanta mata, watakila su ma wadanda aka wulakanta din su zama mafi alheri daga wadanda suka yi isgilancin. Ka da ku yi wa kawunanku zunde kada kuma ku kira junanku da munanan lakabi, tir da sunan fasikanci bayan mutum ya yi imani”.
Ma’anar Isgilanci shi ne: wulakanci da tozartawa, ko nuni ga aibun wani ko tawayarsa ta fuskar yi masa dariya, za a iya yin hakan ta hanyar Magana ko nuni ko kwaikwaya. Nana Aisha – Allah ya kara mata yarda ta ce: Na taba kwaikwayar wani mutum sai Annabi (S.A.W.) ya ce min:
"والله ما أحب أني حاكيت إنسانا ولي كذا وكذا" أبو داود.
“Wallahi b azan so in kwaikwayi wani mutum ba, a ba ni kaza da kaza”. Abu Dawud ya ruwaito shi. Abu Dawud ne ya ruwaito shi.
Abdullahi dan Abbas – Allah ya kara yarda a gare shi ya fada a game da tafsirin fadin Allah:
{ووضع الكتب فترى المجرمين مشفقين مما فيه يقولون يويلنا مال هذا الكتب لايغادر صغيرة ولا كبيرة إلا أحصها} الكهف: 49
“Suna cewa me ya sami wannan littafi ne ba  ya barin karami lo babban laifi face sai ya kididdige shi”. Dan Abbas ya ce: karamin laifi shi ne murmushin isgilanci ga mumini, babban laifi kyalkyala dariya a gare shi. Wannan yana nuna irin yadda yi wa mutane dariya yana daga cikin manya – mayan zunubai.
Daga cikin nau’o’in isgilanci yi wa masu addinin da lazimtar hanyar Allah isgilanci, domin yi wa irin wadannan mutanen isgilanci yana nuna raunin addini da imani, hakan ma zai iya jan mutum zuwa ga ridda da fita daga musulunci gaba daya, Allah yak are mu.
Imam Ibnu Taimiyya – Allah ya ji kansa – yana fada dangane da fadin Allah Madaukakin Sarki:
{قل أبالله وءايته ورسوله كنتم تستهزءون * لاتعتذروا قدكفرتم بعد إيمنكم} التوبة: 65
“Ka fada cewa shin da Allah da ayoyinsa da manzonsa ku ke yin isgilanci, ka da su ba da wani uzuri, hakika kun kafirta bayan kun yi imani” (Taubah: 65-66).
Wannan ayar tana nuni cewa yin isgilanci da Allah da Manzonsa kafirci ne.
Sheikh Iban Baz ya ce: Yin isgilanci ga musulunci ko da wani abu na musulmi kafirci ne tsantsa, duk wanda yak e wa ma’abota addini masu kiyaye sallah bai halata a zauna da su ba, ko a wannan aiki da suke yi, a kuma tsoratar da mutane daga gare shi, haka nan wanda yake kutsawa cikin matsalolin addini da isgilanci kafiri ne.
An tambayi kwamitin dindindin mai bad a fatawa akan hukuncin yin isgilanci ga gemu ko umarni da aske shi?
Sai suka bada amasa cewa: Bai halatta a yi isgilanci ga wwanda ya tsayar da gemu ba, domin ya tsayar da shi ne don cika umarnin Allah da Annabi (S.A.W.) ya kamata a yi masa nasiha a nusar da shi, a kuma yi masa bayanin cewa yin isgilanci ga wanda ya tsayar da gemu, babban zunubi ne, ana ji wa mai yin sa tsoron fita daga addini (ridda) Allah Madaukakin Sarki ya ce:
{قل أبالله وءايته ورسوله كنتم تستهزءون * لاتعتذروا قدكفرتم بعد إيمنكم} التوبة: 65

WAKA
Ya dan uwa musulmi, waka tana daga cikin munanan ayyukan da harshe yake aikatawa, waka tana rusa zuciya kai tsaye, ta hanayr sa mata cuta, koma ta kasheta, yana daga cikin hatsarin waka kasancewar yana dauke da mafi yawancin aibukan harshe, kamar karya, isgilanci, wulakanci, kazafi, fada, jayayya, batsa da mata, ambatar halittarsu mai kyau, da wuraren da suke jawo fitina a jikinsu, da wasu daga cikin abubuwan da suke kore mutane daga tafarkin Allah Madaukakin Sarki, tana kuma budewa bawa kofofin sha’awa ta haram da cututtuka masu halakarwa.
Haramcin waka abu ne tabbatacce a wurin sahabban Annabi (S.A.W.) ba a samo daya daga cikinsu cewa ya halatta waka ba, sai dai sabanin haka.
Hakika an ruwaito daga dan Mas’ud – Allah ya kara yarda da shi – ya ce: yana rantsewa da Allah cewa: Abin da Allah yake nufi da fadinsa:
{ومن الناس من يشتري لهو الحديث ليضل عن سبيل الله} لقمان: 6
“Daga cikin mutane akwai masu siyan Magana nasa don su kautar da mutane daga hanyar Allah”. Dan Mas’ud ya ce: Ita ce waka.
Waka tana daga manyan laifuffukan harshe a wannan zamani, saboda yanzu babu wani gidan kasa ko na siminti da babu waka a ciki, ta hanyar rediyoyi da talabijin, wadanda suka cika duniya da wake-wake dare da rana, har aka wayi gari mutane basa barci sai suna jin waka, idan sun farka wake suke fara ji, suna cin abinci suna jin waka, suna hutawa da hirarsu duk tare da jin wakoki. Lallai waka ta zama babbar annobar cutar wannan zamani.
Wata tana cikin manyan dalilan da suke kawo kekashewar zuciya, da kaucewa ambaton Allah, da nisantar karatun Alkur’ani, domin son wakoki da son Alkur’ani bas a haduwa a zuciya daya har abda, in dai an so daya to dole a rabu da daya.
Waka tana raunana kishin mutum, saboda haka malamai suka ce, waka ita ce ‘yar aiken zina, kuma tana tsirar da munafunci a zuciyar mutum domin ita sarewar shaidan ce.
Annabi (S.A.W.) ya bada labari cewa: za a samu wasu mutane a cikin al’ummarsa wadanda bas u ganin laifin kide-kide da wake – wake. Annabi (S.A.W.) ya ce:
"ليكونن في أمتي أقوام يستحلون الحر والحرير والخمر والمعازف": رواه البخارى
Ma’ana: za a asami wasu mutane al’ummata suna halatta zina da sa tufafin hariri da sarewa (kide-kide). Bukhari ne ya ruwaito shi.
Hakika abin da Annabi (S.A.W.) ya bad a labarinsa ya tabbata. Allah ya yi gaskiya da ya ce:
{وما ينطق عن الهوى (2) إن هو إلا وحى يوحى (4)
“Bay a furuci da wasa, face shi idan an yi masa wahayi” (Najm: 3-4)
Ka ji tsoron Allah ya dan uwana musulmi ka guji wannan mugun ciwo mai halakarwa, ka rike littafin Ubangijinka, kana mai karanta shi, da neman sanin abin da yake cikinsa. Duk wanda ya karanta harafi daya daga littafin Allah (Alkur’ani) za a ba shi lada goma.

No comments:

Post a Comment