Godiya da yabo sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W.) da ilayan gidansa.
Bayan haka: A ranar 8-10-1419 /24-01-1999 ne Allah ya nufe ni da gabatar da wata lacca a Tudun – Wada Kaduna mai matashiyar “Akidar kala-kato a tarihihance” wadda ta kunshi bayani game da mutanen da suke da’awar bin Alkur’ani kadai ba tare da hada shi da sahihan hadisan Manzon Allah (S.A.W.) ba.
Laccar ta samu halartar dimbin jama’a musamman matmasa, mazauna Kaduna da kewayenta, kasancewar lokacin da aka shirya wannan laccar ya dace da tasowar guguwar wannan gurbatacciyar akidar a Kaduna .
Bayan gabatar da wannan lacca da shekaru shida said an uwa Mal. Aminu Abubakar Gwandu mazauni Jihar Borno ya nemi izinina domin ya rubuce wannan lacca daga kaset ta zama littafi, tare da tuntubar wani dan’uwa mai kwazo game da ayyukan musulunci da zai dauki nauyin bugawa, don haka nan take na bashi ininin yin hakan, saboda kwazonsa da na sani wajen irin wannan aiki bisa sharadin zai kawo in duba, kafin a buga, domin yin ragi ko kari ko gyara ta yadda zai dace da sakon karantawa.
Gama aikinsa keda wuya sai ya aiko mini da shi ni kuma na dora nauyin nazarinsa ga Malam Muhd Rabi’u Umar Rijiyar-Lemo, sabdoa yawan ayyuka da naked a su, kuma ya yi dukkan gyare-gyare da ake bukata Allah ya saka da alherinsa.
‘Yan-uwa Musulmi wajibi ne kowane musulmi ya san cewa ana koyon dokoki da hukunce-hukuncen addinin musulunci net a hanyoyi guda uku
(1) Littafin Allah (S.W.T) wato Alkur’ani mai girma wanda shi ne shugaban littattafan da Allah (S.W.T.) ya saukar gaba dayansu.
(2) Ingantattun Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) wadanda suke fassara ne ga Alkur’ani tare da Karin bayani game da abubuwan da Alkur’ani ya kawo su a dunkule.
(3) Fahimtar ma’anonin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) bi sa hasken maganganu da ayyukan sahabban Manzon Allah (S.A.W.) da wadanda suka biyo bayansu (Tabi’ai). Wanda duk ya bi wadannan matakai wajan koyon addinin musulunci to zai dace da daidai da izinin Allah (S.W.T), wanda kuma ya bar daya ko sama da daya daga cikin abubuwan nan uku, to lalle bai kama hanyar shiriya ba.
Allah (S.W.T.) Ya zabi Annabi Muhammad (S.A.W.) ya zama shne tsani a tsakaninmu da shi, wanda zai isar mana abinda Allah yace mu yi ko mu bari . Da Hadisan Annabi (S.A.W.) basu da amfani da sai Allah (S.W.T.) ya saukar mana da Alkur’ani kai tsaye daga sama, kumar yadda yake saukar mana da ruwa daga sama, ba sai ya aiko Annabi cikin mutane ba, ballantana har ya saukar da Alkur’ani ta hannunsa cikin shekaru ashirin da uku (23), sha-uku kafin hijira, goma bayan hijira da mu’amalarsa da mutane.
Duk wannan dalili ne da yake nuna wajibcin bin umarinsa da hanuwa daga abinda ya hana, domin kuwa lafiyayyen hankali ba zai yarda da cewa Annabi ya zo cikin mutane ya rayu da su har tsawon shekaru ashirin da uku (23) a matsayinsa na Annabi, amma bai taba cewa da su ku yi ko ku bari ba, kawai sai dai ya karanta Alkur’ani kadai ya yi shiru, ba tare da sharhi ko bayani a aikace ko a maganance ba.
Sahabbai kuwa sune suka rabauta da gamuwa da Annabi (S.A.W.) da rayuwa tare da shi, suna masu imani da shi. Sune suka rabauta da yin sallah a bayansa, suka zama mataimakansa a wajen jihadi, suka zama surukansa shi ma ya zama surukinsu, suka yi makwabtaka da shi, suka zama abokan shawararsa, suka taya shi gina masallacinsa, suka rayu da shi har karshen rayuwarsa, sune suka yi masa wanka lokacin daya rasu, suka sa masa likkafani da yi masa sallah, suka binne shi a kabarinsa. Wannan kadai ya isa dalili mai gamsarwa bisa nagartarsu da kasancewarsu mafiya daraja a cikin wannan al’umma, domin kuwa Allah (S.W.T) ba zai bar Annabinsa ba a hannun lalatattun mutane su zama sune za su yi masa wanka da sallah da likkafani, wannan ya ci karo da matsayin Annabi a wurin Allah (S.W.T).
Daga karshe ina addu’ar alheri ga dukkan wanda ya taimaka ta ko wace irin hanya wajen samun nasarar fitowar wannan lacca a matsayin littafi. Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu iko bin ta, ya nuna mana karaya ya bamu ikon kauce mata.
Subhaanakal Wabi hamdika ash’hadu analaa’ilaaha illaa Anta astagfiruka wa atubu ilaika.
Ja’afar Mahmud Adam
Usman bn Affa Islamic Trust
K/gadon kaya Kano , Nigeria
27/Sha’aban/1426AH 01/10/2005AC
ALKUR’ANIYYUN KO KALA KATO, ‘YAN TATSINE
Larabawa kance” “Kara’a, yakara’u, kira’atan ko kur’anan” ma’anar kur’anan da kira’atan kuwa shine “karatu” daga baya ne aka dauki wannan kalmar ta “Alkur’an” a shari ance domin ta zamanto tana nufin littafin da Allah (S.A.W) ya saukar ga manzonsa Annabi Muhamamdu (S.A.W.) ta hanyar Mala’ika Jibrilu wanda ya kusnhi surori dari da goma sha hudu (114) hizfi sitttin (60) , wato daga surartul Fatiha zuwa suratun Nas, wannan shine Alkur’ani mai girma.
Saboda haka, idan ance “ALKUR’ANIYYUN: ana nufin mutanen da suke dangantuwa zuwa ga Alkur’ani kadai, suna masu da’awar binsa da aiki da shi, ba tare da hadawa da hadisai ko fahimtar magabata ba.
Wadannan jama’a masu wannan da’awa da wanna akida anfi saninsu da kasar Hausa wato adanda akewa lakabi da “’Yan kala-kato, ko ‘Yan tatsine” domin su a wurinsu duk wani hadisi maganace ta wani kato kawai, ba ruwansu da shi, wannan itace asalin akidar ‘yan tatsine wadanda aka yakesu tun shekaru da dama da ska shude.
BY SHEIKH JA’AFAR MAHMUD ADAM
No comments:
Post a Comment